1 Sai Ayuba ya amsa,
2 “Yadda ka taimaki marar ƙarfi!
3 Ka ba marar hikima shawara!
4 Wane ne ya taimake ka ka yi waɗannan maganganu?
5 “Matattu suna cikin azaba, waɗanda suke ƙarƙashin ruwaye
6 Mutuwa tsirara take a gaban Allah;
7 Ya shimfiɗa arewancin sararin sama a sarari;
8 Ya naɗe ruwaye a cikin gizagizansa,
9 Ya rufe fuskar wata,
10 ya zāna iyakar fuskar ruwa
11 Madogaran sama sun girgiza,
12 Da ikonsa ya kwantar da teku;
13 Da numfashinsa ya sa sararin sama ya yi kyau
14 Waɗannan kaɗan ke nan daga cikin ayyukansa masu yawa.