Levítico 25
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (HAUSA) vs NVI
1 Ubangiji ya yi magana da Musa a kan Dutsen Sinai ya ce,
1 Então disse o Senhor a Moisés no monte Sinai:
2 “Yi wa Isra’ilawa magana, ka ce musu, ‘Sa’ad da kuka shiga ƙasar da zan ba ku, dole ƙasar kanta ta kiyaye Asabbaci ga Ubangiji.
2 "Diga o seguinte aos israelitas: Quando vocês entrarem na terra que lhes dou, a própria terra guardará um sábado para o Senhor.
3 Shekara shida, za ku yi shuki, shekara shida kuma za ku aske gonakin inabinku, ku kuma tattara hatsinsu.
3 Durante seis anos semeiem as suas lavouras, aparem as suas vinhas e façam a colheita de suas plantações.
4 Amma a shekara ta bakwai, ƙasar za tă sami hutun Asabbaci, Asabbaci ga Ubangiji. Kada ku yi shuki a gonakinku, ko kuwa ku aske gonakinku na inabi.
4 Mas no sétimo ano a terra terá um sábado de descanso, um sábado dedicado ao Senhor. Não semeiem as suas lavouras, nem aparem as suas vinhas.
5 Kada ku girbe abin da ya yi girma ba tare da ku kuka shuka ba, ko ku girbe inabin da ba ku aske ba. Ƙasar za tă kasance da shekarar hutu.
5 Não colham o que crescer por si, nem colham as uvas das suas vinhas que não serão podadas. A terra terá um ano de descanso.
6 Duk abin da gonar ta ba da amfani a shekara ta Asabbaci, zai zama abinci gare ku, wa kanku, bayinku maza da mata, da ma’aikatan da kuka ɗauka aiki, da kuma waɗanda ba zama ɗinɗinɗin suke yi tare da ku ba,
6 Vocês se sustentarão do que a terra produzir no ano de descanso, você, o seu escravo, a sua escrava, o trabalhador contratado e o residente temporário que vive entre vocês,
7 haka ma zai zama abinci domin dabbobinku, da kuma namun jeji a ƙasarku. Duk abin da ƙasar ta bayar za a ci.
7 bem como os seus rebanhos e os animais selvagens de sua terra. Tudo o que a terra produzir poderá ser comido.
8 “ ‘Ku ƙirga asabbatai bakwai na shekaru bakwai, sau bakwai. Gama asabbatai bakwai na shekaru bakwai za su yi daidai da shekaru arba’in da tara.
8 "Contem sete semanas de anos, sete vezes sete anos; essas sete semanas de anos totalizam quarenta e nove anos.
9 Sa’an nan a busa ƙaho a ko’ina, a rana ta goma ga wata na bakwai; a Ranar Kafara, a busa ƙaho a dukan ƙasarku.
9 Então façam soar a trombeta no décimo dia do sétimo mês; no Dia da Expiação façam soar a trombeta por toda a terra de vocês.
10 Ku keɓe shekara ta hamsin ku kuma yi shelar ’yanci a dukan ƙasar ga mazaunanta. Za tă zama shekarar murna gare ku; kowannenku zai koma ga mallakar iyalinsa, kuma kowa ga danginsa.
10 Consagrem o qüinquagésimo ano e proclamem libertação por toda a terra a todos os seus moradores. Este lhes será um ano de jubileu, quando cada um de vocês voltará para a propriedade da sua família e para o seu próprio clã.
11 Shekara ta hamsin za tă zama ta murna a gare ku; kada ku yi shuki, kada kuma ku yi girbi abin da ya yi girma da kansa, ko ku girbe inabin da ba ku lura da shi ba.
11 O quinquagésimo ano lhes será jubileu; não semeiem e não ceifem o que cresce por si mesmo nem colham das vinhas não podadas.
12 Gama shekara ce ta murna, za tă kuma zama mai tsarki a gare ku, ku dai ci abin da aka ɗauka kai tsaye daga gonaki.
12 É jubileu, e lhes será santo; comam apenas o que a terra produzir.
13 “ ‘A wannan Shekara ta Murna, kowa zai koma ga mallakarsa.
13 "Nesse ano do jubileu cada um de vocês voltará para a sua propriedade.
14 “ ‘In ka sayar da gona wa wani daga mutanen ƙasarka, ko ka saya wata gona daga gare shi, kada ku cuci juna.
14 "Se vocês venderem alguma propriedade ao seu próximo ou se comprarem alguma propriedade dele, não explore o seu irmão.
