Gênesis 42
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (HAUSA) vs ARA
1 Sa’ad da Yaƙub ya sami labari cewa akwai hatsi a Masar, sai ya ce wa ’ya’yansa maza, “Don me kuke duban juna kawai?”
1 Sabedor Jacó de que havia mantimento no Egito, disse a seus filhos: Por que estais aí a olhar uns para os outros?
2 Ya ci gaba, “Na ji cewa akwai hatsi a Masar. Ku gangara can ku sayo mana, domin mu rayu kada mu mutu.”
2 E ajuntou: Tenho ouvido que há cereais no Egito; descei até lá e comprai-nos deles, para que vivamos e não morramos.
3 Sai goma daga cikin ’yan’uwan Yusuf suka gangara don su saya hatsi daga Masar.
3 Então, desceram dez dos irmãos de José, para comprar cereal do Egito.
4 Amma Yaƙub bai aiki Benyamin, ɗan’uwan Yusuf tare da sauran ba, gama yana tsoro kada wani abu yă faru da shi.
4 A Benjamim, porém, irmão de José, não enviou Jacó na companhia dos irmãos, porque dizia: Para que não lhe suceda, acaso, algum desastre.
5 Sai ’ya’yan Yaƙub suka isa Masar tare da sauran mutanen don sayen abinci, gama yunwar ta kai yankin Kan’ana ma.
5 Entre os que iam, pois, para lá, foram também os filhos de Israel; porque havia fome na terra de Canaã.
6 To, Yusuf ne gwamnar ƙasar wanda yake sayar da hatsi ga dukan mutanenta. Saboda haka sa’ad da ’yan’uwan Yusuf suka isa, sai suka rusuna masa har ƙasa da fuskokinsu.
6 José era governador daquela terra; era ele quem vendia a todos os povos da terra; e os irmãos de José vieram e se prostraram rosto em terra, perante ele.
7 Nan da nan da Yusuf ya ga ’yan’uwansa, sai ya gane su, amma ya yi kamar baƙo, ya kuma yi musu magana da tsawa. Ya tambaya, “Daga ina kuka fito?”
7 Vendo José a seus irmãos, reconheceu-os, porém não se deu a conhecer, e lhes falou asperamente, e lhes perguntou: Donde vindes? Responderam: Da terra de Canaã, para comprar mantimento.
8 Ko da yake Yusuf ya gane ’yan’uwansa, su ba su gane shi ba.
8 José reconheceu os irmãos; porém eles não o reconheceram.
9 Sa’an nan ya tuna da mafarkansa game da su, ya kuma ce musu, “Ku ’yan leƙen asiri ne! Kun zo don ku leƙi asirin ƙasar ku ga inda ba ta da tsaro.”
9 Então, se lembrou José dos sonhos que tivera a respeito deles e lhes disse: Vós sois espiões e viestes para ver os pontos fracos da terra.
10 Suka amsa suka ce, “A’a, ranka yă daɗe, bayinka sun zo don saya abinci ne.
10 Responderam-lhe: Não, senhor meu; mas vieram os teus servos para comprar mantimento.
11 Mu duka ’ya’yan mutum ɗaya maza ne. Bayinka mutane ne masu gaskiya, ba ’yan leƙen asiri ba ne.”
11 Somos todos filhos de um mesmo homem; somos homens honestos; os teus servos não são espiões.
12 Ya ce musu “Sam! Kun zo ne ku ga inda ƙasarmu babu tsaro.”
12 Ele, porém, lhes respondeu: Nada disso; pelo contrário, viestes para ver os pontos fracos da terra.
13 Amma suka amsa suka ce, “Bayinka dā su goma sha biyu ne, ’yan’uwa, ’ya’yan mutum guda maza, wanda yake zama a ƙasar Kan’ana. Ƙaraminmu yanzu yana tare da mahaifinmu, ɗayan kuma ya rasu.”
13 Eles disseram: Nós, teus servos, somos doze irmãos, filhos de um homem na terra de Canaã; o mais novo está hoje com nosso pai, outro já não existe.
14 Yusuf ya ce musu, “Daidai ne yadda na faɗa muku. Ku ’yan leƙen asiri ne!
14 Então, lhes falou José: É como já vos disse: sois espiões.
15 Ga kuwa yadda za a gwada ku. Muddin Fir’auna yana a raye, ba za ku bar wannan wuri ba sai ƙaramin ɗan’uwanku ya zo nan.
