Levítico 15
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (HAUSA) vs NTLH
1 Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,
1 O Senhor Deus deu a Moisés e a Arão as seguintes leis
2 “Yi wa Isra’ilawa magana, ku ce musu, ‘Duk sa’ad da wani namiji yake ɗiga daga azzakarinsa, wannan ɗiga marar tsarki ne.
2 para o povo de Israel: Quando um homem tiver um corrimento no membro, ele ficará
3 Ko ɗigar ta ci gaba da fitowa daga azzakarinsa ko an tsere ta, za tă sa mutumin yă zama marar tsarki. Ga yadda ɗigarsa za tă kawo ƙazantuwa,
3 tanto se o corrimento vazar do membro como se o corrimento parar nele. De um jeito ou do outro o homem ficará impuro.
4 “ ‘Duk gadon da mutumin mai ɗigar ya kwanta a kai, zai zama marar tsarki, kuma duk abin da ya zauna a kai, zai zama marar tsarki.
4 Qualquer cama em que ele se deitar e tudo aquilo em que se assentar ficarão impuros.
5 Duk wanda ya taɓa gadonsa dole yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka, zai kuwa ƙazantu har yamma.
5 Se alguém tocar na cama dele
6 Duk wanda ya zauna a inda wannan mai ɗiga ya zauna a kai, dole yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka, zai kuwa ƙazantu har yamma.
6 ou se sentar onde ele se sentou, essa pessoa deverá lavar a roupa que estiver vestindo e tomar um banho; e ficará impura até o pôr do sol.
7 “ ‘Duk wanda ya taɓa jikin mai ɗiga, dole yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma.
7 E quem tocar no homem que tem o corrimento deverá lavar a roupa que estiver vestindo e tomar um banho; e ficará impuro até o pôr do sol.
8 “ ‘In mai ɗiga ya tofa miyau a kan wani wanda yake tsarkakakke, dole tsarkakakken nan yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma.
8 Se o homem que tem o corrimento cuspir numa pessoa que está pura , essa pessoa deverá lavar a roupa que estiver vestindo e tomar um banho; e ficará impura até o pôr do sol.
9 “ ‘Kowane sirdi da mai ɗigar ya zauna a kai zai ƙazantu,
9 Qualquer sela que o homem montar se tornará impura.
10 kuma duk wanda ya taɓa wani abu cikin abubuwan da suke a ƙarƙashin sirdin zai ƙazantu har yamma; duk wanda ya ɗauki abubuwan nan dole yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka, zai kuwa ƙazantu har yamma.
10 Quem tocar naquilo em que o homem se sentou ficará impuro até o pôr do sol. Se alguém pegar naquilo em que o homem se sentou, deverá lavar a roupa que estiver vestindo e tomar um banho; e ficará impuro até o pôr do sol.
11 “ ‘Duk wanda mai ɗiga ya taɓa ba tare da ya wanke hannuwansa da ruwa ba, dole yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma.
11 Se o homem que tem o corrimento tocar numa pessoa sem primeiro lavar as mãos, então aquela pessoa deverá lavar a roupa que estiver vestindo e tomar um banho; e ficará impura até o pôr do sol.
12 “ ‘Dole a farfashe tukunya lakar da mutumin ya taɓa, kuma dole a ɗauraye duk wani abin da aka yi da katako wanda ya taɓa da ruwa.
12 Qualquer pote de barro que o homem pegar deverá ser quebrado; se for de madeira, deverá ser lavado.
13 “ ‘Sa’ad da aka tsabtacce mai ɗigar, zai ɗauki kwana bakwai don tsabtaccewarsa; dole yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka mai tsabta, zai kuwa zama tsarkakakke.
13 Quando o homem sarar, precisará esperar sete dias para se purificar . Passado esse tempo, deverá lavar a roupa que estiver vestindo e tomar um banho em água de uma fonte; então ficará puro .
14 A rana ta takwas dole yă ɗauki kurciyoyi biyu ko tattabarai biyu, yă zo gaban Ubangiji a ƙofar Tentin Sujada, yă ba da su ga firist.
14 No oitavo dia ele deverá pegar duas rolinhas ou dois pombinhos, ir até a entrada da Tenda Sagrada e, ali na presença de Deus, o Senhor , entregar as aves ao sacerdote.
15 Firist ɗin zai miƙa su, ɗaya domin hadaya don zunubi, ɗayan kuma domin hadaya ta ƙonawa. Ta haka zai yi kafara a gaban Ubangiji saboda mai ɗigar.
15 Este as oferecerá como sacrifício , uma delas como oferta para tirar pecados, e a outra como oferta que será completamente queimada. Assim, na presença do Senhor , o sacerdote fará a cerimônia de purificação, e o homem ficará puro.
16 “ ‘Sa’ad da namiji ya ɗigar maniyyi, dole yă wanke jikinsa gaba ɗaya da ruwa, zai kuma ƙazantu har yamma.
