Juízes 18

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (HAUSA) vs VC

Sair da comparação
VC Versão Católica
1 To, a kwanakin nan Isra’ila ba ta da sarki.
1 Naquele tempo não havia rei em Israel. Por essa mesma época a tribo de Dá buscava uma possessão para habitar nela, porque até então nada tinha recebido entre as tribos de Israel.
2 Saboda haka mutanen Dan suka aika jarumawa guda biyar daga Zora da Eshtawol don su leƙi asirin ƙasar su kuma bincike ta. Waɗannan mutanen sun wakilci dukan kabilar. Suka ce musu, “Ku je, ku bincike ƙasar.”
2 Os danitas enviaram cinco dos seus, cinco homens valorosos escolhidos dentre todas as suas famílias de Sorea e de Estaol, para explorarem cuidadosamente a terra: Ide, disseram-lhes, e examinai bem a terra. Foram e chegaram à montanha de Efraim, e entraram na casa de Micas, onde passaram a noite.
3 Sa’ad da suka yi kusa da gidan Mika, sai suka gane muryar saurayin nan Balawe; saboda haka suka shiga wurin suka tambaye shi, “Wa ya kawo ka nan? Me kake yi a nan? Me ya sa kake a nan?”
3 Perto da casa de Micas ouviram a voz do jovem levita e, aproximando-se dele, disseram-lhe: Quem te trouxe aqui? Que fazes aqui? Por que te encontras neste lugar?
4 Ya gaya musu abin da Mika ya faɗa masa ya ce, “Ya ɗauke ni aiki ya kuma sa in zama masa firist.”
4 Respondeu-lhes o jovem: Micas fez-me isto e isso; deu-me um salário e eu sirvo-lhe, de sacerdote.
5 Sa’an nan suka ce masa, “Muna roƙonka ka nemi mana nufin Allah don mu sani ko tafiyarmu tana da nasara.”
5 Consulta então, replicaram-lhe, o teu deus a fim de saber se nossa viagem será bem sucedida.
6 Firist ya amsa ya ce, “Ku sauka lafiya, gama tafiyarku tana da yardan Ubangiji.”
6 O sacerdote respondeu: Ide em paz: vossa viagem está sob o olhar de Deus.
7 Saboda haka mutum biyar ɗin suka tashi suka iso Layish, inda suka ga mutane suna zamansu a huce, kamar Sidoniyawa, ba sa zato ga tsaro. Kuma da yake ƙasarsu ba ta bukata kome, suna da wadata. Suna kuma nesa da Sidoniyawa, ba sa kuma hulɗa da kowa.
7 Os cinco homens puseram-se a caminho e foram até Lais. Viram ali um povo que habitava seguro, pacífico e tranqüilo, segundo o costume dos sidônios. Não havia naquele terra nenhum rei que dominasse sobre os seus habitantes, ou que os molestasse em coisa alguma. Viviam longe dos sidônios e não tinham relações com ninguém.
8 Da suka komo Zora da Eshtawol, ’yan’uwansu suka tambaye su, “Me kuka gano?”
8 Voltando para seus irmãos em Sorea e Estaol, estes disseram: Que pudestes fazer?
9 Suka ce, “Ku zo mu yaƙe su! Mun ga ƙasar tana da kyau sosai. Ba za ku yi wani abu ba? Kada ku yi wata-wata, ku je kun mallaki ƙasar.
9 Eles responderam: Vamos, subamos contra eles. Vimos a sua terra que é excelente. Por que ficais aí sem nada dizer? Não demoreis a pôr-vos em marcha para tomar posse dessa terra.
10 Sa’ad da kun kai can, za ku iske mutanen suna zama a sake, ƙasar kuwa mai faɗi ce wadda Allah ya sa a hannuwanku, ƙasar da ba tă rasa kome ba.”
10 Quando ali entrardes, encontrareis um povo que vive em segurança e uma terra espaçosa que Deus vos entregará nas mãos, uma região onde nada falta daquilo que a terra produz.
11 Sai mutane ɗari shida daga kabilar Dan suka yi ɗamarar yaƙi, suka tashi daga Zora da Eshtawol.
11 Seiscentos homens da família de Dá partiram, pois, de Sorea e de Estaol, munidos com armas de guerra
12 A kan hanyarsu suka kafa sansani kusa da Kiriyat Yeyarim a Yahuda. Shi ya sa a ana kira wurin nan yamma da Kiriyat Yeyarim Mahane Dan har wa yau.
12 e acamparam em Cariatiarim, em Judá. Por isso deu-se àquele lugar o nome de Mahanê-Dã, o qual assim se chama ainda hoje, e está situado ao ocidente de Cariatiarim.
13 Daga can suka tafi ƙasar tudu ta Efraim suka zo gidan Mika.
13 Dali passaram às montanhas de Efraim e chegaram à casa de Micas.
14 Sa’an nan mutum biyar ɗin nan da suka leƙi asirin ƙasar Layish suka ce wa ’yan’uwansu, “Kun san cewa ɗaya daga cikin gidajen nan yana da efod, waɗansu allolin iyali, siffar da aka sassaƙa da kuma gunki na zubi? To, kun san abin da za ku yi.”
14 E os cinco homens que tinham sido enviados a explorar a terra de Lais disseram aos seus irmãos: Sabeis que há nessa casa um efod, uns terafim e um ídolo fundido? Considerai agora o que tendes a fazer.
15 Saboda haka suka juya a wurin suka shiga gidan saurayin nan Balawe a wajen Mika suka gaishe shi.
15 Dirigiram-se para lá e entraram na casa do jovem levita, em casa de Micas, para saudá-lo e informar-se de como ia passando.
16 Mutanen Dan ɗari shida da suka sha ɗamarar yaƙi suka tsaya a bakin ƙofa.
