Lucas 20
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (HAUSA) vs ARA
1 Wata rana da Yesu yana koyar da mutane, yana musu wa’azin bishara a filin haikalin, sai manyan firistoci da malaman dokoki, tare da dattawan suka zo wurinsa.
1 Aconteceu que, num daqueles dias, estando Jesus a ensinar o povo no templo e a evangelizar, sobrevieram os principais sacerdotes e os escribas, juntamente com os anciãos,
2 Suka ce masa, “Gaya mana, da wane iko kake yin waɗannan abubuwa. Wa ya ba ka wannan ikon?”
2 e o arguiram nestes termos: Dize-nos: com que autoridade fazes estas coisas? Ou quem te deu esta autoridade?
3 Ya amsa ya ce, “Ni ma zan yi muku wata tambaya. Ku faɗa mini,
3 Respondeu-lhes: Também eu vos farei uma pergunta; dizei-me:
4 baftismar Yohanna, daga sama ne ta fito, ko kuwa daga wurin mutane ne?”
4 o batismo de João era dos céus ou dos homens?
5 Sai suka yi shawara da junansu, suka ce, “In muka ce, ‘Daga sama ne,’ zai tambaya, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’
5 Então, eles arrazoavam entre si: Se dissermos: do céu, ele dirá: Por que não acreditastes nele?
6 Amma in kuma muka ce, ‘Daga mutane ne,’ dukan mutanen za su jajjefe mu da duwatsu, domin sun tabbata cewa, Yohanna annabi ne.”
6 Mas, se dissermos: dos homens, o povo todo nos apedrejará; porque está convicto de ser João um profeta.
7 Don haka, sai suka amsa cewa, “Ba mu san inda ta fito ba.”
7 Por fim, responderam que não sabiam.
8 Yesu ya ce, “To, ni ma ba zan gaya muku, ko da wane iko ne, nake yin waɗannan abubuwa ba.”
8 Então, Jesus lhes replicou: Pois nem eu vos digo com que autoridade faço estas coisas.
9 Sai ya ci gaba da gaya wa mutanen wannan misali ya ce, “Wani mutum ya yi gonar inabi, sai ya ba da hayarta ga waɗansu manoma, sa’an nan ya yi wata doguwar tafiya.
9 A seguir, passou Jesus a proferir ao povo esta parábola: Certo homem plantou uma vinha, arrendou-a a lavradores e ausentou-se do país por prazo considerável.
10 A lokacin girbi, sai ya aiki bawa zuwa wurin masu hayan, don su ba shi daga cikin ’ya’yan inabin. Amma ’yan hayan suka yi wa bawan nan dūka, suka kore shi hannu wofi.
10 No devido tempo, mandou um servo aos lavradores para que lhe dessem do fruto da vinha; os lavradores, porém, depois de o espancarem, o despacharam vazio.
11 Ya sāke aikan wani bawa, shi ma suka yi masa dūka, suka kunyata shi, suka kuma kore shi hannu wofi.
11 Em vista disso, enviou-lhes outro servo; mas eles também a este espancaram e, depois de o ultrajarem, o despacharam vazio.
12 Har yanzu, ya sāke aikan na uku, amma suka ji masa rauni, suka jefar da shi waje.
12 Mandou ainda um terceiro; também a este, depois de o ferirem, expulsaram.
13 “Sai mai gonar inabin ya ce, ‘Me zan yi? Zan aiki ɗana da nake ƙauna, wataƙila za su girmama shi.’
13 Então, disse o dono da vinha: Que farei? Enviarei o meu filho amado; talvez o respeitem.
14 “Amma da ’yan hayan suka gan shi, sai suka tattauna zancen, suka ce, ‘Wannan shi ne magājin, mu kashe shi sa’an nan gādon zai zama namu!’
14 Vendo-o, porém, os lavradores, arrazoavam entre si, dizendo: Este é o herdeiro; matemo-lo, para que a herança venha a ser nossa.
