Números 28

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (HAUSA) vs ARA

Sair da comparação
ARA Almeida Revista e Atualizada 1993
1 Sai Ubangiji ya ce wa Musa,
1 Disse mais o Senhor a Moisés:
2 “Ka umarci Isra’ilawa cewa, ‘Ku tabbatar kun miƙa mini hadaya ta abinci ta wuta mai daɗin ƙanshi a gare ni, a daidai lokaci.’
2 Dá ordem aos filhos de Israel e dize-lhes: Da minha oferta, do meu manjar para as minhas ofertas queimadas, do aroma agradável, tereis cuidado, para mas trazer a seu tempo determinado.
3 Ka gaya musu, ‘Ga hadaya ta ƙonawa ta kowace rana, da za ku miƙa wa Ubangiji, raguna biyu, bana ɗaya-ɗaya, marasa lahani.
3 Dir-lhes-ás: Esta é a oferta queimada que oferecereis ao Senhor , dia após dia: dois cordeiros de um ano, sem defeito, em contínuo holocausto;
4 A miƙa rago ɗaya da safe, ɗaya kuma da yamma,
4 um cordeiro oferecerás pela manhã, e o outro, ao crepúsculo da tarde;
5 tare da hadaya ta lallausan gari kashi ɗaya bisa goma na efan, kwaɓaɓɓe da kwalaba ɗaya na man zaitun mafi kyau.
5 e a décima parte de um efa de flor de farinha, em oferta de manjares, amassada com a quarta parte de um him de azeite batido.
6 Wannan ita ce hadaya ta ƙonawa ta kullum wadda aka kafa a Dutsen Sinai, don daɗin ƙanshi, wato, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.
6 É holocausto contínuo, instituído no monte Sinai, de aroma agradável, oferta queimada ao Senhor .
7 Hadaya ta sha, za tă zama kwalaba ɗaya na ruwan inabi, da ɗan rago guda. Za a kwarara hadaya ta sha ga Ubangiji a wuri mai tsarki.
7 A sua libação será a quarta parte de um him para o cordeiro; no santuário, oferecerás a libação de bebida forte ao Senhor .
8 Ɗayan ɗan ragon kuma za a miƙa shi da yamma, tare irin hadaya ta lallausan gari, da hadaya ta sha da ka yi da safe. Wannan hadaya ce ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
8 E o outro cordeiro oferecerás no crepúsculo da tarde; como a oferta de manjares da manhã e como a sua libação, o trarás em oferta queimada de aroma agradável ao Senhor .
9 “ ‘A ranar Asabbaci, za a miƙa ’yan raguna biyu, bana ɗaya-ɗaya marasa lahani, tare da hadaya ta sha, da hadaya ta lallausan gari kashi biyu bisa goma na efa, kwaɓaɓɓe da mai.
9 No dia de sábado, oferecerás dois cordeiros de um ano, sem defeito, e duas décimas de um efa de flor de farinha, amassada com azeite, em oferta de manjares, e a sua libação;
10 Wannan ita ce hadaya ta ƙonawa ta kowace Asabbaci, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da ta hadaya ta sha.
10 é holocausto de cada sábado, além do holocausto contínuo e a sua libação.
11 “ ‘A rana ta fari ga kowane wata, za a miƙa wa Ubangiji hadayun ’yan bijimai biyu, rago ɗaya, da ’yan tumaki bakwai, bana ɗaya-ɗaya, dukansu kuma marasa lahani.
11 Nos princípios dos vossos meses, oferecereis, em holocausto ao Senhor , dois novilhos e um carneiro, sete cordeiros de um ano, sem defeito,
12 Da kowane bijimi, a kasance da hadaya ta lallausan garin da aka kwaɓa da mai na kashi uku bisa goma na efa; da ɗan rago kuwa, a kasance da hadaya ta lallausan garin da aka kwaɓa da mai na kashi biyu bisa goma na efa;
12 e três décimas de um efa de flor de farinha, amassada com azeite, em oferta de manjares, para um novilho; duas décimas de flor de farinha, amassada com azeite, em oferta de manjares, para um carneiro;
13 da kowane tunkiya kuma, a kasance da hadaya ta lallausan garin da aka kwaɓa da mai, na kashi ɗaya bisa goma na efa. Wannan hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.
13 e uma décima de um efa de flor de farinha, amassada com azeite, em oferta de manjares, para um cordeiro; é holocausto de aroma agradável, oferta queimada ao Senhor .
14 Da kowane bijimi, za a kasance da hadaya ta sha, na rabin kwalabar ruwan inabi; da rago kuwa, a kasance da kashi ɗaya bisa uku; da kowace tunkiya kuma, a kasance da kashi ɗaya bisa huɗu. Wannan ita ce hadaya ta ƙonawa don tsayawar kowane sabon wata na shekara.
14 As suas libações serão a metade de um him de vinho para um novilho, e a terça parte de um him para um carneiro, e a quarta parte de um him para um cordeiro; este é o holocausto da lua nova de cada mês, por todos os meses do ano.
