Levítico 27
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (HAUSA) vs NTLH
1 Ubangiji ya ce wa Musa,
1 O Senhor Deus deu a Moisés
2 “Ka yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Duk sa’ad da mutum ya yi rantsuwa ta musamman zai keɓe wani ga Ubangiji, ta wurin biyan kuɗaɗen fansa,
2 as seguintes leis para o povo de Israel: Quando uma pessoa que foi separada para o serviço do
3 ga yadda ma’aunin biyan zai kasance, mutum mai shekara tsakanin ashirin da sittin, za a biya azurfa hamsin.
3 de acordo com a tabela oficial. Os homens de vinte a sessenta anos de idade pagarão cinquenta barras de prata ,
4 Mace kuma za a biya azurfa talatin.
4 e as mulheres da mesma idade pagarão trinta.
5 Saurayi mai shekara tsakanin biyar da ashirin, za a biya azurfa ashirin, yarinya kuma azurfa goma.
5 Os jovens de cinco a vinte anos de idade pagarão vinte barras de prata, e as jovens pagarão dez.
6 Yaro mai shekara tsakanin wata ɗaya da shekara biyar, za a biya azurfa biyar, ’yar yarinya kuma azurfa uku.
6 Os meninos de um mês a cinco anos pagarão cinco barras de prata, e as meninas pagarão três.
7 Namijin da ya fi shekara sittin, za a biya azurfa goma sha biyar, mace kuma azurfa goma.
7 Os homens de sessenta anos para cima pagarão quinze barras de prata, e as mulheres pagarão dez.
8 In mai alkawarin matalauci ne da ba zai iya biyan ƙayyadadden abin da aka tsara ba, sai yă tafi wurin firist, shi firist kuma yă duba yadda mutumin da ya yi alkawarin zai iya biya. Sa’an nan mutumin zai biya abin da firist ya faɗa.
8 Se a pessoa for pobre e não puder pagar a quantia marcada, ela irá falar com o sacerdote, e ele cobrará o que a pessoa puder pagar.
9 “ ‘In abin da ya yi alkawarin yardajje ne a matsayin hadaya ga Ubangiji, wannan dabbar da aka bayar ga Ubangiji, za tă zama mai tsarki.
9 Quando alguém promete a Deus, o Senhor , um animal que pode ser oferecido em sacrifício , esse animal é considerado sagrado
10 Kada yă yi musayarta ko yă yi musaya mai kyau da marar kyau, ko marar kyau da mai kyau; in lalle ne yă yi musayar dabbar da wata, to, duk wannan da kuma wanda zai yi musayar da ita za su zama masu tsarki.
10 e não poderá ser trocado por outro, seja melhor ou pior. Mas, se houver troca, então os dois animais pertencem ao Senhor .
11 In abin da ya yi alkawari dabba ce marar tsarki, wadda ba yardajje ba ce, a matsayin hadaya ga Ubangiji, dole a kai dabbar wa firist,
11 Se o animal for impuro , isto é, um dos animais que o Senhor não aceita, então o dono o levará ao sacerdote
12 wanda zai yanke hukunci dacewarta, ko mai kyau ce, ko marar kyau. Duk darajar da firist ya kimanta, haka za tă zama.
12 para que ele veja quanto vale. O sacerdote dará o preço de acordo com a condição do animal.
13 In mai shi yana so yă fanshi dabbar, dole yă ƙara kashi ɗaya bisa biyar na darajarta.
13 Se o dono quiser tornar a comprar o animal, ele pagará o preço, mais um quinto.
14 “ ‘In mutum ya miƙa gidansa a matsayin wani abu mai tsarki ga Ubangiji, firist zai daidaita dacewar ko mai kyau ne, ko marar kyau. Duk darajar da firist ya kimanta, haka za tă zama.
14 Quando alguém dedicar a sua casa a Deus, o Senhor , o sacerdote fará a avaliação da casa de acordo com a sua condição e dará o preço.
15 In mutumin da ya keɓe gidansa ya fanshe shi, dole yă ƙara kashi ɗaya bisa biyar na darajar, gidan kuma zai zama nasa.
15 Se o dono quiser tornar a comprar a casa, pagará o preço, mais um quinto.
16 “ ‘In wani ya keɓe wa Ubangiji wani sashe daga cikin gonarsa ta gādo, sai yă kimanta kuɗin gonar daidai da yawan irin da za a iya shuka a gonar. Za a kimanta kuɗin a kan shekel hamsin na irin sha’ir.
16 Se alguém oferecer para o serviço de Deus, o Senhor , uma parte dos terrenos que recebeu do pai, o sacerdote fará a avaliação do terreno de acordo com a quantidade de sementes necessária para semeá-lo, na base de cinquenta barras de prata por cem quilos de cevada .
17 In ya keɓe gonarsa a Shekara ta Murna, darajar da aka kimanta za tă zauna.
17 Se ele dedicar o terreno a Deus no Ano da Libertação, o terreno valerá o preço máximo;
18 Amma in ya keɓe gonar bayan Shekara ta Murnan, firist zai kimanta darajar bisa ga yawan shekarun da suka rage har zuwa Shekara ta Murna mai zuwa, sai a rage darajar da aka kimanta a kanta.
18 mas, se for depois do Ano da Libertação, o sacerdote calculará o seu valor, tendo como base os anos que ainda faltarem para o seguinte Ano da Libertação, e assim o preço será mais baixo.
19 In mutumin da ya keɓe gonar, yana so yă fanshe ta, to, dole yă ƙara kashi ɗaya bisa biyar na darajarta, gonar kuwa tă zama nasa.
