Ezequiel 16

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (HAUSA) vs NVT

Sair da comparação
NVT Nova Versão Transformadora
1 Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
1 Então recebi outra mensagem do S enhor :
2 “Ɗan mutum, ka sa Urushalima ta san ayyukanta masu banƙyama
2 “Filho do homem, faça Jerusalém ver como são detestáveis seus pecados.
3 ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa wa Urushalima, Asalinki da haihuwarki daga ƙasar Kan’ana ne; mahaifinki mutumin Amoriyawa ne, mahaifiyarki kuma mutuniyar Hitti ce.
3 Transmita-lhe esta mensagem do S enhor Soberano: Você não passa de uma cananeia! Seu pai era amorreu, e sua mãe era hitita.
4 A ranar da aka haife ki ba a yanke cibiyarki ba, ba a kuma yi miki wanka don a tsabtacce ki ba, ba a kuma goge ki da gishiri ba ko a naɗe ki cikin tsummoki.
4 No dia em que você nasceu, ninguém cortou seu cordão umbilical, nem a lavou, nem a esfregou com sal, nem a enrolou em panos.
5 Ba wanda ya dube ki da tausayi ko ya nuna miki isashen jinƙai don yă yi miki ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa. A maimako, sai aka jefar da ke a fili, gama a ranar da aka haife ki an ji ƙyamarki.
5 Ninguém teve compaixão nem cuidou de você. No dia em que nasceu, você foi rejeitada e abandonada num campo.
6 “ ‘Sa’an nan na wuce na ga kina birgima cikin jininki, yayinda kike kwance can cikin jininki sai na ce miki, “Ki rayu!”
6 “Mas eu passei por lá e a vi, indefesa, esperneando em seu sangue, e lhe disse: ‘Viva!’.
7 Na sa kin yi girma kamar tsiro a fili. Kin yi girma kika kuma yi tsayi kika zama mafiya kyau na kayan ado. Nononki suka fito, gashinki kuwa suka yi girma, duk da haka tsirara kike tik.
7 Eu a fiz desenvolver-se, como uma planta no campo. Você cresceu e se tornou uma linda joia. Seus seios se formaram e seu cabelo cresceu, mas você continuava nua.
8 “ ‘Daga baya na wuce, da na dube ki sai na ga cewa kin yi girma sosai har kin kai a ƙaunace ki, na yafa gefen tufafina a kanki na kuma rufe tsiraincinki. Na rantse miki, na ƙulla alkawari da ke, kin kuwa zama tawa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
8 Quando passei por você outra vez, vi que já tinha idade suficiente para amar. Eu a envolvi com meu manto para cobrir sua nudez e pronunciei meus votos de casamento. Fiz uma aliança com você, diz o S enhor Soberano, e você se tornou minha.
9 “ ‘Na yi miki wanka na wanke miki jini daga gare ki na kuma shafa miki mai.
9 “Então lavei você, limpei o sangue e passei óleo perfumado em sua pele.
10 Na rufe ki da rigar da aka yi wa ado na kuma sa miki takalman fata. Na sa miki riga ta lilin mai kyau na kuma rufe ki da riguna masu tsada.
10 Eu lhe dei roupas caras de linho fino e de seda com lindos bordados e sandálias feitas do mais excelente couro de cabra.
11 Na yi miki ado da kayan ado masu daraja, na sa miki mundaye a hannuwanki da abin wuya a wuyanki,
11 Também lhe dei belas joias, pulseiras e lindos colares,
12 na kuma sa miki zobe a hancinki, abin kunne a kunnuwanki da rawani mai kyau a kanki.
12 uma argola para o nariz, brincos para as orelhas e uma bela coroa para a cabeça.
13 Haka kuwa aka caɓa miki zinariya da azurfa; tufafinki kuwa na lilin mai kyau da riguna masu tsada waɗanda aka yi musu ado. Abincinki na gari mai laushi ne, zuma da man zaitun. Kika zama kyakkyawa har kika kuma zama sarauniya.
13 Assim, você foi enfeitada com ouro e prata. Suas roupas eram feitas de linho fino e seda e tinham lindos bordados. Você comia os alimentos mais seletos — farinha da melhor qualidade, mel e azeite — e se tornou mais linda que nunca. Parecia uma rainha, e de fato era!
