Jeremias 35
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (HAUSA) vs NAA
1 Ga maganar da ta zo wa Irmiya daga wurin Ubangiji a lokacin mulkin Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda.
1 Palavra que foi dita a Jeremias da parte do Senhor , nos dias de Jeoaquim, filho de Josias, rei de Judá:
2 “Ka tafi wurin iyalin Rekabawa ka gayyace su su zo a ɗaya daga cikin ɗakunan da suke gefe a gidan Ubangiji ka kuma ba su ruwan inabi su sha.”
2 — Vá à casa dos recabitas, fale com eles, leve-os à Casa do Senhor , a uma das câmaras, e ofereça-lhes vinho para beber.
3 Sai na tafi don in kawo Ya’azaniya ɗan Irmiya, ɗan Habazziniya, da ’yan’uwansa da kuma dukan ’ya’yansa maza, dukan iyalin Rekabawa.
3 Então fui falar com Jazanias, filho de Jeremias, filho de Habazinias, com os irmãos dele, com todos os filhos dele e com toda a casa dos recabitas,
4 Na kawo su cikin gidan Ubangiji, a cikin ɗakin ’ya’yan Hanan ɗan Igdaliya maza mutumin Allah. Ɗakin ne kusa da ɗakin fadawa, wanda yake bisa na Ma’asehiya ɗan Shallum mai tsaron ƙofa.
4 e os levei à Casa do Senhor , à câmara dos filhos de Hanã, filho de Jigdalias, homem de Deus. Esta câmara ficava junto à câmara dos oficiais e sobre a câmara de Maaseias, filho de Salum, guarda da porta.
5 Sai na ajiye ƙwarya cike da ruwan inabi da waɗansu kwaf a gaban iyalin Rekabawan na kuma ce musu, “Ku sha ruwan inabin.”
5 Então pus jarras cheias de vinho e copos diante dos filhos da casa dos recabitas e lhes disse: — Bebam!
6 Amma sai suka amsa suka ce, “Ba ma shan ruwan inabi, domin kakanmu Yehonadab ɗan Rekab ya umarce mu cewa, ‘Ko ku, ko zuriyarku kada ku sha ruwan inabi.
6 Mas eles disseram: — Não beberemos vinho, porque Jonadabe, filho de Recabe, nosso pai, nos ordenou: “Nunca bebam vinho, nem vocês nem os seus filhos.
7 Haka kuma ba za ku gina gidaje, ku dasa iri ko ku nome gonakin inabi ba; kada ku kasance da wani daga cikin waɗannan abubuwa, amma dole kullum ku zauna a tentuna. Ta haka za ku yi dogon rai a cikin ƙasar baƙuncinku.’
7 Não construam casas, não façam plantações, não cultivem nem possuam vinhas. Morem a vida inteira em tendas, para que vocês vivam muitos dias sobre a terra em que são estrangeiros.”
8 Mun yi biyayya da kome da kakanmu Yehonadab ɗan Rekab ya umarce mu. Mu ko matanmu ko ’ya’yanmu maza da mata ba mu taɓa shan ruwan inabi ba
8 E nós temos obedecido à voz de Jonadabe, filho de Recabe, nosso pai, em tudo o que ele nos ordenou. Nunca bebemos vinho, nem nós, nem nossas mulheres, nem nossos filhos, nem nossas filhas.
9 ba mu kuma gina gidaje mu zauna a ciki ba ko mu yi gonakin inabi, gonaki ko hatsi ba.
9 Não construímos casas para morar. Não temos vinhas, nem campos, nem plantações.
10 Mun yi rayuwarmu a cikin tentuna mun kuma yi biyayya ƙwarai da kowane abin da kakanmu Yehonadab ya umarce mu.
10 Temos morado em tendas, e, assim, temos obedecido e feito tudo o que o nosso pai Jonadabe nos ordenou.
11 Amma da Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kawo wa ƙasan nan hari, sai muka ce, ‘Ku zo, dole mu tafi Urushalima don mu tsira daga Babiloniyawa da kuma sojojin Arameyawa.’ Saboda haka ne muke a Urushalima.”