15 Sa’ad da mutum ya sayi fili daga abokin zamansa, kuɗin zai kasance bisa ga yawan shekara hamsin ta murna da suka wuce, da kuma bisa ga yawan shekarun noma da suka rage kafin wata shekara hamsin ta murna.
15 O que comprarem do seu próximo será avaliado com base no número de anos desde o Jubileu. E fará a venda com base no número de anos que restam de colheitas.
16 Idan shekarun suna da yawa, sai ku kara kuɗin filin, idan kuma shekarun ba su da yawa, sai ku rage kuɗin filin, gama ainihin abin da ake sayar maka shi ne yawan hatsin.
16 Quando os anos forem muitos, vocês deverão aumentar o preço, mas quando forem poucos, deverão diminuir o preço, pois o que ele está lhes vendendo é o número de colheitas.
17 Kada ku cuci juna, amma ku ji tsoron Allahnku. Ni ne Ubangiji Allahnku.
17 Não explorem um ao outro, mas temam ao Deus de vocês. Eu sou o Senhor, o Deus de vocês.
18 “ ‘Ku bi farillaina, ku kuma yi hankali ga kiyaye dokokina, za ku kuwa zauna lafiya a ƙasar.
18 "Pratiquem os meus decretos e obedeçam às minhas ordenanças, e vocês viverão com segurança na terra.
19 Sa’an nan ƙasar za tă ba da amfaninta, za ku kuwa ci ku ƙoshi, ku kuma zauna lafiya.
19 Então a terra dará o seu fruto, e vocês comerão até fartar-se e ali viverão em segurança.
20 Mai yiwuwa ku ce, “Me za mu ci a shekara ta bakwai in ba mu yi shuki ko girbin hatsinmu ba?”
20 Vocês poderão perguntar: ‘Que iremos comer no sétimo ano, se não plantarmos nem fizermos a colheita? ’
21 Zan aika muku da irin albarka a shekara ta shida har da ƙasar za tă ba da amfani isashe na shekara uku.
21 Saibam que eu lhes enviarei a minha bênção no sexto ano, e a terra produzirá o suficiente para três anos.
22 Yayinda kuke shuki a shekara ta takwas, za ku kasance da raguwa hatsi na shekarar da ta wuce, za ku kuma ci gaba da ci daga gare shi har girbin shekara ta tara yă shigo.
22 Quando vocês estiverem plantando no oitavo ano, comerão ainda da colheita anterior e dela continuarão a comer até a colheita do nono ano.
23 “ ‘Kada a sayar da gona ɗinɗinɗin, gama ƙasar tawa ce, ku kuwa baƙi ne kawai, kuma ’yan haya nawa.
23 "A terra não poderá ser vendida definitivamente, porque ela é minha, e vocês são apenas estrangeiros e imigrantes.
24 Ko’ina a ƙasar da kuke da mallaka, dole ku tanadar da dama fansar ƙasar.
24 Em toda terra em que tiverem propriedade, concedam o direito de resgate da terra.
25 “ ‘In ɗaya daga cikin mutanen ƙasarku ya talauta, ya kuma sayar da mallakarsa, sai danginsa na kusa yă je yă fanshi abin da mutumin ƙasarsa ya sayar.
25 "Se alguém do seu povo empobrecer e vender parte da sua propriedade, seu parente mais próximo virá e resgatará aquilo que o seu compatriota vendeu.
26 In mutumin ba shi da wanda zai fansa masa ita, shi kansa kuwa ya wadace, ya kuma sami isashen halin fansarta,
26 Se, contudo, um homem não tiver quem lhe resgate a terra, mas ele mesmo prosperar e adquirir recursos para resgatá-la,
27 sai yă lasafta yawan shekarun da aka yi tun da an sayar da filin. Kuɗin filin zai dangana ga yawan shekarun da suka rage kafin shekara hamsin ta murna da za tă zo; sa’an nan zai iya koma ga mallakarsa.
27 calculará os anos desde que a vendeu e devolverá a diferença àquele a quem a vendeu; então poderá voltar para a sua propriedade.
28 Amma in bai sami halin sāke biyansa ba, abin nan da ya sayar zai ci gaba da zama mallakar mai sayan, sai Shekara ta Murna. Za a maido masa da ita a Shekara ta Murna, sa’an nan zai iya koma ga mallakarsa.
28 Mas, se não adquirir recursos para devolver-lhe o valor, a propriedade que vendeu permanecerá em posse do comprador até o ano do jubileu. Será devolvida no Jubileu, e ele então poderá voltar para a sua propriedade.
