Gênesis 47

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (HAUSA) vs NVI

Sair da comparação
NVI Nova Versão Internacional
1 Yusuf ya tafi yă faɗa wa Fir’auna, “Mahaifina da ’yan’uwana, tare da garkunansu da shanunsu da kome da suke da shi, sun zo daga ƙasar Kan’ana, suna kuwa a Goshen yanzu.”
1 José foi dar as notícias ao faraó: "Meu pai e meus irmãos chegaram de Canaã com suas ovelhas, seus bois e tudo o que lhes pertence, e estão agora em Gósen".
2 Sai ya zaɓi mutum biyar daga cikin ’yan’uwansa, ya gabatar da su a gaban Fir’auna.
2 Depois escolheu cinco de seus irmãos e os apresentou ao faraó.
3 Fir’auna ya tambayi ’yan’uwan, “Mece ce sana’arku?”
3 Perguntou-lhes o faraó: "Em que vocês trabalham? " Eles lhe responderam: "Teus servos são pastores, como os nossos antepassados".
4 Suka kuma ce masa, “Mun zo, mu zauna a nan na ɗan lokaci, gama yunwa ta yi tsanani a Kan’ana, dabbobin bayinka kuma ba su da wurin kiwo. Saboda haka yanzu, muna roƙonka, bari bayinka su zauna a Goshen.”
4 Disseram-lhe ainda: "Viemos morar aqui por uns tempos, porque a fome é rigorosa em Canaã, e os rebanhos de teus servos não têm pastagem. Agora, por favor, permite que teus servos se estabeleçam em Gósen".
5 Fir’auna ya ce wa Yusuf, “Mahaifinka da ’yan’uwanka sun zo maka,
5 Então o faraó disse a José: "Seu pai e seus irmãos vieram a você,
6 ƙasar Masar kuma tana gabanka, ka zaunar da mahaifinka da ’yan’uwanka a sashe mafi kyau na ƙasar, bari su zauna a Goshen. Idan kuma ka ga waɗansu a cikinsu da suka fi dacewa, sai ka sa su lura mini da shanuna.”
6 e a terra do Egito está a sua disposição; faça com que seu pai e seus irmãos habitem na melhor parte da terra. Deixe-os morar em Gósen. E se você vê que alguns deles são competentes, coloque-os como responsáveis por meu rebanho".
7 Sa’an nan Yusuf ya shigar da Yaƙub mahaifinsa, ya gabatar da shi a gaban Fir’auna. Bayan Yaƙub ya albarkaci Fir’auna,
7 Então José levou seu pai Jacó ao faraó e o apresentou a ele. Depois Jacó abençoou o faraó,
8 sai Fir’auna ya tambaye shi, “Shekarunka nawa da haihuwa?”
8 e este lhe perguntou: "Quantos anos o senhor tem? "
9 Yaƙub kuwa ya ce wa Fir’auna, “Shekarun hijirata, shekaru ɗari da talatin ne. Shekaruna kaɗan ne cike da wahala, ba za a kuwa daidaita su da shekarun hijirar kakannina ba.”
9 Jacó respondeu ao faraó: "São cento e trinta os anos da minha peregrinação. Foram poucos e difíceis e não chegam aos anos da peregrinação dos meus antepassados".
10 Sai Yaƙub ya albarkaci Fir’auna, ya yi masa bankwana, sa’an nan ya fita.
10 Então, Jacó abençoou o faraó e retirou-se.
11 Ta haka Yusuf ya zaunar da mahaifinsa da ’yan’uwansa a Masar, ya ba su mallaka a sashe mafi kyau na ƙasar, a yankin nan na Rameses, kamar yadda Fir’auna ya umarta.
11 José instalou seu pai e seus irmãos e deu-lhes propriedade na melhor parte das terras do Egito, na região de Ramessés, conforme a ordem do faraó.
12 Yusuf ya kuma tanada wa mahaifinsa da kuma ’yan’uwansa da dukan gidan mahaifinsa, abinci bisa ga yawan ’ya’yansu.
12 Providenciou também sustento para seu pai, para seus irmãos e para toda a sua família, de acordo com o número de filhos de cada um.