15 Nisto sereis provados: pela vida de Faraó, daqui não saireis, sem que primeiro venha o vosso irmão mais novo.
16 Ku aiki ɗaya daga cikinku yă kawo ɗan’uwanku; za a sa sauranku a kurkuku, saboda a gwada maganarku a ga ko gaskiya ce kuke faɗi. In ba haka ba, to, da ran Fir’auna, ku ’yan leƙen asiri ne!”
16 Enviai um dentre vós, que traga vosso irmão; vós ficareis detidos para que sejam provadas as vossas palavras, se há verdade no que dizeis; ou se não, pela vida de Faraó, sois espiões.
17 Ya kuwa sa su duka a kurkuku na kwana uku.
17 E os meteu juntos em prisão três dias.
18 A rana ta uku, Yusuf ya ce musu, “Ku yi wannan za ku kuwa rayu, gama ina tsoron Allah.
18 Ao terceiro dia, disse-lhes José: Fazei o seguinte e vivereis, pois temo a Deus.
19 In ku mutane masu gaskiya ne, ku bar ɗaya daga cikin ’yan’uwanku yă zauna a kurkuku, yayinda sauranku su tafi, su kai hatsi don gidajenku da suke yunwa.
19 Se sois homens honestos, fique detido um de vós na casa da vossa prisão; vós outros ide, levai cereal para suprir a fome das vossas casas.
20 Amma dole ku kawo ƙaramin ɗan’uwanku gare ni, saboda a tabbatar da maganarku har ba za ku mutu ba.” Suka kuwa yi haka.
20 E trazei-me vosso irmão mais novo, com o que serão verificadas as vossas palavras, e não morrereis. E eles se dispuseram a fazê-lo.
21 Sai suka ce wa juna, “Tabbatacce ana hukunta mu ne saboda ɗan’uwanmu. Mun ga yadda ya yi wahala sa’ad da ya roƙe mu saboda ransa, amma ba mu saurare shi ba, shi ya sa wannan wahala ta zo mana.”
21 Então, disseram uns aos outros: Na verdade, somos culpados, no tocante a nosso irmão, pois lhe vimos a angústia da alma, quando nos rogava, e não lhe acudimos; por isso, nos vem esta ansiedade.
22 Ruben ya amsa, “Ban faɗa muku cewa kada ku ɗauki alhakin yaron nan ba, sai kuka ƙi ji, to, yau ga alhakin jininsa muke biya.”
22 Respondeu-lhes Rúben: Não vos disse eu: Não pequeis contra o jovem? E não me quisestes ouvir. Pois vedes aí que se requer de nós o seu sangue.
23 Ba su san cewa Yusuf yana jin su ba, da yake yana amfani da mai fassara ne.
23 Eles, porém, não sabiam que José os entendia, porque lhes falava por intérprete.
24 Sai ya juya daga gare su ya yi kuka, sa’an nan ya dawo ya yi musu magana kuma. Ya sa aka ɗauke Simeyon daga gare su, aka daure shi a idanunsu.
24 E, retirando-se deles, chorou; depois, tornando, lhes falou; tomou a Simeão dentre eles e o algemou na presença deles.
25 Yusuf ya yi umarni a cika buhunansu da hatsi, a kuma sa azurfan kowane mutum a cikin buhunsa, a kuma ba su kalaci don tafiyarsu. Bayan aka yi musu wannan,
25 Ordenou José que lhes enchessem de cereal os sacos, e lhes restituíssem o dinheiro, a cada um no saco de cereal, e os suprissem de comida para o caminho; e assim lhes foi feito.
26 suka jibga hatsinsu a kan jakuna, sai suka kama hanya.
26 E carregaram o cereal sobre os seus jumentos e partiram dali.
27 A wurin da suka tsaya don su kwana, ɗaya daga cikinsu ya buɗe buhunsa don yă ciyar da jakinsa, sai ya ga azurfansa a bakin buhunsa.
27 Abrindo um deles o saco de cereal, para dar de comer ao seu jumento na estalagem, deu com o dinheiro na boca do saco de cereal.
28 Sai ya ce wa ’yan’uwansa, “An mayar mini da azurfata. Ga shi a cikin buhuna.”
28 Então, disse aos irmãos: Devolveram o meu dinheiro; aqui está na boca do saco de cereal. Desfaleceu-lhes o coração, e, atemorizados, entreolhavam-se, dizendo: Que é isto que Deus nos fez?