16 Quando um homem tiver perda de esperma, deverá tomar um banho e ficará impuro até o pôr do sol.
17 Dole a wanke duk riga ko fatar da yake da maniyyin a kansa da ruwa, zai kuma ƙazantu har yamma.
17 Qualquer roupa ou pedaço de couro em que cair esperma deverá ser lavado e ficará impuro até o pôr do sol.
18 Sa’ad da namiji ya kwana da mace ya kuwa zub da maniyyi, dole dukansu biyu su yi wanka, za su kuma ƙazantu har yamma.
18 Depois que um homem e uma mulher tiverem relações, os dois deverão tomar um banho e ficarão impuros até o pôr do sol.
19 “ ‘Sa’ad mace take al’adarta ta ƙa’ida, rashin tsabtarta ta al’adar zai ɗauki kwana bakwai, kuma duk wanda ya taɓa ta, zai ƙazantu har yamma.
19 Quando uma mulher tiver a sua menstruação, ficará impura sete dias. Quem tocar nela durante esse tempo ficará impuro até o pôr do sol.
20 “ ‘Duk abin da ta kwanta a kai a lokacin al’adarta zai ƙazantu, kuma duk abin da ta zauna a kai zai ƙazantu.
20 Qualquer cama em que ela se deitar e qualquer coisa em que se sentar ficarão impuras. Quem tocar na cama em que ela se deitou ou naquilo em que ela se sentou deverá lavar a roupa que estiver vestindo e tomar um banho; e ficará impuro até o pôr do sol.
21 Duk wanda ya taɓa gadonta dole yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma.
21 — ausente —
22 Duk wanda ya taɓa wani abin da ta zauna a kai, dole yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma.
22 — ausente —
23 Ko gado ne, ko kuwa wani abin da ta zauna a kai, sa’ad da wani ya taɓa shi, zai ƙazantu har yamma.
23 — ausente —
24 “ ‘In namiji ya kwana da ita, al’adarta kuwa ta taɓa shi, zai ƙazantu na kwana bakwai; duk kuma gadon da ya kwanta a kai, zai ƙazantu.
24 E o homem que tiver relações com a mulher durante a menstruação ficará impuro sete dias; e qualquer cama em que ele se deitar ficará impura.
25 “ ‘Idan mace tana ɗigar jini na tsawon kwanaki, ban da kwanakin ganin al’adarta, ko kuwa idan al’adarta ya wuce yawan kwanakin da ya kamata, to, za tă ƙazantu daidai kamar na kwanakin al’adar da ta saba yi. Wato, muddin tana cikin ɗiga, ta zama mai ƙazanta.
25 A mulher que tiver hemorragia ou que continuar menstruada além do tempo normal ficará impura como durante a menstruação.
26 Duk gadon da ta kwanta yayinda ta ci gaba da ɗiga zai zama marar tsarki, kamar yadda gadonta yake a lokacin al’adarta, kuma duk abin da ta zauna a kai zai zama marar tsarki, kamar yadda yake a lokacin al’adarta.
26 Qualquer cama em que ela se deitar e qualquer coisa em que se sentar durante esse tempo ficarão impuras.
27 Duk wanda ta taɓa su zai zama marar tsarki; dole yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma.
27 E quem tocar na cama ou naquilo em que ela se sentou ficará impuro e deverá lavar a roupa que estiver vestindo e tomar um banho; e ficará impuro até o pôr do sol.
28 “ ‘Sa’ad da aka tsabtacce ta daga ɗigarta, dole tă ɗauki kwana bakwai, bayan haka za tă zama mai tsarki.
28 Quando a hemorragia parar, ela deverá esperar sete dias e então estará pura .
29 A rana ta takwas, dole tă ɗauki kurciyoyi biyu ko tattabari biyu ta kawo su ga firist a bakin ƙofar Tentin Sujada.
29 No oitavo dia ela pegará duas rolinhas ou dois pombinhos, irá até a entrada da Tenda Sagrada e entregará as aves ao sacerdote.
30 Firist zai miƙa ɗaya saboda hadaya don zunubi, ɗayan kuma don hadaya ta ƙonawa. Ta haka zai yi kafara dominta a gaban Ubangiji saboda ƙazantar ɗigarta.
30 Este as oferecerá como sacrifício, uma delas como oferta para tirar pecados, e a outra como oferta que será completamente queimada. Assim, na presença de Deus, o Senhor , o sacerdote fará a cerimônia de purificação , e a mulher ficará pura .
31 “ ‘Ta haka za ka tsarkake Isra’ilawa daga rashin tsarkinsu, domin kada su mutu saboda rashin tsarkinsu ta wurin ƙazantar da wurin zamana wanda yake tsakiyarsu.’ ”
31 Essas leis são para livrar os israelitas das suas impurezas, a fim de que não morram por tornarem impura a Tenda Sagrada, que fica no meio do acampamento.
32 Waɗannan su ne ƙa’idodi a kan wanda yake ɗiga, da wanda yake zubar da maniyyi,
32 São essas as leis a respeito do homem que ficar impuro por causa de corrimento no membro ou de perda de esperma;
33 ƙa’idodi ne kuma ga mace wadda take al’ada, ga namiji ko macen da take ɗiga, ga kuma namijin da ya kwana da mace marar tsarki.
33 da mulher durante a menstruação; e do homem que tiver relações com uma mulher menstruada.
Atalhos do teclado
- Capítulo anterior←
- Próximo capítulo→
- Versículo anteriork
- Próximo versículoj
- Limpar seleçãoEsc
- Esta ajuda?
Estude este capítulo no WhatsApp
Peça à IA da Bíblia Fala para explicar Levítico 15, comparar traduções ou montar um estudo — tudo direto pelo WhatsApp.