Ezequiel 39

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (HAUSA) vs VC

Sair da comparação
VC Versão Católica
1 “Ɗan mutum, ka yi annabci a kan Gog ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da kai, ya Gog, babban sarkin Meshek da Tubal.
1 E tu, filho do homem, profetiza contra Gog nestes termos: eis o que diz o Senhor Javé: é contra ti que venho, Gog, príncipe soberano de Mosoc e de Tubal.
2 Zan juya ka in kuma ja ka. Zan kawo ka daga can arewa in aike ka don ka fāɗa wa duwatsun Isra’ila.
2 Eu te vou fazer ir e vir, eu te conduzirei, eu te transportarei dos confins do norte contra as montanhas de Israel.
3 Sa’an nan zan karya bakan da take a hannun hagunka, in sa kibiyoyin da suke a hannun damanka su fāɗi.
3 De tua mão esquerda escapará teu arco, que eu quebrarei, e de tua mão direita farei cair tuas flechas.
4 A kan duwatsun Isra’ila za ka fāɗi, kai da sojojinka da kuma al’ummai da suke tare da kai. Zan bayar da kai ka zama abinci ga tsuntsaye da namun jeji masu cin nama.
4 Tombarás sobre os montes de Israel, com tuas tropas e as hordas que te seguirem. Dar-te-ei por pasto às aves de rapina, aos voláteis de toda espécie e às feras.
5 Za ka mutu a fili, gama haka ni na faɗa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
5 Serás estirado na terra, porquanto eu disse - oráculo do Senhor Javé.
6 Zan aika da wuta a kan Magog da kuma a kan waɗanda suke zama lafiya a bakin teku, za su kuwa san cewa ni ne Ubangiji.
6 Expedirei fogo a Magog e entre aqueles que ocupam tranqüilamente as praias marinhas; eles saberão que sou eu o Senhor.
7 “ ‘Zan sanar da sunana mai tsarki a cikin mutanena Isra’ila. Ba zan ƙara bari a ɓata sunana mai tsarki ba, kuma al’ummai za su san cewa Ni Ubangiji Mai Tsarki ne a cikin Isra’ila.
7 Farei assim conhecer meu santo nome no meio do meu povo de Israel, sem mais deixá-lo profanar. As nações saberão assim que sou eu o Senhor, santo em Israel.
8 Yana zuwa! Tabbatacce zai faru, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ranar da na yi magana ke nan.
8 Ora, eis o que irá suceder, e isso está próximo - oráculo do Senhor Javé -, eis o dia que eu havia predito.
9 “ ‘Sa’an nan waɗanda suke zama a garuruwan Isra’ila za su fita su tattara makamai su hura wuta da su su kuma ƙone su, manya da ƙanana garkuwoyi, bakkuna da kibiyoyi, kulake da māsu. Shekara bakwai za su yi amfani da su don hura wuta.
9 De todas as cidades de Israel sairão cidadãos para acender um fogo onde hão de queimar as armas: capacetes, escudos, arcos, flechas, lanças, dardos, dos quais se fará uma fogueira durante sete anos.
10 Ba za su yi wahalar zuwa jeji don neman itacen hura wuta ba, domin za su yi amfani da makamai don hura wuta. Za su kuma washe waɗanda suka washe su ganima, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
10 Não mais irão aos campos amontoar lenha, não mais hão de fazer derrubada na floresta, porque com as armas é que se farão fogueiras. Pilharão os saqueadores, destruirão os destruidores - oráculo do Senhor Javé.
11 “ ‘A ranar zan yi wa Gog makabarta a cikin Isra’ila, a kwarin waɗanda suke tafiya wajen gabashin Teku. Za tă tare hanyar matafiya, domin za a binne Gog da dukan mutanensa a can. Ta haka za a kira wurin Kwarin Haman Gog.
11 Naquele dia, assinalarei a Gog o local da sepultura em Israel, o vale dos viandantes, a oriente do mar, que tapará o caminho aos passantes. Aí se enterrará Gog e toda a horda de suas gentes, e chamar-se-á esse vale Hamon-Gog.
12 “ ‘Watanni bakwai gidan Isra’ila zai yi ta binne su don a tsarkake ƙasar.
12 Os israelitas gastarão sete meses para enterrá-los e para limpar a terra.
13 Dukan mutanen ƙasar za su binne su, kuma ranar da za a ɗaukaka ni za tă zama ranar tuni a gare su, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
13 Todas as gentes da terra trabalharão nessa sepultura e hão de orgulhar-se do dia em que eu manifestar a minha glória - oráculo do Senhor Javé.
14 “ ‘Za a ɗauki mutane kullum don tsabtacce ƙasar. Waɗansu za su ratsa ƙasar, ƙari da waɗannan, waɗansu za su binne gawawwakin da suka ragu a ƙasar. A ƙarshen watanni bakwai ɗin za su fara bincikensu.
14 Designar-se-ão homens encarregados de percorrer continuamente a terra para a limparem, enterrando os cadáveres que ficarem distendidos pelo solo: essa procura durará sete meses.
15 Yayinda suke ratsa ƙasar, in waninsu ya ga ƙashin mutum, zai kafa shi kamar alama a gefe sai masu haƙa kabari sun binne shi a Kwarin Haman Gog.