29 “ ‘In mutum ya sayar da gida a birni mai katanga, yana da izini yă fanshe shi a ƙarshen shekara guda, bayan ya sayar da shi.
29 "Se um homem vender uma casa numa cidade murada, terá o direito de resgate até que se complete um ano após a venda. Nesse período poderá resgatá-la.
30 In ba a fanshe shi a ƙarshen shekara ba, gidan da yake a birni mai katanga, zai zama mallakar na ɗinɗinɗin na mai sayan da kuma zuriyarsa. Ba za a mai da shi a Shekara ta Murna ba.
30 Se não for resgatada antes de se completar um ano, a casa da cidade murada pertencerá definitivamente ao comprador e aos seus descendentes; não será devolvida no Jubileu.
31 Amma za a ɗauki gidaje a ƙauyuka marasa katanga kewaye da su daidai da gonaki. Za a iya fanshe su, a kuma mayar da su a Shekara ta Murna.
31 Mas as casas dos povoados sem muros ao redor serão consideradas campo aberto. Poderão ser resgatadas e serão devolvidas no Jubileu.
32 “ ‘Kullum, Lawiyawa suna da izini su fanshi gidajensu a biranen Lawiyawa waɗanda suka mallaka.
32 "No caso das cidades dos levitas, eles sempre terão direito de resgatar suas casas nas cidades que lhes pertencem.
33 Saboda haka ana iya fansa mallakar Lawiyawa, wato, gidan da aka sayar a duk birnin da yake nasu, za a kuma mayar a Shekara ta Murna, gama gidaje a biranen Lawiyawa, mallakar Isra’ilawa ne.
33 Assim, a propriedade dos levitas, isto é, uma casa vendida em qualquer cidade deles, é resgatável e deverá ser devolvida no Jubileu, porque as casas das cidades dos levitas são propriedade deles entre os israelitas.
34 Amma kada a sayar da filayen kiwo na waɗannan birane; mallakarsu ce, ta ɗinɗinɗin.
34 Mas as pastagens pertencentes às suas cidades não serão vendidas; são propriedade permanente deles.
35 “ ‘In ɗaya daga ciki mutanen ƙasarku ya talauta, ba ya kuma iya tallafa wa kansa a cikinku, sai ku taimake shi kamar yadda za ku yi da baƙo a cikinku.
35 "Se alguém do seu povo empobrecer e não puder sustentar-se, ajudem-no como se faz ao estrangeiro e ao residente temporário, para que possa continuar a viver entre vocês.
36 Kada ku karɓi riba ta kowace iri daga gare shi, amma ku ji tsoron Allahnku, saboda mutumin ƙasarku yă ci gaba da zama a cikinku.
36 Não cobrem dele juro algum, mas temam o seu Deus, para que o seu próximo continue a viver entre vocês.
37 Kada ku ba shi rancen kuɗi da ruwa, ko ku sayar masa abinci don samun riba.
37 Vocês não poderão exigir dele juros nem emprestar-lhe mantimento visando lucro.
38 Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar, don in ba ku ƙasar Kan’ana in kuma zama Allahnku.
38 Eu sou o Senhor, o Deus de vocês, que os tirou da terra do Egito para dar-lhes a terra de Canaã e para ser o seu Deus.
39 “ ‘In ɗaya daga cikin mutanen ƙasarku ya talauta a cikinku, ya kuma sayar da kansa gare ku, kada ku sa yă yi kamar bawa.
39 "Se alguém do seu povo empobrecer e se vender a algum de vocês, não o façam trabalhar como escravo.
40 Amma a ɗauke shi a matsayin ma’aikacin da aka ɗauka aiki, ko mazaunan da ba na ɗinɗinɗin ba a cikinku, sai yă yi muku aiki sai Shekara ta Murna.
40 Ele deverá ser tratado como trabalhador contratado ou como residente temporário; trabalhará para quem o comprou até o ano do jubileu.
41 Sa’an nan a sake shi da ’ya’yansa, yă kuma koma ga danginsa da mallakar kakanninsa.
41 Então ele e os seus filhos estarão livres, e ele poderá voltar para o seu próprio clã e para a propriedade dos seus antepassados.
42 Gama Isra’ilawa bayina ne, waɗanda na saya daga Masar, kada a sayar da su a matsayin bayi.
42 Pois os israelitas são meus servos, a quem tirei da terra do Egito; não poderão ser vendidos como escravos.
43 Kada ku gwada musu azaba, amma ku ji tsoron Allahnku.
43 Não dominem impiedosamente sobre eles, mas temam o seu Deus.
44 “ ‘Bayinku maza da mata, za su zo daga al’ummai da suke kewaye da ku, daga gare su za ku iya saya bayi.
