Ezequiel 44
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (HAUSA) vs ARA
1 Sai mutumin ya komo da ni zuwa ƙofar waje na wuri mai tsarki, wadda take fuskantar gabas, tana kuwa a rufe.
1 Então, o homem me fez voltar para o caminho da porta exterior do santuário, que olha para o oriente, a qual estava fechada.
2 Ubangiji ya ce mini, “Wannan ƙofar za tă kasance a rufe. Ba za a buɗe ta ba; ba wanda zai shiga ta wurinta. Za tă kasance a rufe domin Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya shiga ta wurinta.
2 Disse-me o Senhor : Esta porta permanecerá fechada, não se abrirá; ninguém entrará por ela, porque o Senhor , Deus de Israel, entrou por ela; por isso, permanecerá fechada.
3 Sarki kansa ne kaɗai zai zauna a hanyar shiga don yă ci a gaban Ubangiji. Zai shiga ta hanyar shirayin hanyar shiga yă kuma fita a wannan hanya.”
3 Quanto ao príncipe, ele se assentará ali por ser príncipe, para comer o pão diante do Senhor ; pelo vestíbulo da porta entrará e por aí mesmo sairá.
4 Sa’an nan mutumin ya kawo ni ta hanyar ƙofar arewa zuwa gaban haikali. Na duba na kuma ga ɗaukakar Ubangiji tana cika haikalin Ubangiji, sai na fāɗi rubda ciki.
4 Depois, o homem me levou pela porta do norte, diante da casa; olhei, e eis que a glória do Senhor enchia a Casa do Senhor ; então, caí rosto em terra.
5 Ubangiji ya ce mini, “Ɗan mutum, ka lura sosai, ka saurara sosai ka kuma mai da hankali ga kome da na faɗa maka game da dukan ƙa’idodi game da haikalin Ubangiji. Ka lura sosai da ƙofar shigar haikali da kuma dukan ƙofofin wuri mai tsarki.
5 Disse-me o Senhor : Filho do homem, nota bem, e vê com os próprios olhos, e ouve com os próprios ouvidos tudo quanto eu te disser de todas as determinações a respeito da Casa do Senhor e de todas as leis dela; nota bem quem pode entrar no templo e quem deve ser excluído do santuário.
6 Faɗa wa ’yan tawayen gidan Isra’ila, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ayyukan banƙyamarku sun isa haka, ya gidan Isra’ila!
6 Dize aos rebeldes, à casa de Israel: Assim diz o Senhor Deus: Bastem-vos todas as vossas abominações, ó casa de Israel!
7 Ban da dukan sauran ayyukanku na banƙyama, kun kawo baƙi marasa kaciya a zuciya da jiki a wurina mai tsarki, kun kuma ƙazantar da haikalina yayinda kuke miƙa mini abinci, kitse da kuma jini, kun kuma karya alkawarina.
7 Porquanto introduzistes estrangeiros, incircuncisos de coração e incircuncisos de carne, para estarem no meu santuário, para o profanarem em minha casa, quando ofereceis o meu pão, a gordura e o sangue; violastes a minha aliança com todas as vossas abominações.
8 A maimakon yin ayyukanku bisa ga abubuwana masu tsarki, kun sa waɗansu su lura da wurina mai tsarki.
8 Não cumpristes as prescrições a respeito das minhas coisas sagradas; antes, constituístes em vosso lugar estrangeiros para executarem o serviço no meu santuário.
9 Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ba baƙo marar kaciya a zuciya da jiki da zai shiga wurina mai tsarki, kai, har ma da baƙin da suke zama a cikin Isra’ila.
9 Assim diz o Senhor Deus: Nenhum estrangeiro que se encontra no meio dos filhos de Israel, incircunciso de coração ou incircunciso de carne, entrará no meu santuário.
10 “ ‘Lawiyawan da suka yi nesa da ni sa’ad da Isra’ila suka kauce da kuma waɗanda suka karkata daga gare ni suka bi gumakansu, dole su ɗauki alhakin zunubinsu.
