Êxodo 2
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (HAUSA) vs ARA
1 Ana nan, sai wani Balawe ya auri wata Balawiya,
1 Foi-se um homem da casa de Levi e casou com uma descendente de Levi.
2 ta kuwa yi ciki, ta haifi ɗa. Sa’ad da ta ga jaririn kyakkyawa ne, sai ta ɓoye shi har watanni uku.
2 E a mulher concebeu e deu à luz um filho; e, vendo que era formoso, escondeu-o por três meses.
3 Amma da ba tă iya ɓoye shi kuma ba, sai ta yi kwandon kyauro ta shafa masa kwalta. Bayan haka sai ta sa jaririn a cikin kwandon, ta je ta ajiye kwandon tare da jaririn a cikin kyauro, a bakin kogin.
3 Não podendo, porém, escondê-lo por mais tempo, tomou um cesto de junco, calafetou-o com betume e piche e, pondo nele o menino, largou-o no carriçal à beira do rio.
4 ’Yar’uwarsa ta tsaya da ɗan rata tana lura da abin da zai faru da shi.
4 A irmã do menino ficou de longe, para observar o que lhe haveria de suceder.
5 Sai ’yar Fir’auna ta gangara zuwa kogi domin tă yi wanka, bayinta kuwa suna tafiya a bakin kogi. Sai ta ga kwandon a ciyawa, ta aiki ɗaya daga cikin masu hidimarta tă ɗauko mata.
5 Desceu a filha de Faraó para se banhar no rio, e as suas donzelas passeavam pela beira do rio; vendo ela o cesto no carriçal, enviou a sua criada e o tomou.
6 Da ta buɗe kwandon, sai ta ga yaro yana kuka, ta kuwa ji tausayinsa. Ta ce, “Wannan ɗaya daga cikin jariran Ibraniyawa ne.”
6 Abrindo-o, viu a criança; e eis que o menino chorava. Teve compaixão dele e disse: Este é menino dos hebreus.
7 Sai ’yar’uwarsa ta tambayi ’yar Fir’auna, ta ce, “In tafi in samo ɗaya daga cikin matan Ibraniyawa tă yi miki renon yaron?”
7 Então, disse sua irmã à filha de Faraó: Queres que eu vá chamar uma das hebreias que sirva de ama e te crie a criança?
8 Sai ta amsa ta ce, “I, tafi.” Sai yarinyar ta tafi ta kawo mahaifiyar yaron.
8 Respondeu-lhe a filha de Faraó: Vai. Saiu, pois, a moça e chamou a mãe do menino.
9 Diyar Fir’auna ta ce mata, “Ɗauki jaririn, ki yi mini renonsa, zan kuwa biya ki.” Saboda haka ta ɗauki yaron, ta yi renonsa.
9 Então, lhe disse a filha de Faraó: Leva este menino e cria-mo; pagar-te-ei o teu salário. A mulher tomou o menino e o criou.
10 Sa’ad da ya yi girma, sai ta kawo shi wajen ’yar Fir’auna, ya kuwa zama ɗanta, ta kuma ba shi suna Musa, tana cewa, “Na tsamo shi daga ruwa.”
10 Sendo o menino já grande, ela o trouxe à filha de Faraó, da qual passou ele a ser filho. Esta lhe chamou Moisés e disse: Porque das águas o tirei.
11 Wata rana, bayan Musa ya yi girma, sai ya haura, ya tafi inda mutanensa suke, ya kuma ga yadda suke shan wahala da aiki. Ya ga wani mutumin Masar yana dūkan mutumin Ibraniyawa, ɗaya daga cikin mutanensa.
11 Naqueles dias, sendo Moisés já homem, saiu a seus irmãos e viu os seus labores penosos; e viu que certo egípcio espancava um hebreu, um do seu povo.
12 Da ya leƙa nan da can bai kuwa ga kowa ba, sai ya kashe mutumin Masar, ya ɓoye shi a yashi.
12 Olhou de um e de outro lado, e, vendo que não havia ali ninguém, matou o egípcio, e o escondeu na areia.
13 Kashegari ya fita, sai ya ga Ibraniyawa biyu suna faɗa. Ya tambayi mai laifin ya ce, “Don me kake bugun ɗan’uwanka, mutumin Ibraniyawa?”