16 Entretanto, os seiscentos danitas, armados como estavam, ficaram à porta.
17 Sai mutum biyar da suka leƙi asirin ƙasar suka shiga ciki suka ɗauke gunkin da aka sassaƙa, efod, sauran allolin gida da kuma gunki na zubi yayinda firist ɗin tare da mutane ɗari shida da suka yi ɗamarar yaƙi suna tsaye a bakin ƙofa.
17 Os cinco exploradores penetraram {sozinhos} na capela e tomaram o ídolo com o efod e os terafim, enquanto o sacerdote se achava com os seiscentos homens armados à entrada da porta.
18 Sa’ad da waɗannan mutane suka shiga gidan Mika suka ɗauke gunkin da aka sassaƙa, efod, sauran allolin gida da kuma gunki na zubi, sai firist ya ce musu, “Me kuke yi?”
18 Tiraram, pois, da casa de Micas, o ídolo, o efod e os terafim. O sacerdote disse-lhes: Que fazeis vós?
19 Suka ce, “Ka yi shiru! Kada ka ce wani abu. Zo tare da mu, ka zama mahaifinmu da kuma firist. Bai fi maka ka yi wa kabila da kuma zuriya a Isra’ila aikin firist ba, da ka bauta wa iyali guda kawai?”
19 Cala-te, responderam-lhe, põe a mão na boca e vem conosco; tu nos servirás de pai e de sacerdote. O que é melhor para ti: ser sacerdote na casa de um particular, ou numa tribo e numa família de Israel?
20 Sai firist ya yi farin ciki. Ya ɗauki efod, sauran allolin gida da siffar da aka sassaƙa ya tafi tare da mutanen.
20 Alegrou-se o coração do sacerdote, e ele, tomando o efod, os terafim e o ídolo, foi com a tropa.
21 Suka sa ’ya’yansu ƙanana a gaba, dabbobinsu da mallakansu a gabansu, suka juya suka tafi.
21 Puseram-se de novo a caminho, precedidos das crianças, do gado e das bagagens.
22 Sa’ad da suka yi ɗan nisa daga gidan Mika, sai aka kira mutanen da suke maƙwabtakar da Mika suka taru suka bi mutanen Dan suka cim musu.
22 Estando eles já longe da casa de Micas, os vizinhos deste ajuntaram-se e perseguiram os danitas.
23 Da suna ihu suna binsu, sai mutanen Dan suka waiga suka cewa Mika, “Mece ce damuwarka da ka kira mutanenka su zo su fāɗa mana?”
23 Interrogados, os filhos de Dã voltaram-se e disseram a Micas: Que queres tu, e por que trazes toda essa gente?
24 Ya amsa ya ce, “Kun kwashe allolin da na yi, da kuma firist nawa, kuka tafi. Me kuma nake da shi? Yaya za ku ce, ‘Mece ce damuwata?’ ”
24 Ele respondeu: Tirastes os meus deuses que fiz para mim, tomastes o sacerdote e partistes. Que me resta agora? E como podeis perguntar o que quero?
25 Mutanen Dan suka ce, “Kada ka kuskura ka ce kome, in ba haka ba mutanen nan za su harzuƙa, da kai da iyalinka duka ku rasa rayukanku.”
25 Os danitas replicaram: Nem mais uma palavra diante de nós! Não suceda que alguns se impacientem contra vós e percais a vida, tu e tua família!
26 Saboda haka mutanen Dan suka kama hanyarsu, Mika kuwa da ya ga an fi ƙarfinsa, sai ya juya ya koma gida.
26 E os danitas continuaram o seu caminho. Micas, vendo que aqueles homens eram mais fortes que ele, voltou para a sua casa.
27 Sa’an nan suka ɗauko abin da Mika ya yi, da firist nasa, suka tafi Layish, suka fāɗa wa mutanen da suke zaman lafiya, ransu kuma a kwance. Suka fāɗa musu suka kuma ƙone birninsu.
27 Desse modo, tomaram os danitas a obra que Micas tinha feito, juntamente com o seu sacerdote. Atacaram então Lais, um povo pacífico e seguro, passaram-no ao fio da espada e queimaram a cidade.
28 Ba wanda zai cece su domin suna nesa da Bet-Sidon kuma ba sa hulɗa da kowa. Birnin yana a kwari kusa da Bet-Rekob.
28 Não houve quem a salvasse, porque estava longe de Sidon e não tinham relações com ninguém. Essa cidade estava situada no vale pertencente a Bet-Roob. Os danitas reedificaram a cidade e habitaram-na,
29 Suka sa wa birnin suna Dan, wato, sunan kakansu Dan, wanda aka haifa wa Isra’ila, ko da yake a dā ana kira birnin Layish.
29 chamando-a cidade de Dã, nome de seu pai, que tinha nascido de Israel; a cidade chamava-se primitivamente Lais.
30 A can mutanen Dan suka kafa wa kansu gumaka, Yonatan ɗan Gershom, ɗan Musa, da ’ya’yansa maza firistoci ne na kabilar Dan har lokacin da aka kwashe mutane zuwa bauta.
30 E erigiram em seguida o ídolo. Jonatã, filho de Gersã filho de Moisés, e seus descendentes foram sacerdotes na tribo de Dã até o dia de sua deportação.
31 Suka ci gaba da amfani da gumakan da Mika ya yi, a duk wannan lokacin gidan Allah yana a Shilo.
31 O ídolo de Micas foi conservado entre eles durante todo o tempo que o santuário de Deus ficou em Silo.

Ler em outra tradução

Comparar com outra

Estude este capítulo no WhatsApp

Peça à IA da Bíblia Fala para explicar Juízes 18, comparar traduções ou montar um estudo — tudo direto pelo WhatsApp.