13 A yanzu, a cikin ƙasar duka, ba abinci, gama yunwa ta yi tsanani ƙwarai, har ƙasar Masar da ƙasar Kan’ana suka shiga matsananciyar wahala!
13 Não havia mantimento em toda a região, pois a fome era rigorosa; tanto o Egito como Canaã desfaleciam por causa da fome.
14 Yusuf ya tattara dukan kuɗaɗen da suke a Masar da Kan’ana don biyan hatsin da suke saya, ya kuwa kawo su a fadan Fir’auna.
14 José recolheu toda a prata que circulava no Egito e em Canaã, dada como pagamento do trigo que o povo comprava, e levou-a ao palácio do faraó.
15 Sa’ad da kuɗin mutanen Masar da Kan’ana suka ƙare, dukan Masar ta zo wurin Yusuf ta ce, “Ka ba mu abinci. Me zai sa mu mutu a idanunka? Kuɗinmu duk sun ƙare.”
15 Quando toda a prata do Egito e de Canaã se esgotou, todos os egípcios foram suplicar a José: "Dá-nos comida! Não nos deixes morrer só porque a nossa prata acabou".
16 Yusuf ya ce, “To, ku kawo dabbobinku, zan sayar muku da abinci a madadin dabbobinku, tun da kuɗinku ya ƙare.”
16 E José lhes disse: "Tragam então os seus rebanhos, e em troca lhes darei trigo, uma vez que a prata de vocês acabou".
17 Saboda haka suka kawo dabbobinsu wa Yusuf, ya kuma ba su abinci a madadin dawakai, tumaki da awaki, shanu da jakunansu. Ya kuwa ba su abinci a madadin dabbobinsu, a wannan shekara.
17 E trouxeram a José os rebanhos, e ele deu-lhes trigo em troca de cavalos, ovelhas, bois e jumentos. Durante aquele ano inteiro ele os sustentou em troca de todos os seus rebanhos.
18 Sa’ad da wannan shekara ta ƙare, sai suka zo wurinsa a shekara ta biye suka ce, “Ba za mu ɓoye maka ba ranka yă daɗe, kuɗinmu sun ƙare, dabbobinmu kuma sun zama naka. Ranka yă daɗe, in ban da jikunanmu da gonakinmu, ba abin da ya rage mana.
18 O ano passou, e no ano seguinte voltaram a José, dizendo: "Não temos como esconder de ti, meu senhor, que uma vez que a nossa prata acabou e os nossos rebanhos lhe pertencem, nada mais nos resta para oferecer, a não ser os nossos próprios corpos e as nossas terras.
19 Kada ka bar mu mu mutu, ka yi wata dabara! Kada ka bari mu rasa gonakinmu. Ka musaye mu da abinci, mu da gonakinmu. Mu kuwa za mu zama bayin Fir’auna. Ka ba mu iri don mu rayu, kada mu mutu, don kuma kada gonakin ƙasarmu su zama kango.”
19 Não deixes que morramos e que as nossas terras pereçam diante dos teus olhos! Compra-nos, juntamente com as terras, em troca de trigo, e nós, com as nossas terras, seremos escravos do faraó. Dá-nos sementes para que sobrevivamos e não morramos de fome, a fim de que a terra não fique desolada".
20 Ta haka Yusuf ya saya wa Fir’auna ƙasar Masar duka, gama Masarawa duka sun sayar da gonakinsu, saboda yunwa ta tsananta musu. Ƙasar ta zama mallakar Fir’auna.
20 Assim, José comprou todas as terras do Egito para o faraó. Todos os egípcios tiveram que vender os seus campos, pois a fome os obrigou a isso. A terra tornou-se propriedade do faraó.
21 Yusuf kuwa ya mai da mutanen bayi, daga wannan iyakar Masar zuwa wancan.
21 Quanto ao povo, José o reduziu à servidão, de uma à outra extremidade do Egito.