15 Sai suka fitar da shi waje, suka kashe shi.
15 E, lançando-o fora da vinha, o mataram. Que lhes fará, pois, o dono da vinha?
16 Zai zo ya karkashe masu hayan nan, ya ba wa waɗansu gonar inabin.”
16 Virá, exterminará aqueles lavradores e passará a vinha a outros. Ao ouvirem isto, disseram: Tal não aconteça!
17 Yesu ya zura musu ido ya ce, “To, mene ne ma’anar abin da aka rubuta cewa,
17 Mas Jesus, fitando-os, disse: Que quer dizer, pois, o que está escrito:
18 Duk wanda ya fāɗi a kan dutsen nan, zai kakkarye. Kuma in dutsen nan ya fāɗi a kan wani, zai murƙushe shi.”
18 Todo o que cair sobre esta pedra ficará em pedaços; e aquele sobre quem ela cair ficará reduzido a pó.
19 Malaman dokoki da manyan firistoci, suka nemi hanyar kama shi nan da nan, domin sun san cewa, ya yi wannan misali a kansu ne, amma suna jin tsoron mutane.
19 Naquela mesma hora, os escribas e os principais sacerdotes procuravam lançar-lhe as mãos, pois perceberam que, em referência a eles, dissera esta parábola; mas temiam o povo.
20 Sai suka sa masa ido, suka aiki ’yan leƙen asiri, waɗanda suka nuna kamar su masu gaskiya ne, suna nufin su kama shi game da abin da zai faɗa, domin su ba da shi ga gwamna mai mulki, da mai iko.
20 Observando-o, subornaram emissários que se fingiam de justos para verem se o apanhavam em alguma palavra, a fim de entregá-lo à jurisdição e à autoridade do governador.
21 Sai ’yan leƙen asirin suka tambaye shi, suka ce, “Malam, mun sani kana faɗin, kuma kana koyar da abin da yake daidai, ba ka kuma nuna bambanci, amma kana koyar da hanyar Allah bisa ga gaskiya.
21 Então, o consultaram, dizendo: Mestre, sabemos que falas e ensinas retamente e não te deixas levar de respeitos humanos, porém ensinas o caminho de Deus segundo a verdade;
22 Daidai ne mu biya haraji ga Kaisar, ko babu?”
22 é lícito pagar tributo a César ou não?
23 Ya gane makircinsu, sai ya ce musu,
23 Mas Jesus, percebendo-lhes o ardil, respondeu:
24 “Nuna mini dinari. Hoton wane ne, kuma rubutun wane ne a kai?”
24 Mostrai-me um denário. De quem é a efígie e a inscrição? Prontamente disseram: De César. Então, lhes recomendou Jesus:
25 Sai ya ce musu, “Ku ba wa Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba wa Allah abin da yake na Allah.”
25 Dai, pois, a César o que é de César e a Deus o que é de Deus.
26 Ba su iya kama shi a kan abin da ya faɗa a fili ba. Amsarsa ya ba su mamaki, shi ya sa suka yi shiru.
26 Não puderam apanhá-lo em palavra alguma diante do povo; e, admirados da sua resposta, calaram-se.
27 Waɗansu Sadukiyawa da suke cewa, ba tashin matattu, suka zo wurin Yesu da tambaya cewa,
27 Chegando alguns dos saduceus, homens que dizem não haver ressurreição,
28 “Malam, Musa ya rubuta mana cewa, ‘In ɗan’uwan wani mutum ya mutu, ya bar mata amma ba ’ya’ya, dole mutumin ya aure gwauruwar, ya samo wa ɗan’uwansa ’ya’ya.’
28 perguntaram-lhe: Mestre, Moisés nos deixou escrito que, se morrer o irmão de alguém, sendo aquele casado e não deixando filhos, seu irmão deve casar com a viúva e suscitar descendência ao falecido.
29 To, an yi waɗansu ’yan’uwa bakwai. Na fari ya auri wata mace, ya mutu ba ’ya’ya.
29 Ora, havia sete irmãos: o primeiro casou e morreu sem filhos;
30 Na biyun,
30 o segundo e o terceiro também desposaram a viúva;
31 da na ukun suka aure ta. Haka nan dukansu bakwai suka mutu babu ’ya’ya.
31 igualmente os sete não tiveram filhos e morreram.