14 Sunanki ya yaɗu a cikin al’ummai saboda kyanki, domin darajar da na ba ki ya sa kyanki ya zama cikakke, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
14 Sua fama logo se espalhou por todo o mundo, por causa de sua beleza. Eu a vesti com meu esplendor e aperfeiçoei sua beleza, diz o S enhor Soberano.
15 “ ‘Amma kika dogara ga kyanki kika kuma yi amfani da sunan da kika yi don ki zama karuwa. Kin yi ta jibga alherai a kan kowa da ya wuce, sai kyanki ya zama naki.
15 “No entanto, você pensou que era dona de sua fama e de sua beleza. Então, entregou-se como prostituta a todo homem que passava. Sua beleza estava à disposição de quem a pedisse.
16 Kin ɗauki waɗansu tufafinki don ki yi wa kanki masujadai masu ado, inda kike karuwancinki. Irin waɗannan abubuwa bai kamata su faru ba, bai kuma kamata su taɓa faruwa ba.
16 Usou os presentes lindos que lhe dei para fazer altares para seus ídolos e ali se prostituiu. Nunca se viu uma coisa dessas!
17 Kika kuma ɗauki kayan ado masu kyau da na ba ki, kayan adon da aka yi da zinariya da azurfa, kika yi wa kanki gumakan maza kika kuma yi ta yin karuwanci da su.
17 Pegou as joias e os enfeites de ouro e prata que lhe dei, fez estátuas de homens e as adorou. Desse modo, cometeu adultério contra mim.
18 Kika ɗauki rigunanki masu ado don ki sa a kansu, kika kuma miƙa maina da turarena a gabansu.
18 Com as lindas roupas bordadas que lhe dei, vestiu seus ídolos e usou meu óleo perfumado e meu incenso para adorá-los.
19 Haka ma abincin da na tanada miki, lallausan gari, man zaitun, da zuman da na ba ki ki ci, kin miƙa su kamar turare mai ƙanshi a gabansu, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
19 Colocou diante deles como sacrifício a farinha da melhor qualidade, o azeite e o mel com que cuidei de você, diz o S enhor Soberano.
20 “ ‘Kika kuma kwashe ’ya’yanki maza da mata waɗanda kin haifa mini kika miƙa su kamar abinci ga gumakanki. Karuwancinki bai isa ba ne?
20 “Depois, pegou seus filhos e suas filhas, que havia gerado para mim, e os sacrificou a seus deuses. Acaso não bastou você se prostituir?
21 Kin kashe ’ya’yana kika kuma miƙa su ga gumaka.
21 Também teve de matar meus filhos como sacrifício a ídolos?
22 Cikin dukan ayyukan banƙyamarki da karuwancinki ba ki tuna da kwanakin ƙuruciyarki ba, sa’ad da kike tsirara tik, kina birgima cikin jininki.
22 Em todo o seu pecado detestável e em seu adultério, você não se lembrou daqueles dias, muito tempo atrás, em que estava nua e abandonada, esperneando em seu sangue.
23 “ ‘Kaito! Kaitonki, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Bugu da ƙari a kan dukan waɗansu muguntarki,
23 “Que aflição a espera!, diz o S enhor Soberano. Além de todas as suas maldades,
24 kin gina wa kanki ɗakunan sama da gidajen tsafi a kowane dandali.
24 você construiu um lugar de adoração e ergueu altares a ídolos em todas as praças da cidade.
25 A kowane titi kin gina ɗakin tsafi kika kuma wulaƙanta kyanki, kina miƙa jikinki da ƙarin fasikanci ga duk mai wucewa.
25 Em cada esquina, contaminou sua beleza e ofereceu seu corpo a todos que passavam, aumentando sua prostituição.
26 Kin yi karuwanci da Masarawa, maƙwabtanki masu kwaɗayi, kika tsokane ni har na yi fushi da ƙarin fasikancinki.
26 Então acrescentou a seus amantes o lascivo Egito e provocou minha ira com promiscuidade cada vez maior.
27 Saboda haka na miƙa hannuna gāba da ke na kuma rage iyakarki; na ba da ke ga abokan gābanki masu haɗama, ’yan matan Filistiyawa, waɗanda suka sha mamaki saboda halinki na lalata.