22 Amma bai sayi gonakin firistoci ba, gama suna karɓa rabo daga Fir’auna ne, suna kuma da isashen abinci daga rabon da Fir’auna yake ba su. Dalilin ke nan da ba su sayar da gonakinsu ba.
22 Somente as terras dos sacerdotes não foram compradas, porque, por lei, esses recebiam sustento regular do faraó, e disso viviam. Por isso não tiveram que vender as suas terras.
23 Yusuf ya ce wa mutane, “Yanzu da na saye ku da kuma gonakinku a yau wa Fir’auna, ga iri don ku shuka a gonaki.
23 Então José disse ao povo: "Ouçam! Hoje comprei vocês e suas terras para o faraó; aqui estão as sementes para que cultivem a terra.
24 Amma sa’ad da hatsi suka nuna, za ku ba da kashi ɗaya bisa biyar ga Fir’auna. Sauran kashi huɗu bisa biyar kuma ku riƙe a matsayin iri don gonaki da kuma abinci wa kanku da gidajenku da kuma ’ya’yanku.”
24 Mas vocês darão a quinta parte das suas colheitas ao faraó. Os outros quatro quintos ficarão para vocês como sementes para os campos e como alimento para vocês, seus filhos e os que vivem em suas casas".
25 Suka ce, “Ka ceci rayukanmu, in ya gamshe ka, ranka yă daɗe, za mu zama bayin Fir’auna.”
25 Eles disseram: "Meu senhor, tu nos salvaste a vida. Visto que nos favoreceste, seremos escravos do faraó".
26 Ta haka Yusuf ya kafa wannan ya zama doka game da ƙasa a Masar, har yă zuwa yau cewa kashi ɗaya bisa biyar na amfani gona ya zama na Fir’auna. Gonakin firistoci ne kaɗai ba su zama na Fir’auna ba.
26 Assim, quanto à terra, José estabeleceu o seguinte decreto no Egito, que permanece até hoje: Um quinto da produção pertence ao faraó. Somente as terras dos sacerdotes não se tornaram propriedade do faraó.
27 To, Isra’ilawa suka zauna a Masar a yankin Goshen. Suka mallaki filaye a can, suka riɓaɓɓanya suka ƙaru ƙwarai.
27 Os israelitas se estabeleceram no Egito, na região de Gósen. Lá adquiriram propriedades, foram prolíferos e multiplicaram-se muito.
28 Yaƙub ya yi zama a Masar shekaru goma sha bakwai, yawan shekarunsa duka sun zama ɗari da arba’in da bakwai.
28 Jacó viveu dezessete anos no Egito, e os anos da sua vida chegaram a cento e quarenta e sete.
29 Sa’ad da lokaci ya gabato da Isra’ila zai mutu, sai ya kira ɗansa Yusuf, ya ce masa, “Ka yi mini wannan alheri, ka sa hannunka ƙarƙashin cinyar ƙafata, ka yi mini alkawari saboda ina roƙonka kaɗa ka bizne ni a Masar,
29 Aproximando-se a hora da sua morte, Israel chamou seu filho José e lhe disse: "Se quer agradar-me, ponha a mão debaixo da minha coxa e prometa que será bondoso e fiel comigo: Não me sepulte no Egito.
30 amma sa’ad da na huta da kakannina, ka ɗauke ni, ka fid da ni daga Masar, ka binne ni a inda aka binne su.”
30 Quando eu descansar com meus pais, leve-me daqui do Egito e sepulte-me junto a eles". José respondeu: "Farei como o senhor me pede".
31 Yaƙub ya ce, “Ka rantse mini.” Sai Yusuf ya rantse masa, Isra’ila kuwa ya yi godiya ga Allah yayinda ya jingina a kan sandansa.
31 Mas Jacó insistiu: "Jure-me". E José lhe jurou, e Israel curvou-se apoiado em seu bordão.

Ler em outra tradução

Comparar com outra

Estude este capítulo no WhatsApp

Peça à IA da Bíblia Fala para explicar Gênesis 47, comparar traduções ou montar um estudo — tudo direto pelo WhatsApp.