13 Saiu no dia seguinte, e eis que dois hebreus estavam brigando; e disse ao culpado: Por que espancas o teu próximo?
14 Mutumin ya ce masa, “Wa ya mai da kai mai mulki da mai hukunci a kanmu? Kana so ne ka kashe ni kamar yadda ka kashe mutumin Masar nan?” Sai Musa ya tsorata, ya yi tunani ya ce, “To, fa, abin nan da na yi, ya zama sananne.”
14 O qual respondeu: Quem te pôs por príncipe e juiz sobre nós? Pensas matar-me, como mataste o egípcio? Temeu, pois, Moisés e disse: Com certeza o descobriram.
15 Da Fir’auna ya ji wannan, sai ya yi ƙoƙari yă kashe Musa, amma Musa ya gudu daga wajen Fir’auna, ya tafi ƙasar Midiyan inda ya zauna kusa da wata rijiya.
15 Informado desse caso, procurou Faraó matar a Moisés; porém Moisés fugiu da presença de Faraó e se deteve na terra de Midiã; e assentou-se junto a um poço.
16 To, fa, akwai wani firist na Midiyan, yana da ’ya’ya mata bakwai, suka zo su shayar da dabbobin mahaifinsu.
16 O sacerdote de Midiã tinha sete filhas, as quais vieram a tirar água e encheram os bebedouros para dar de beber ao rebanho de seu pai.
17 Sai waɗansu makiyaya suka zo suka kore su, amma Musa ya tashi ya taimake su ya shayar da dabbobinsu.
17 Então, vieram os pastores e as enxotaram dali; Moisés, porém, se levantou, e as defendeu, e deu de beber ao rebanho.
18 Da ’yan matan suka komo wurin Reyuwel mahaifinsu, sai ya tambaye su ya ce, “Yaya kuka dawo da wuri yau?”
18 Tendo elas voltado a Reuel, seu pai, este lhes perguntou: Por que viestes, hoje, mais cedo?
19 Suka amsa suka ce, “Wani mutumin Masar ne ya taimake mu daga hannun waɗansu makiyaya. Har ma ya ɗebo ruwa ya shayar da dabbobin.”
19 Responderam elas: Um egípcio nos livrou das mãos dos pastores, e ainda nos tirou água, e deu de beber ao rebanho.
20 Ya tambayi ’yan matansa, “To ina yake? Don me kuka bar shi a can? A gayyace shi, yă zo, yă ci wani abu.”
20 E onde está ele?, disse às filhas; por que deixastes lá o homem? Chamai-o para que coma pão.
21 Musa ya yarda yă zauna da mutumin wanda ya ba da ’yarsa Ziffora aure da Musa.
21 Moisés consentiu em morar com aquele homem; e ele deu a Moisés sua filha Zípora,
22 Ziffora ta haifi wa Musa ɗa, ya kuma raɗa masa suna Gershom cewa, “Na zama baƙo a baƙuwar ƙasa.”
22 a qual deu à luz um filho, a quem ele chamou Gérson, porque disse: Sou peregrino em terra estranha.
23 Ana nan dai, a kwana a tashi, sai sarkin Masar ya mutu. Isra’ilawa suka yi kuka mai zafi saboda bautarsu mai wuya, sai kukar neman taimakonsu saboda bauta, ya kai wurin Allah.
23 Decorridos muitos dias, morreu o rei do Egito; os filhos de Israel gemiam sob a servidão e por causa dela clamaram, e o seu clamor subiu a Deus.
24 Allah kuwa ya ji kukansu sai ya tuna da alkawarinsa da Ibrahim da Ishaku da Yaƙub.
24 Ouvindo Deus o seu gemido, lembrou-se da sua aliança com Abraão, com Isaque e com Jacó.
25 Sai Allah ya dubi Isra’ilawa, ya kuma damu da su.
25 E viu Deus os filhos de Israel e atentou para a sua condição.
Atalhos do teclado
- Capítulo anterior←
- Próximo capítulo→
- Versículo anteriork
- Próximo versículoj
- Limpar seleçãoEsc
- Esta ajuda?
Estude este capítulo no WhatsApp
Peça à IA da Bíblia Fala para explicar Êxodo 2, comparar traduções ou montar um estudo — tudo direto pelo WhatsApp.