10 Os levitas, porém, que se apartaram para longe de mim, quando Israel andava errado, que andavam transviados, desviados de mim, para irem atrás dos seus ídolos, bem levarão sobre si a sua iniquidade.
11 Za su iya yin hidima a wurina mai tsarki, suna lura da ƙofofin haikali suna kuma hidima a cikinsu; za su iya yankan hadayun ƙonawa da sadaka don mutane su kuma tsaya a gaban mutane su yi musu hidima.
11 Contudo, eles servirão no meu santuário como guardas nas portas do templo e ministros dele; eles imolarão o holocausto e o sacrifício para o povo e estarão perante este para lhe servir.
12 Amma domin sun yi musu hidima a gaban gumakansu suka sa gidan Isra’ila ya yi zunubi, saboda haka na ɗaga hannu na rantse cewa dole su ɗauki alhakin zunubinsu, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
12 Porque lhe ministraram diante dos seus ídolos e serviram à casa de Israel de tropeço de maldade; por isso, levantando a mão, jurei a respeito deles, diz o Senhor Deus, que eles levarão sobre si a sua iniquidade.
13 Ba za su yi kusa don su yi hidima kamar firistoci ko su zo kusa da abubuwana masu tsarki ko hadayuna mafi tsarki ba; dole su sha kunya saboda ayyukansu na banƙyama.
13 Não se chegarão a mim, para me servirem no sacerdócio, nem se chegarão a nenhuma de todas as minhas coisas sagradas, que são santíssimas, mas levarão sobre si a sua vergonha e as suas abominações que cometeram.
14 Duk da haka zan sa su su lura da ayyukan haikali da kuma dukan ayyukan da za a yi a cikinsa.
14 Contudo, eu os encarregarei da guarda do templo, e de todo o serviço, e de tudo o que se fizer nele.
15 “ ‘Amma firistoci, waɗanda suke Lawiyawa kuma zuriyar Zadok waɗanda suka yi aminci ta wurin yin ayyukansu a wurina mai tsarki sa’ad da Isra’ilawa suka kauce daga gare ni, su ne za su zo kusa don hidima a gabana; za su tsaya a gabana don miƙa hadayun kitse da jini, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
15 Mas os sacerdotes levitas, os filhos de Zadoque, que cumpriram as prescrições do meu santuário, quando os filhos de Israel se extraviaram de mim, eles se chegarão a mim, para me servirem, e estarão diante de mim, para me oferecerem a gordura e o sangue, diz o Senhor Deus.
16 Su ne kaɗai za su shiga wurina mai tsarki; su ne kaɗai za su zo kusa da teburina don yin hidima a gabana su kuma yi hidimata.
16 Eles entrarão no meu santuário, e se chegarão à minha mesa, para me servirem, e cumprirão as minhas prescrições.
17 “ ‘Sa’ad da suka shiga ƙofofin fili na can ciki, dole su sa tufafin lilin; kada su sa wani rigar da aka yi da ulu yayinda suke hidima a ƙofofin fili na can ciki da cikin haikali.
17 E será que, quando entrarem pelas portas do átrio interior, usarão vestes de linho; não se porá lã sobre eles, quando servirem nas portas do átrio interior, dentro do templo.
18 Za su naɗa rawunan lilin a kawunansu, su kuma sa wandunan lilin. Kada su sa wani abin da zai sa su yi zuffa.
18 Tiaras de linho lhes estarão sobre a cabeça, e calções de linho sobre as coxas; não se cingirão a ponto de lhes vir suor.
19 Sa’ad da suka fita daga haikali zuwa fili na waje inda mutane suke, sai su tuɓe rigunan da suka yi hidima da su su bar su a tsarkakan ɗakuna, su sa waɗansu riguna, don kada su tsarkake mutane ta wurin rigunansu.
19 Saindo eles ao átrio exterior, ao povo, despirão as vestes com que ministraram, pô-las-ão nas santas câmaras e usarão outras vestes, para que, com as suas vestes, não santifiquem o povo.
20 “ ‘Ba za su aske kawunansu ko su bar gashin kansu ya yi tsayi ba, amma sai su sausaye gashin kansu.