29 Sa’ad da suka zo wurin mahaifinsu Yaƙub a ƙasar Kan’ana, suka faɗa masa dukan abin da ya faru da su. Suka ce,
29 E vieram para Jacó, seu pai, na terra de Canaã, e lhe contaram tudo o que lhes acontecera, dizendo:
30 “Mutumin da yake shugaba a ƙasar ya yi mana matsananciyar magana, ya kuma ɗauke mu tamƙar ’yan leƙen asirin ƙasa.
30 O homem, o senhor da terra, falou conosco asperamente e nos tratou como espiões da terra.
31 Amma muka ce masa, ‘Mu masu gaskiya ne; mu ba ’yan leƙen asiri ba ne.
31 Dissemos-lhe: Somos homens honestos; não somos espiões;
32 Dā mu ’yan’uwa ne goma sha biyu, ’ya’yan mahaifi guda maza. Ɗayanmu ya rasu, kuma ƙaramin yanzu yana tare da mahaifinmu a Kan’ana.’
32 somos doze irmãos, filhos de um mesmo pai; um já não existe, e o mais novo está hoje com nosso pai na terra de Canaã.
33 “Sai mutumin wanda yake shugaba a kan ƙasar ya ce mana, ‘Ga yadda zan san ko ku mutane masu gaskiya ne. Ku bar ɗaya daga cikin ’yan’uwanku a nan tare da ni, ku ɗauki abinci domin gidajenku masu yunwa, ku tafi.
33 Respondeu-nos o homem, o senhor da terra: Nisto conhecerei que sois homens honestos: deixai comigo um de vossos irmãos, tomai o cereal para remediar a fome de vossas casas e parti;
34 Amma ku kawo mini ƙaramin ɗan’uwanku domin in san cewa ku ba ’yan leƙen asiri ba ne, amma mutane ne masu gaskiya. Sa’an nan zan mayar muku da ɗan’uwanku, ku kuma iya yin sana’a a ƙasar.’ ”
34 trazei-me vosso irmão mais novo; assim saberei que não sois espiões, mas homens honestos. Então, vos entregarei vosso irmão, e negociareis na terra.
35 Yayinda suke juyewa hatsi daga buhunansu, sai ga ƙunshin azurfan kowane mutum a buhunsa! Sa’ad da su da mahaifinsu suka ga ƙunshe-ƙunshen kuɗi, suka firgita.
35 Aconteceu que, despejando eles os sacos de cereal, eis cada um tinha a sua trouxinha de dinheiro no saco de cereal; e viram as trouxinhas com o dinheiro, eles e seu pai, e temeram.
36 Yaƙub mahaifinsu, ya ce musu, “Kun sa ni rashin ’ya’yana. Yusuf ya rasu, Simeyon kuma ba ya nan, yanzu kuma kuna so ku ɗauki Benyamin. Kome yana gāba da ni!”
36 Então, lhes disse Jacó, seu pai: Tendes-me privado de filhos: José já não existe, Simeão não está aqui, e ides levar a Benjamim! Todas estas coisas me sobrevêm.
37 Sai Ruben ya ce wa mahaifinsa, “Ka kashe dukan ’ya’yana maza, in ban dawo da shi gare ka ba. Ka sa shi ga kulawata, zan kuwa dawo da shi.”
37 Mas Rúben disse a seu pai: Mata os meus dois filhos, se to não tornar a trazer; entrega-mo, e eu to restituirei.
38 Amma Yaƙub ya ce, “Ɗana ba zai gangara zuwa can tare da ku ba, ɗan’uwansa ya rasu, shi ne kaɗai ya rage. In wani abu ya faru da shi a tafiyar da za ku yi, za ku sa furfurata ta gangara zuwa kabari cikin baƙin ciki.”
38 Ele, porém, disse: Meu filho não descerá convosco; seu irmão é morto, e ele ficou só; se lhe sucede algum desastre no caminho por onde fordes, fareis descer minhas cãs com tristeza à sepultura.
Atalhos do teclado
- Capítulo anterior←
- Próximo capítulo→
- Versículo anteriork
- Próximo versículoj
- Limpar seleçãoEsc
- Esta ajuda?
Estude este capítulo no WhatsApp
Peça à IA da Bíblia Fala para explicar Gênesis 42, comparar traduções ou montar um estudo — tudo direto pelo WhatsApp.