44 "Os seus escravos e as suas escravas deverão vir dos povos que vivem ao redor de vocês; deles vocês poderão comprar escravos e escravas.
45 Za ku iya saya waɗansu mutanen da ba sa zama ɗinɗinɗin a cikinku, da kuma membobin danginsu da aka haifa a ƙasarku.
45 Também poderão comprá-los entre os filhos dos residentes temporários que vivem entre vocês e entre os que pertencem aos clãs deles, ainda que nascidos na terra de vocês; eles se tornarão propriedade de vocês.
46 Za ku iya ba da su ga ’ya’yanku a matsayin kayan gādo, za ku kuma iya mai da su bayi dukan rayuwarsu, amma kada ku yi mulki a bisa ’yan’uwanku Isra’ilawa da tsanani.
46 Vocês poderão deixá-los como herança para os seus filhos e poderão fazê-los escravos para sempre, mas sobre os seus irmãos israelitas vocês não poderão dominar impiedosamente.
47 “ ‘In baƙo, ko wani da yake zama ba na ɗinɗinɗin ba a cikinku, ya wadace, ɗaya daga cikin mutanen ƙasarku kuwa ya talauta, ya kuma sayar da kansa ga baƙon da yake zama a cikinku, ko memba na dangin baƙon,
47 "Se um estrangeiro ou um residente temporário entre vocês enriquecer e alguém do seu povo empobrecer e se vender a esse estrangeiro ou a alguém que pertence ao clã desse estrangeiro,
48 yana da izini samun fansa, bayan ya sayar da kansa. Ɗaya daga cikin danginsa zai iya fansarsa.
48 manterá o direito de resgate mesmo depois de vender a si mesmo. Um dos seus parentes poderá resgatá-lo:
49 Kawu ko yaron ɗan’uwan mahaifin wannan mutum, ko kuwa wani dangi a cikin zuriyarsa, zai iya fanshe shi. Ko kuma in ya azurta, zai iya fansar kansa.
49 ou tio, ou primo, ou qualquer parente próximo poderá resgatá-lo. Se, todavia, prosperar, poderá resgatar a si mesmo.
50 Da shi da mai sayansa, za su ƙirga lokaci daga shekarar da ya sayar da kansa har zuwa Shekara ta Murna. Farashin sakinsa zai dangana a kuɗin da ake biyan ma’aikacin da aka ɗauka aiki, na yawan shekarun ne.
50 Ele e o seu comprador contarão o tempo desde o ano em que vendeu a si mesmo até o ano do jubileu. O preço do resgate se baseará no salário de um empregado contratado por aquele número de anos.
51 In shekaru sun ragu, dole yă biya don fansarsa da kuɗi mai yawa fiye da wanda aka saye shi.
51 Se restarem muitos anos, pagará o seu resgate proporcionalmente ao preço de compra.
52 In shekarun sun rage kaɗan ne kafin Shekara ta Murna, sai yă yi lissafin wannan, yă kuma biya fansarsa daidai wa daida.
52 Se restarem apenas poucos anos até o ano do jubileu, fará o cálculo, e pagará o seu resgate proporcionalmente aos anos.
53 Sai a yi da shi kamar ma’aikacin da aka ɗauka aiki, daga shekara zuwa shekara; dole ku tabbata mai shi bai mallake shi da tsanani ba.
53 Ele deverá ser tratado como um empregado contratado anualmente; não permitam que o seu senhor domine impiedosamente sobre ele.
54 “ ‘Ko ma ba a fanshe shi a ɗaya daga cikin waɗannan hanyoyi ba, sai a sake shi da ’ya’yansa a Shekara ta Murna,
54 "Se não for resgatado por nenhuma dessas maneiras, ele e os seus filhos estarão livres no ano do jubileu,
55 gama Isra’ilawa nawa ne a matsayin bayi. Su bayina ne waɗanda na saya daga Masar. Ni ne Ubangiji Allahnku.
55 porque os israelitas são meus servos, os quais tirei da terra do Egito. Eu sou o Senhor, o Deus de vocês".
Atalhos do teclado
- Capítulo anterior←
- Próximo capítulo→
- Versículo anteriork
- Próximo versículoj
- Limpar seleçãoEsc
- Esta ajuda?
Estude este capítulo no WhatsApp
Peça à IA da Bíblia Fala para explicar Levítico 25, comparar traduções ou montar um estudo — tudo direto pelo WhatsApp.