20 Não raparão a cabeça, nem deixarão crescer o cabelo; antes, como convém, tosquiarão a cabeça.
21 Kada firist ya sha ruwan inabi sa’ad da zai shiga fili na can ciki.
21 Nenhum sacerdote beberá vinho quando entrar no átrio interior.
22 Kada su auri gwauruwa ko macen da aka sāke; za su auri budurwai ne kaɗai na Isra’ilawa ko gwaurayen firistoci.
22 Não se casarão nem com viúva nem com repudiada, mas tomarão virgens da linhagem da casa de Israel ou viúva que o for de sacerdote.
23 Za su koyar da mutanena bambanci tsakanin tsarki da rashin tsarki su kuma nuna musu yadda za su bambanta marar tsarki da mai tsarki.
23 A meu povo ensinarão a distinguir entre o santo e o profano e o farão discernir entre o imundo e o limpo.
24 “ ‘A duk wani rashin jituwa, firistoci za su zama alƙalai su kuma yanke magana bisa ga farillaina. Za su kiyaye dokokina da ƙa’idodina a dukan ƙayyadaddun bukukkuwana, su kuma kiyaye Asabbataina da tsarki.
24 Quando houver contenda, eles assistirão a ela para a julgarem; pelo meu direito julgarão; as minhas leis e os meus estatutos em todas as festas fixas guardarão e santificarão os meus sábados.
25 “ ‘Firist ba zai ƙazantar da kansa ta wurin zuwa kusa da gawa ba; amma, in gawar mahaifinsa ko mahaifiyarsa, ko ɗansa ko ’yarsa, ko ɗan’uwansa ko ’yar’uwarsa ce, to, ba zai ƙazantar da kansa ba.
25 Não se aproximarão de nenhuma pessoa morta, porque se contaminariam; somente por pai, ou mãe, ou filho, ou filha, ou irmão, ou por irmã que não tiver marido, se poderão contaminar.
26 Bayan ya tsarkaka, dole yă jira har kwana bakwai.
26 Depois de ser ele purificado, contar-se-lhe-ão sete dias.
27 A ranar da ya shiga fili na can ciki na wuri mai tsarki don hidima a wuri mai tsarki, zai miƙa hadaya don zunubi saboda kansa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
27 No dia em que ele entrar no lugar santo, no átrio interior, para ministrar no lugar santo, apresentará a sua oferta pelo pecado, diz o Senhor Deus.
28 “ ‘Ni ne kaɗai zan zama abin gādon da firistoci za su kasance da shi. Kada ka ba su wani mallaka a Isra’ila; zan zama mallakarsu.
28 Os sacerdotes terão uma herança; eu sou a sua herança. Não lhes dareis possessão em Israel; eu sou a sua possessão.
29 Za su ci hadaya ta gari, hadaya don zunubi da hadaya don laifi; da kuma kowane keɓaɓɓen abu a Isra’ila da za a ba wa Ubangiji zai zama nasu.
29 A oferta de manjares, e a oferta pelo pecado, e a pela culpa eles comerão; e toda coisa consagrada em Israel será deles.
30 Mafi kyau na nunan farinku da kuma dukan kyautanku na musamman za su zama na firistoci. Za ku ba su rabo na fari na ɓarzajjen hatsinku saboda albarka ta kasance a gidanku.
30 O melhor de todos os primeiros frutos de toda espécie e toda oferta serão dos sacerdotes; também as primeiras das vossas massas dareis ao sacerdote, para que faça repousar a bênção sobre a vossa casa.
31 Firistoci ba za su ci mushen tsuntsu ko na dabba ba, ba kuwa za su ci waɗanda namun jeji suka kashe ba.
31 Não comerão os sacerdotes coisa alguma que de si mesma haja morrido ou tenha sido dilacerada de aves e de animais.
Atalhos do teclado
- Capítulo anterior←
- Próximo capítulo→
- Versículo anteriork
- Próximo versículoj
- Limpar seleçãoEsc
- Esta ajuda?
Estude este capítulo no WhatsApp
Peça à IA da Bíblia Fala para explicar Ezequiel 44, comparar traduções ou montar um estudo — tudo direto pelo WhatsApp.