19 Se o dono do terreno quiser tornar a comprá-lo, ele pagará o preço calculado, mais um quinto.
20 In kuma bai fanshe gonar ba, ko kuwa in ya sayar wa wani dabam, ba za a taɓa fanshe ta ba.
20 Mas, se não quiser tornar a comprá-lo ou se outra pessoa o comprar, ele perderá o direito de tornar a comprá-lo.
21 Sa’ad da aka saki gonar a Shekara ta Murna, za tă zama mai tsarki, a matsayin gonar da aka miƙa ga Ubangiji, za tă zama mallakar firistoci.
21 No Ano da Libertação, quando o terreno ficar livre, ele será oferecido para o serviço de Deus, o Senhor ; é um terreno sagrado que pertence aos sacerdotes.
22 “ ‘In mutum ya keɓe gonar da ya saya, wadda take ba sashe na gonar iyali ba, ga Ubangiji,
22 Se alguém oferecer para o serviço de Deus, o Senhor , um terreno que comprou,
23 firist zai kimanta darajarta har Shekara ta Murna, dole kuma mutumin yă biya darajarta a ranar, a matsayin wani abu mai tsarki ga Ubangiji.
23 o sacerdote calculará o valor do terreno, tendo como base os anos que ainda faltarem para o Ano da Libertação. Nesse mesmo dia o homem pagará o preço total e oferecerá o dinheiro para o serviço do Senhor .
24 A Shekara ta Murna ɗin, gonar za tă dawo ga mutumin da aka saye ta daga wurinsa, wanda yake mai gonar.
24 No seguinte Ano da Libertação o terreno voltará a pertencer ao seu dono, isto é, ao homem que o recebeu como herança.
25 A kimanta kowace daraja bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, gera ashirin ga shekel.
25 Todos os preços serão calculados de acordo com a tabela oficial; a barra padrão, o siclo, vale vinte geras.
26 “ ‘Ba wani da zai iya keɓe ɗan farin dabba, da yake ɗan fari ya riga ya zama na Ubangiji, ko na saniya, ko na tunkiya, na Ubangiji ne.
26 A primeira cria das vacas, ovelhas ou cabras pertence a Deus, o Senhor . Portanto, ninguém poderá oferecê-la ao Senhor , pois já pertence a ele.
27 In tana cikin dabbobin da suke marasa tsarki, zai iya saye ta a darajar da aka kimanta, yă ƙara da kashi ɗaya bisa biyar na darajarta. In bai fanshe ta ba, sai a sayar da ita a darajar da aka kimanta.
27 Mas a primeira cria de um animal impuro poderá ser comprada de novo; deverá ser pago o preço da tabela, mais um quinto. Se não for comprada de novo, a cria poderá ser vendida pelo preço da tabela.
28 “ ‘Amma babu abin da mutum ya mallaka, ya kuma keɓe ga Ubangiji, ko mutum ne, ko dabba, ko ganar iyali da za a sayar, ko a fansa; kome da aka keɓe a wannan hanya, mafi tsarki ne ga Ubangiji.
28 Ninguém poderá vender ou tornar a comprar uma coisa, seja pessoa, animal ou terreno, que tiver sido dedicada para ser usada somente no serviço de Deus, o Senhor . É uma coisa sagrada e pertence completamente ao Senhor .
29 “ ‘Babu wani da aka keɓe don hallaka da za a fansa; dole a kashe shi.
29 Nem mesmo uma pessoa que tenha sido dedicada assim poderá ser comprada de novo; ela será morta.
30 “ ‘Ushirin kome daga gona, ko hatsi daga ƙasa, ko ’ya’yan itatuwa daga itatuwa, na Ubangiji ne, mai tsarki ne ga Ubangiji.
30 A décima parte das colheitas, tanto dos cereais como das frutas, pertence a Deus, o Senhor , e será dada a ele.
31 In mutum ya fanshi wani zakansa, dole yă ƙara kashi ɗaya bisa biyar na darajar.
31 Se o dono quiser tornar a comprar alguma porção dessa décima parte, pagará o preço marcado, mais um quinto.
32 Ushirin gaba ɗaya na garken shanu, da na tumaki, kowane kashi ɗaya bisa goma na dabbar da ta wuce ƙarƙashin sandan mai kiwo, za tă zama mai tsarki ga Ubangiji.
32 De cada dez animais domésticos um pertence a Deus, o Senhor . Quando o dono contar o seu gado e as suas ovelhas e cabras, cada décimo animal pertencerá ao Senhor ,
33 Kada kuwa ya zaɓa mai kyau daga marar kyau, ko yă yi musaya. In ya yi musaya kuwa, dabbar da wadda ya musayar, za su zama masu tsarki, ba kuma za a fanshe su ba.’ ”
33 qualquer que seja a condição do animal. O dono não poderá trocar um animal por outro. Mas, se houver troca, então os dois animais pertencem ao Senhor e não poderão ser comprados de novo.
34 Waɗannan su ne dokokin da Ubangiji ya ba wa Musa a Dutsen Sinai saboda Isra’ilawa.
34 Foram esses os mandamentos que o Senhor Deus deu a Moisés, no monte Sinai, para o povo de Israel.
Atalhos do teclado
- Capítulo anterior←
- Próximo capítulo→
- Versículo anteriork
- Próximo versículoj
- Limpar seleçãoEsc
- Esta ajuda?
Estude este capítulo no WhatsApp
Peça à IA da Bíblia Fala para explicar Levítico 27, comparar traduções ou montar um estudo — tudo direto pelo WhatsApp.