Romanos 12

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (HAUSA) vs BKJ

Sair da comparação
1 Saboda haka, ina roƙonku, ’yan’uwa, saboda yawan jinƙan Allah, ku miƙa jikunanku hadaya wadda take mai rai, mai tsarki abin karɓa kuma ga Allah, wannan ita ce hanyar hidimarku ta ruhaniya.
1 Suplico-vos, pois, irmãos, pelas misericórdias de Deus, de apresentardes os vossos corpos em sacrifício vivo, santo e agradável a Deus, que é o vosso culto racional.
2 Kada ku ci gaba da yin abin da duniya take yi, sai dai ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so yake, abu mai kyau, mai daɗi da kuma cikakke.
2 E não sede conformados com este mundo, mas sede transformados pela renovação da vossa mente, para que experimenteis qual é a boa, agradável e perfeita vontade de Deus.
3 Gama ta wurin alherin nan da aka yi mini ne ina ce wa kowannenku. Kada yă ɗauki kansa fiye da yadda ya kamata, a maimakon haka bari yă auna kansa cikin natsuwa, gwargwadon baiwar bangaskiyar da Allah yi masa.
3 Pois eu digo, pela graça que me é dada, para todo mundo que está dentre vós, não pense de si mesmo muito mais do que deveria pensar, senão que pense com sobriedade, assim como Deus tem dado a cada um uma medida de fé.
4 Kamar dai yadda kowannenmu yake da jiki ɗaya da gaɓoɓi da yawa, gaɓoɓin nan kuwa ba aiki iri ɗaya suke yi ba,
4 Porque assim como temos muitos membros em um corpo, e nem todos os membros têm a mesma função,
5 haka ma a cikin Kiristi mu da muke da yawa mun zama jiki ɗaya, kuma kowace gaɓar ɗan’uwan sauran ne.
5 assim nós, que somos muitos, somos um só corpo em Cristo, e cada um, membros uns dos outros.
6 Muna da baye-baye dabam-dabam, gwargwadon alherin da aka yi mana. In baiwar mutum ta yin annabci ce, sai yă yi amfani da ita gwargwadon bangaskiyarsa.
6 Então, tendo diferentes dons, segundo a graça que nos foi dada, se for profecia, profetizemos segundo a medida da fé;
7 In ta hidima ce; sai yă yi hidima. In kuma ta koyarwa ce, sai yă koyar;
7 se é ministério, seja em ministrar; se é ensinar, haja dedicação no ensinar;
8 in ta ƙarfafawa ce, sai yă ƙarfafa; in kuma ta ba da taimako ce don biyan bukatun waɗansu, sai yă yi haka hannu sake; in ta shugabanci ce, sai yă yi shugabanci da himma; in ta nuna jinƙai ce, sai yă yi haka da fara’a.
8 ou o que exorta, na exortação; o que reparte, faça-o com simplicidade; o que governa, com diligência; o que demonstra misericórdia, com alegria.
9 Dole ƙauna tă zama ta gaskiya. Ku ƙi duk abin da yake mugu; ku manne wa abin da yake nagari.
9 O amor seja sem dissimulação. Aborrecei o que é mau e apegai-vos ao que é bom.
10 Ku ba da kanku ga juna cikin ƙauna irin ta ’yan’uwa. Kowa yă yi ƙoƙari wajen girmama wani fiye da kansa.
10 Sede amigavelmente afeiçoados uns aos outros com amor fraternal, preferindo-vos em honra uns aos outros.
11 Kada ku zama marasa himma, sai dai masu himma a ruhaniyarku, kuna bauta wa Ubangiji.
11 Não sejais negligentes nas atividades; ferventes no espírito, servindo ao Senhor.
12 Ku yi farin ciki cikin bege, haƙuri cikin shan wuya, aminci cikin addu’a.
12 Regozijai-vos na esperança, sede pacientes na tribulação, perseverai na oração;
13 Ku taimaki mutanen Allah masu bukata. Ku zama masu karɓan baƙi.
13 compartindo à necessidade dos santos, sede dados à hospitalidade.
14 Ku sa wa masu tsananta muku albarka; ku sa albarka kada fa ku la’anta.
14 Abençoai aos que vos perseguem; abençoai e não amaldiçoeis.
15 Ku yi murna da masu murna, ku yi kuka da masu kuka.
15 Regozijai-vos com os que se regozijam, e chorai com os que choram.
16 Ku yi zaman lafiya da juna. Kada ku nuna girman kai, sai ma ku riƙa cuɗanya da talakawa. Kada ku zama masu ɗaga kai.
16 Tende o mesmo pensamento uns para com os outros; Não tencione coisas altas, mas condescendem a homens de baixa renda. Não sejais sábios em seus próprios conceitos.
17 Idan kowa ya yi muku mugunta, kada ku sāka masa da mugunta. Ku lura don ku aikata abin da kowa zai iya gani cewa daidai ne.
17 Não retribuas a nenhum homem mal por mal; procurai as coisas honestas à vista de todos os homens.
18 Ku yi iya ƙoƙarinku, in zai yiwu, ku yi zaman lafiya da kowa.
18 Se for possível, no que depender de vós, vivei em paz com todos os homens.
19 Kada ku yi ramuwa, abokaina, sai dai ku bar wa Allah. Gama a rubuce yake cewa, “Ramuwa tawa ce; zan kuwa sāka,” in ji Ubangiji.
19 Amados, não vos vingueis a vós mesmos, mas dai lugar à ira, porque está escrito: A vingança é minha; eu recompensarei, diz o Senhor.
20 A maimakon haka,
20 Portanto, se o teu inimigo tiver fome, alimenta-o; se ele tiver sede, dá-lhe de beber; porque fazendo isto, amontoarás brasas de fogo sobre a sua cabeça.
21 Kada ku bar mugunta ta sha kanku, sai dai ku sha kan mugunta ta wurin aikata nagarta.
21 Não sejas vencido pelo mal, mas vence o mal com o bem.

Ler em outra tradução

Comparar com outra

Estude este capítulo no WhatsApp

Peça à IA da Bíblia Fala para explicar Romanos 12, comparar traduções ou montar um estudo — tudo direto pelo WhatsApp.