15 Quando em suas caminhadas virem eles ossos humanos, de todo lado farão sinal até que os coveiros os tenham enterrado no vale de Hamon-Gog.
16 Akwai wani garin da ake kira Hamona zai kasance a can. Ta haka za su tsabtacce ƙasar.’
16 Uma cidade terá o nome de Hamona. É assim que se purificará a terra.
17 “Ɗan mutum, ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, ka gayyato kowane irin tsuntsu da dukan namun jeji, ‘Ku taru ku kuma zo wuri ɗaya daga ko’ina don hadayar da nake shirya muku, babbar hadaya a kan duwatsun Isra’ila. A can za ku ci nama ku kuma sha jini.
17 E tu, filho do homem, escuta o que diz o Senhor Javé: dize às aves de toda espécie e a todos os animais dos campos: ajuntai-vos! Vinde, reuni-vos para o sacrifício que vos preparo, um grande sacrifício nas montanhas de Israel: comereis carne e bebereis sangue.
18 Za ku ci naman manyan mutane ku kuma sha jinin sarakunan duniya sai ka ce an yanka raguna da ’yan tumaki, awaki da bijimai, dukansu turkakkun dabbobi daga Bashan.
18 Ireis comer a carne dos heróis e beber o sangue dos príncipes da terra: carneiros, cordeiros, cabritos, touros robustos de Basã.
19 A hadayar da nake shirya muku, za ku ci kitse sai kun ƙoshi ku kuma sha jini sai kun bugu.
19 Nesse sacrifício ao qual vos convido, comereis gordura até vos fartardes, e bebereis sangue até a embriaguez.
20 A teburina za ku ci iya ƙoshiyarku da naman jama’a da kuma mahaya, manyan mutane da sojoji na kowane iri,’ in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
20 À minha mesa vos saciareis de corcéis, cavaleiros, heróis e guerreiros de toda espécie - oráculo do Senhor Javé.
21 “Zan nuna ɗaukakata a cikin al’ummai, kuma dukan al’ummai za su ga hukuncin da zan yi da kuma hannu mai nauyin da zan ɗora a kansu.
21 Desse modo, manifestarei minha glória entre as nações: todas elas me hão de ver executar os meus atos de justiça e pôr a mão sobre elas.
22 Daga wannan rana zuwa gaba gidan Isra’ila zai san cewa ni ne Ubangiji Allahnsu.
22 E, a partir daquele dia, os israelitas saberão que sou eu o Senhor, seu Deus.
23 Al’ummai kuma za su san cewa mutanen Isra’ila sun tafi zaman bauta saboda zunubinsu, domin sun yi rashin aminci gare ni. Saboda haka na kawar da fuskata daga gare su na miƙa su ga abokan gābansu, suka kuwa mutu ta takobi.
23 As nações reconhecerão que é por causa da sua iniqüidade que Israel foi deportado, e que é por causa da sua infidelidade que lhes tenho ocultado a minha face e as tenho entregue nas mãos dos seus inimigos, para que pereçam pela espada.
24 Na yi da su gwargwadon rashin tsabtarsu da laifofinsu, na kuma kawar da fuskata daga gare su.
24 Escondendo-lhes minha face, só lhes fiz o que mereciam por suas iniqüidades e prevaricações.
25 “Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan komo da Yaƙub daga zaman bauta zan kuma yi wa dukan Isra’ila jinƙai, zan kuma yi kishi saboda sunana mai tsarki.
25 E, por isso, eis o que diz o Senhor Javé: dentro em breve vou reconduzir os cavalos de Jacó e apiedar-me de toda a casa de Israel; vou mostrar-me cioso do meu santo nome.
26 Za su manta da kunyar da suka sha da dukan rashin amincin da suka nuna mini sa’ad da suke zama lafiya a ƙasarsu inda ba wanda zai tsorata su.
26 E serão livres de toda vergonha e das infidelidades de que se tornaram culpados para comigo, quando habitarem de novo tranqüilamente sua terra, sem que ninguém os inquiete.
27 Sa’ad da na komo da su daga al’ummai na kuma tattara su daga ƙasashen abokan gābansu, zan nuna kaina mai tsarki ta wurinsu a gaban al’ummai masu yawa.
27 Logo que os houver reconduzido dentre as nações e reunido dos países inimigos, e que houver manifestado a minha santidade aos olhos das nações numerosas por meu proceder a seu respeito,
28 Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji Allahnsu, gama ko da yake na tura su zaman bauta a cikin al’ummai, zan tattara su zuwa ƙasarsu, ba tare da barin wani a baya ba.
28 reconhecerão eles que sou eu o Senhor, que sou seu Deus, porque depois de tê-los exilado entre as nações, eu os reunirei no seu solo sem lá deixar um só.
29 Ba zan ƙara kawar da fuskata daga gare su, gama zan zuba Ruhuna a kan gidan Isra’ila, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.”
29 Não esconderei mais deles a minha face, porque espargirei meu Espírito sobre toda a casa de Israel - oráculo do Senhor Javé.

Ler em outra tradução

Comparar com outra

Estude este capítulo no WhatsApp

Peça à IA da Bíblia Fala para explicar Ezequiel 39, comparar traduções ou montar um estudo — tudo direto pelo WhatsApp.