15 Ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadaya ta sha, za a miƙa bunsuru ɗaya ga Ubangiji, hadaya ce don zunubi.
15 Também se trará um bode como oferta pelo pecado, ao Senhor , além do holocausto contínuo, com a sua libação.
16 “ ‘Za a yi Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji a rana ta goma sha huɗu ga wata na fari.
16 No primeiro mês, aos catorze dias do mês, é a Páscoa do Senhor .
17 A rana ta goma sha biyar ga wannan wata, za a yi biki; kwana bakwai za a ci burodi marar yisti.
17 Aos quinze dias do mesmo mês, haverá festa; sete dias se comerão pães asmos.
18 A rana ta farko, za ku yi tsattsarkan taro, ba kuwa za a yi aikin da aka saba yi na kullum ba.
18 No primeiro dia, haverá santa convocação; nenhuma obra servil fareis;
19 Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da bijimai biyu, rago ɗaya, da ’yan raguna bakwai, bana ɗaya-ɗaya; dukansu kuma marasa lahani ga Ubangiji.
19 mas apresentareis oferta queimada em holocausto ao Senhor , dois novilhos, um carneiro e sete cordeiros de um ano; ser-vos-ão eles sem defeito.
20 Da kowane bijimi, a shirya kashi ɗaya bisa uku na efan lallausan gari, kwaɓaɓɓe da mai; da rago guda kuwa, a shirya kashi biyu bisa goma na efan lallausan gari, kwaɓaɓɓe da mai;
20 A sua oferta de manjares será flor de farinha, amassada com azeite; oferecereis três décimas para um novilho e duas décimas para um carneiro.
21 da kowane ’yan raguna bakwai, kashi ɗaya bisa goma.
21 Para cada um dos sete cordeiros oferecereis uma décima;
22 A haɗa da bunsuru guda, a matsayin hadaya don zunubi, don yin muku kafara.
22 e um bode, para oferta pelo pecado, para fazer expiação por vós.
23 Ku shirya wannan tare da hadaya ta ƙonawa ta kowace safiya.
23 Estas coisas oferecereis, além do holocausto da manhã, que é o holocausto contínuo.
24 Ta haka za a shirya abinci don hadayar da aka yi da wuta, kowace rana, har kwana bakwai don daɗin ƙanshi ga Ubangiji; a shirya shi haɗe da hadaya ta ƙonawa ta kullum, da kuma hadaya ta sha.
24 Assim, oferecereis cada dia, por sete dias, o manjar da oferta queimada em aroma agradável ao Senhor ; além do holocausto contínuo, se oferecerá isto com a sua libação.
25 A rana ta bakwai, za ku yi tsattsarkan taro, amma ba za a yi aikin da aka saba yi kullum ba.
25 No sétimo dia, tereis santa convocação; nenhuma obra servil fareis.
26 “ ‘A ranar nunan fari, sa’ad da za ku miƙa wa Ubangiji hadayar sabon hatsi, a lokacin Bikin Makoni, za a yi tsattsarkan taro, ba kuwa za a yi aikin da aka saba yi ba.
26 Também tereis santa convocação no dia das primícias, quando trouxerdes oferta nova de manjares ao Senhor , segundo a vossa Festa das Semanas; nenhuma obra servil fareis.
27 A miƙa hadaya ta ƙonawa da ’yan bijimai biyu, rago ɗaya da ’yan raguna bakwai, bana ɗaya-ɗaya don daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
27 Então, oferecereis ao Senhor por holocausto, em aroma agradável: dois novilhos, um carneiro e sete cordeiros de um ano;
28 Da kowane bijimi a kasance da hadaya ta lallausan gari kashi uku bisa goma na efa, kwaɓaɓɓe da mai; da rago kuwa, a kasance da hadaya ta lallausan gari kashi biyu bisa goma na efa, kwaɓaɓɓe da mai;
28 a sua oferta de manjares de flor de farinha, amassada com azeite: três décimas de um efa para um novilho, duas décimas para um carneiro,
29 da kowane ’yan raguna bakwai, kashi ɗaya bisa goma.
29 uma décima para cada um dos sete cordeiros;
30 A haɗa da bunsuru guda don yin muku kafara.
30 e um bode, para fazer expiação por vós.
31 A miƙa waɗannan tare da hadayarsu ta sha, haɗe da hadaya ta ƙonawa ta kullum, da kuma hadayarta ta sha. A tabbata dabbobin nan marasa lahani ne.
31 Oferecê-los-eis, além do holocausto contínuo, e da sua oferta de manjares, e das suas libações. Ser-vos-ão eles sem defeito.

Ler em outra tradução

Comparar com outra

Estude este capítulo no WhatsApp

Peça à IA da Bíblia Fala para explicar Números 28, comparar traduções ou montar um estudo — tudo direto pelo WhatsApp.