32 A ƙarshe, ita macen ma ta mutu.
32 Por fim, morreu também a mulher.
33 Shin, a tashin matattu, matar wa za tă zama? Tun da su bakwan nan, sun aure ta.”
33 Esta mulher, pois, no dia da ressurreição, de qual deles será esposa? Porque os sete a desposaram.
34 Yesu ya amsa ya ce, “Mutanen zamanin nan suna aure, suna kuma ba da aure,
34 Então, lhes acrescentou Jesus: Os filhos deste mundo casam-se e dão-se em casamento;
35 amma su waɗanda aka ga sun cancantar kasancewa a zamanin can, da kuma na tashin matattu, ba za su yi aure, ko su ba da aure ba.
35 mas os que são havidos por dignos de alcançar a era vindoura e a ressurreição dentre os mortos não casam, nem se dão em casamento.
36 Kuma ba za su sāke mutuwa ba, gama su kamar mala’iku ne. Su ’ya’yan Allah ne, tun da su ’ya’yan tashin matattu ne.
36 Pois não podem mais morrer, porque são iguais aos anjos e são filhos de Deus, sendo filhos da ressurreição.
37 Amma bisa ga labari na bishiya nan, mai cin wuta da Musa ya gani a jeji, ko Musa ma, ya nuna cewa, matattu suna tashi. Gama ya kira Ubangiji, ‘Allah na Ibrahim, da Allah na Ishaku, da kuma Allah na Yaƙub.’
37 E que os mortos hão de ressuscitar, Moisés o indicou no trecho referente à sarça, quando chama ao Senhor o Deus de Abraão, o Deus de Isaque e o Deus de Jacó.
38 Shi ba Allah na matattu ba ne, amma na masu rai ne, gama a gare shi, duka na da rai.”
38 Ora, Deus não é Deus de mortos, e sim de vivos; porque para ele todos vivem.
39 Sai waɗansu malaman dokoki suka amsa suka ce, “Ka faɗi daidai, malam!”
39 Então, disseram alguns dos escribas: Mestre, respondeste bem!
40 Kuma ba wanda ya sami ƙarfin halin yin masa waɗansu tambayoyi.
40 Dali por diante, não ousaram mais interrogá-lo.
41 Sai Yesu ya ce musu, “Yaya suke cewa, ‘Kiristi ɗan Dawuda ne?’
41 Mas Jesus lhes perguntou: Como podem dizer que o Cristo é filho de Davi?
42 Dawuda da kansa ya faɗa a cikin Zabura,
42 Visto como o próprio Davi afirma no livro dos Salmos:
43 sai na sa abokan gābanka
43 até que eu ponha os teus inimigos por estrado dos teus pés.
44 Dawuda ya kira shi ‘Ubangiji.’ Ta, yaya zai zama ɗansa?”
44 Assim, pois, Davi lhe chama Senhor, e como pode ser ele seu filho?
45 Yayinda dukan mutane suna cikin sauraronsa, sai Yesu ya ce wa almajiransa,
45 Ouvindo-o todo o povo, recomendou Jesus a seus discípulos:
46 “Ku yi hankali da malaman dokoki. Sukan so sa manyan riguna suna zaga, suna sha’awan karɓan gaisuwa a wuraren kasuwanci, da kuma wuraren zama mafi daraja a majami’u, da wuraren bangirma a bukukkuwa.
46 Guardai-vos dos escribas, que gostam de andar com vestes talares e muito apreciam as saudações nas praças, as primeiras cadeiras nas sinagogas e os primeiros lugares nos banquetes;
47 Suna mamaye gidajen gwauraye, kuma don burga, suna dogayen addu’o’i. Ga irin waɗannan mutane, za a yi musu hukunci mai tsanani sosai.”
47 os quais devoram as casas das viúvas e, para o justificar, fazem longas orações; estes sofrerão juízo muito mais severo.
Atalhos do teclado
- Capítulo anterior←
- Próximo capítulo→
- Versículo anteriork
- Próximo versículoj
- Limpar seleçãoEsc
- Esta ajuda?
Estude este capítulo no WhatsApp
Peça à IA da Bíblia Fala para explicar Lucas 20, comparar traduções ou montar um estudo — tudo direto pelo WhatsApp.