27 Por isso eu a feri com minha mão e reduzi seu território. Entreguei-a a seus inimigos, os filisteus, e até eles ficaram espantados com sua conduta depravada.
28 Kin kuma yi karuwanci da Assuriyawa, domin ba kya ƙoshi; kai ko bayan wannan, ba ki ƙoshi ba.
28 Você também se prostituiu com os assírios. Parece que nunca se cansa de procurar amantes! E, mesmo depois de se prostituir com eles, não ficou satisfeita.
29 Sai kika ƙara fasikancinki da ya haɗa da ƙasar cinikin Babilon, amma duk da haka ba ki ƙoshi ba.
29 Acrescentou a seus amantes a Babilônia, terra de comerciantes, mas ainda assim não se contentou.
30 “ ‘Kina da rashin ƙarfi a zuci, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, sa’ad da kika yi duk waɗannan abubuwa, kina yi kamar karuwar da aka watsa!
30 “Como seu coração é fraco, diz o S enhor Soberano, para fazer essas coisas e se comportar como uma prostituta desavergonhada!
31 Sa’ad da kika gina ɗakunan samanki a kowane gefen titi kika kuma gina ɗakunan tsafinki a kowane dandali, ba kamar karuwa kike ba, domin kin karɓi kuɗi.
31 Constrói lugares de adoração em todas as esquinas e altares a seus ídolos em todas as praças. Na verdade, você foi pior que uma prostituta, pois nem exigiu pagamento.
32 “ ‘Ke mazinaciyar mace! Kin gwammace baƙi a maimakon mijinki!
32 Sim, você é uma esposa adúltera que acolhe estranhos em vez do marido.
33 Kowace karuwa kan karɓi kuɗi, amma kina ba da kyautai ga dukan kwartayenki, kina ba su cin hanci don su zo wurinki daga ko’ina don alherai marasa ƙa’ida.
33 As prostitutas cobram por seus serviços, mas você não! Oferece presentes a seus amantes e os suborna para adulterarem com você.
34 Saboda haka cikin karuwancinki kin sha bamban da saura; babu wanda yake binki saboda alheranki. Ke dai dabam ce, gama kikan biya kuma ba mai biyanki.
34 Faz, portanto, o contrário de outras prostitutas. Paga seus amantes em vez de eles pagarem você!”
35 “ ‘Saboda haka, ke karuwa, ki ji maganar Ubangiji!
35 “Portanto, prostituta, ouça esta mensagem do S enhor .
36 Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa domin kin zubar da dukiyarki kika bayyana tsiraicinki cikin fasikancinki da kwartayenki, kuma saboda dukan gumakan banƙyamarki, kuma saboda kin ba su jinin ’ya’yansu,
36 Assim diz o S enhor Soberano: Visto que você derramou sua lascívia e se expôs em prostituição a todos os seus amantes, adorou ídolos detestáveis e matou seus filhos como sacrifícios a seus deuses,
37 saboda haka zan tattara dukan kwartayenki, waɗanda kike jin daɗinsu, waɗanda kike ƙauna da waɗanda kike ƙi. Zan tattara su gāba da ke daga dukan kewaye zan kuma tuɓe ki a gabansu, za su kuwa ga dukan tsiraicinki.
37 ouça o que farei. Reunirei todos os seus aliados — seus amantes com os quais você teve prazer, os que você amou e também os que odiou — e a deixarei nua diante deles, para que todos a vejam.
38 Zan hukunta ki da hukuncin matan da suke zina da kuma waɗanda suke zub da jini; zan kawo hakkin jini na fushina da kuma fushin kishina.
38 Eu a castigarei por homicídio e adultério e, na fúria de meu ciúme, a cobrirei de sangue.
39 Sa’an nan zan miƙa ki ga kwartayenki, za su kuwa rurrushe ɗakunan samanki su kuma farfashe ɗakunan tsafinki. Za su tuɓe miki tufafinki su kuma kwashe kayan adonki masu kyau su bar ki tsirara tik.
39 Então a entregarei a esses muitos povos que são seus amantes, e eles a destruirão. Derrubarão seus lugares de adoração e os altares de seus ídolos. Arrancarão suas roupas, levarão suas lindas joias e a deixarão completamente nua.