11 Mas, quando Nabucodonosor, rei da Babilônia, começou a marchar contra esta terra, dissemos: “Venham, vamos nos refugiar em Jerusalém, por causa do exército dos caldeus e dos sírios.” E assim ficamos em Jerusalém.
12 Sai maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya cewa,
12 Então a palavra do Senhor veio a Jeremias, dizendo:
13 “Ga abin da Ubangiji, Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ka tafi ka faɗa wa mutanen Yahuda da kuma mutanen Urushalima cewa, ‘Ba za ku koyi darasi ku kuma yi biyayya da maganata ba?’ In ji Ubangiji.
13 — Assim diz o Senhor dos Exércitos, o Deus de Israel: Vá e diga ao povo de Judá e aos moradores de Jerusalém: “Será que vocês nunca vão aceitar a minha advertência para obedecer às minhas palavras? — diz o Senhor .
14 ‘Yehonadab ɗan Rekab ya umarci ’ya’yansa maza kada su sha ruwan inabi sun kuma kiyaye wannan umarni. Har yă zuwa yau ba sa shan ruwan inabi, domin sun yi biyayya da umarnin kakansu. Amma na yi muku magana sau da sau, duk da haka ba ku yi biyayya ba.
14 As palavras de Jonadabe, filho de Recabe, que ordenou a seus filhos que não bebessem vinho, foram guardadas; eles não bebem vinho até o dia de hoje, porque obedecem às ordens de seu pai. A mim, porém, que tenho falado a vocês sempre de novo, vocês não obedecem.
15 Sau da sau na aika dukan bayina annabawa gare ku. Suka ce, “Kowannenku ya juyo daga mugayen hanyoyinsa ya sabunta ayyukansa; kada yă bi waɗansu alloli don yă bauta musu. Ta haka za ku zauna a cikin ƙasar da na ba ku da kuma kakanninku.” Amma ba ku saurara ba, ba ku kuwa ji ni ba.
15 Sempre de novo eu enviei todos os meus servos, os profetas, dizendo: ‘Convertam-se agora, cada um de vocês, do seu mau caminho, corrijam as suas ações, não sigam outros deuses para servi-los, e assim vocês ficarão na terra que eu dei a vocês e aos seus pais.’ Mas vocês não me deram ouvidos, nem atenderam.
16 Zuriyar Yehonadab ɗan Rekab sun yi biyayya da umarnin da kakansu ya ba su, amma waɗannan mutane ba su yi mini biyayya ba.’
16 Os filhos de Jonadabe, filho de Recabe, guardaram o mandamento de seu pai, que ele lhes deu, mas este povo não me obedeceu.
17 “Saboda haka, ga abin da Ubangiji Allah Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘Ku saurara! Zan kawo wa Yahuda da kuma kowane mutumin da yake zama a Urushalima kowace masifar da na ambata a kansu. Na yi musu magana, amma ba su saurara ba; na kira su, amma ba su amsa ba.’ ”
17 Por isso, assim diz o Senhor , o Deus dos Exércitos, o Deus de Israel: Eis que trarei sobre Judá e sobre todos os moradores de Jerusalém todo o mal que falei contra eles. Porque lhes falei e eles não me obedeceram, chamei e eles não responderam.”
18 Sai Irmiya ya ce wa iyalin Rekabawa, “Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘Kun yi biyayya da umarnin kakanku Yehonadab kuka kuma kiyaye dukan umarnansa kuka yi kome bisa ga tsari.’
18 E à casa dos recabitas Jeremias disse: — Assim diz o
19 Saboda haka, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘Yehonadab ɗan Rekab ba zai taɓa rasa mutumin da zai yi mini hidima ba.’ ”
19 Por isso, assim diz o Senhor dos Exércitos, o Deus de Israel: Nunca faltará a Jonadabe, filho de Recabe, um descendente homem para me servir.”
Atalhos do teclado
- Capítulo anterior←
- Próximo capítulo→
- Versículo anteriork
- Próximo versículoj
- Limpar seleçãoEsc
- Esta ajuda?
Estude este capítulo no WhatsApp
Peça à IA da Bíblia Fala para explicar Jeremias 35, comparar traduções ou montar um estudo — tudo direto pelo WhatsApp.