40 Za su kawo taron jama’a a kanki, waɗanda za su jajjefe ki da dutse su sassare ki gunduwa-gunduwa da takubansu.
40 Eles se juntarão e formarão uma multidão violenta que a apedrejará e a cortará com espadas.
41 Za su ƙone gidajenki su kuma hukunta ki a idon mata masu yawa. Zan kawo ƙarshen karuwancinki, ba za ki kuma ƙara biyan kwartayenki ba.
41 Queimarão suas casas e a castigarão diante de muitas mulheres. Eu porei fim à sua prostituição, e você não pagará mais seus muitos amantes.
42 Sa’an nan fushina a kanki zai huce fushin kishina kuma ya kwanta; zan huce ba kuwa zan ƙara yin fushi ba.
42 “Por fim, satisfarei minha fúria contra você, e meu ciúme se acalmará. Ficarei tranquilo e já não ficarei irado com você.
43 “ ‘Domin ba ki tuna da kwanakin ƙuruciyarki ba amma kika husatar da ni da waɗannan abubuwa, tabbatacce zan sāka miki alhakin ayyukanki, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ba kin ƙara lalata ga dukan waɗansu ayyuka masu banƙyamarki ba?
43 Primeiro, porém, uma vez que você não se lembrou de sua juventude, mas provocou minha ira com todas as suas maldades, eu lhe darei o castigo merecido por sua conduta, diz o S enhor Soberano. Pois a todos os seus pecados detestáveis você acrescentou a depravação.
44 “ ‘Duk mai yin amfani da karin magana zai faɗi wannan karin magana a kanki cewa, “Kamar yadda mahaifiya take haka ’yar take.”
44 Todos que inventam provérbios dirão a seu respeito: ‘Tal mãe, tal filha’.
45 Ke ’yar mahaifiyarki ce da gaske, wadda ta ƙi mijinta da ’ya’yanta; ke kuma ’yar’uwar ’yar’uwanki mata ce da gaske, waɗanda suka ƙi mazansu da ’ya’yansu. Mahaifiyarki mutuniyar Hitti ce, mahaifinki kuma mutumin Amoriyawa ne.
45 Pois sua mãe detestava o marido e os filhos, e você faz o mesmo. É exatamente como suas irmãs, que também desprezaram marido e filhos. De fato, sua mãe era hitita, e seu pai, amorreu.
46 Babbar ’yar’uwarki mutuniyar Samariya ce, wadda take zaune da ’ya’yanta mata wajen arewa da ke; ƙanuwarki ita ce Sodom wadda take zaune kudu da ke tare da ’ya’yanta mata.
46 “Sua irmã mais velha era Samaria, que vivia com as filhas ao norte. Sua irmã mais nova era Sodoma, que vivia com as filhas ao sul.
47 Ba ki bi hanyoyinsu da abubuwansu na banƙyama kaɗai ba, sai ka ce wannan ya yi miki kaɗan, amma kin lalace fiye da su.
47 Mas você não apenas imitou sua conduta e seus pecados detestáveis; em pouco tempo, você as superou em sua depravação.
48 Muddin in raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, ’yar’uwarki Sodom da ’ya’yanta mata ba su yi abin da ’ya’yanki mata suka yi ba.
48 Tão certo como eu vivo, diz o S enhor Soberano, Sodoma e suas filhas nunca foram tão perversas quanto você e suas filhas.
49 “ ‘To, fa, ga zunubin ’yar’uwarki Sodom. Ita da ’ya’yanta mata sun yi girman kai, sun ƙoshi fiye da kima kuma ba su kula da wani abu ba; ba su taimaki matalauta da kuma masu bukata ba.
49 Sodoma cometia os pecados de orgulho, glutonaria e preguiça, enquanto os pobres e necessitados sofriam.
50 Su masu girman kai ne kuma suka aikata abubuwa masu banƙyama a gabana. Saboda haka na kau da su kamar yadda ka gani.
50 Era arrogante e cometia pecados detestáveis, por isso eu a exterminei, como você viu.
51 Samariya ba tă aikata ko rabin zunubanki ba. Kin aikata abubuwa masu banƙyama fiye da su, suka kuma sa ’yan’uwanki mata suka zama kamar masu adalci ta wurin dukan waɗannan abubuwa da kika aikata.
51 “Nem mesmo Samaria cometeu metade dos pecados que você cometeu. Você fez coisas muito mais detestáveis que suas irmãs. Comparadas a você, elas parecem justas.
52 Ki sha kunyarki, gama kin yi rangwame wa ’yan’uwanki mata. Saboda zunubanki sun yi muni fiye da nasu, sai suka zama kamar sun fi ki adalci. Saboda haka, ki sha kunya ki kuma sha ƙasƙancinki, gama kin sa ’yan’uwanki mata suka zama kamar su masu adalci ne.
52 Você deveria se envergonhar. Seus pecados são tão terríveis que fazem suas irmãs parecerem justas, e até mesmo puras. Que coisa vergonhosa!
53 “ ‘Amma fa, zan komo da nasarar Sodom da ’ya’yanta mata da ta Samariya da ’ya’yanta mata, nasararki kuma tare da su,
53 “Um dia, porém, restaurarei Sodoma e Samaria, e você também.
54 domin ki sha ƙasƙancinki ki kuma sha kunyar dukan abin da kika aikata ta wurin ta’azantar da su.
54 Então você ficará verdadeiramente envergonhada de tudo que fez, pois seus pecados fazem suas irmãs se sentirem bem em comparação com você.
55 ’Yan’uwanki kuwa, Sodom da ’ya’yanta mata da Samariya tare da ’ya’yanta mata, za su koma kamar yadda suke a dā; ke kuma da ’ya’yanki mata za ku koma kamar yadda kike a dā.
55 Quando suas irmãs, Sodoma e Samaria, e todos os seus habitantes forem restaurados, você também será restaurada.
56 Ba za ki ma iya ambaci ’yar’uwarki Sodom a ranar fariyarki ba,
56 Você, em seus dias de arrogância, desprezava Sodoma.
57 kafin a tone muguntarki. Ko da ma haka, yanzu ’ya’yan Arameyawa mata da dukan maƙwabtanta da kuma ’ya’yan Filistiyawa mata suna miki dariyar, dukan waɗanda suke kewaye da ke da suka rena ki.
57 Agora, porém, sua perversidade se tornou evidente para todo o mundo, e você é desprezada por Edom, por todos os vizinhos dele e pela Filístia.
58 Za ki ɗauki hakkin lalatarki da kuma ayyukanki masu banƙyama, in ji Ubangiji.
58 Esse é o castigo por sua depravação e seus pecados detestáveis, diz o S enhor .
59 “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan hukunta kamar yadda ya dace da ke, domin kin ƙyale rantsuwana ta wurin karya alkawari.
59 “Assim diz o S enhor Soberano: Eu lhe darei o que você merece, pois não levou a sério seus votos solenes e quebrou sua aliança.
60 Duk da haka zan tuna da alkawarin da na yi da ke a kwanakin ƙuruciyarki, zan kuma kafa madawwamin alkawari da ke.
60 Contudo, me lembrarei da aliança que fiz com você em sua juventude e estabelecerei com você uma aliança permanente.
61 Sa’an nan za ki tuna da hanyoyinki ki kuma ji kunya sa’ad da kika karɓi ’yan’uwanki mata, waɗanda suka girme ki da kuma waɗanda kika girme su. Zan ba da su kamar ’ya’ya mata gare ki, amma ba bisa alkawarina da ke ba.
61 Então você se lembrará com vergonha de tudo que fez. Farei que suas irmãs, Samaria e Sodoma, se tornem suas filhas, embora elas não façam parte de nossa aliança.
62 Ta haka zan kafa alkawarina da ke, za ki kuma san cewa ni ne Ubangiji.
62 Reafirmarei minha aliança com você, e você saberá que eu sou o S enhor .
63 Sa’an nan, sa’ad da na yi kafara saboda ke domin dukan abin da kika aikata, za ki tuna ki kuma ji kunya har ki kāsa buɗe bakinki saboda kunya, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”
63 Você se lembrará de seus pecados e ficará calada de tanta vergonha quando eu perdoar tudo que fez. Eu, o S enhor Soberano, falei!”.

Ler em outra tradução

Comparar com outra

Estude este capítulo no WhatsApp

Peça à IA da Bíblia Fala para explicar Ezequiel 16, comparar traduções ou montar um estudo — tudo direto pelo WhatsApp.