Atos 21

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (HAUSA) vs VC

Sair da comparação
VC Versão Católica
1 Bayan muka rabu da su da ƙyar, sai muka shiga jirgin ruwa, muka miƙe zuwa Kos. Kashegari muka tafi Rods daga can kuma muka je Fatara.
1 Depois de nos separarmos dele, embarcamos e fomos em direção a Cós, e no dia seguinte a Rodes e dali a Pátara.
2 Sai muka sami wani jirgin ruwa da zai ƙetare zuwa Funisiya, sai muka shiga muka kama tafiya.
2 Encontramos aí um navio que ia partir para a Fenícia. Entramos e seguimos viagem.
3 Bayan muka hangi Saifurus muka wuce shi ta kudu, sai muka ci gaba zuwa Suriya. Muka sauka a Taya, inda jirgin ruwanmu zai sauke kayansa.
3 Quando estávamos à vista de Chipre, deixando-a à esquerda, continuamos rumo à Síria e aportamos em Tiro, onde o navio devia ser descarregado.
4 Da muka sami almajirai a can, sai muka zauna da su kwana bakwai. Ta wurin Ruhu, suka yi ƙoƙari su hana Bulus wucewa zuwa Urushalima.
4 Como achássemos uns discípulos, detivemo-nos com eles por sete dias. Eles, sob a inspiração do Espírito, aconselhavam Paulo que não subisse a Jerusalém.
5 Amma da lokacin tashinmu ya yi, sai muka tashi muka ci gaba da tafiyarmu. Dukan almajirai da matansu da ’ya’yansu suka raka mu har bayan birni, a can kuwa a bakin teku muka durƙusa muka yi addu’a.
5 Mas, passados que foram esses dias, partimos e seguimos a nossa viagem. Todos eles com suas mulheres e filhos acompanharam-nos até fora da cidade. Ajoelhados na praia, fizemos a nossa oração.
6 Bayan mun yi bankwana da juna, sai muka shiga jirgin ruwa, su kuwa suka koma gida.
6 Despedimo-nos então e embarcamos, enquanto eles voltaram para suas casas.
7 Muka ci gaba da tafiyarmu daga Taya muka sauka a Tolemayis, inda muka gai da ’yan’uwa muka yi kwana ɗaya tare da su.
7 Navegando, fomos de Tiro a Ptolemaida, onde saudamos os irmãos, passando um dia com eles.
8 Da muka tashi kashegari, sai muka isa Kaisariya muka kuma sauka a gidan Filibus mai bishara, ɗaya daga cikin Bakwai ɗin nan.
8 Partindo no dia seguinte, chegamos a Cesaréia e, entrando na casa de Filipe, o Evangelista, que era um dos sete {diáconos}, ficamos com ele.
9 Yana da ’ya’ya huɗu ’yan mata da ba su yi aure ba, waɗanda suka yi annabci.
9 Tinha quatro filhas virgens que profetizavam.
10 Bayan muka yi ’yan kwanaki da dama a can, sai wani annabin da ake kira Agabus ya gangaro daga Yahudiya.
10 Já estávamos aí fazia alguns dias, quando chegou da Judéia um profeta, chamado Ágabo.
11 Da ya zo wurinmu, sai ya ɗauki ɗamarar Bulus, ya ɗaura hannuwansa da ƙafafunsa da ita sa’an nan ya ce, “Ruhu Mai Tsarki ya ce, ‘Haka Yahudawan Urushalima za su daure mai wannan ɗamara su kuma ba da shi ga Al’ummai.’ ”
11 Veio ter conosco, tomou o cinto de Paulo e, amarrando-se com ele pés e mãos, disse: Isto diz o Espírito Santo: assim os judeus em Jerusalém ligarão o homem a quem pertence este cinto e o entregarão às mãos dos pagãos.
12 Sa’ad da muka ji haka, sai mu da mutanen da suke can muka roƙi Bulus kada yă je Urushalima.
12 A estas palavras, nós e os fiéis que eram daquele lugar, rogamos-lhe que não subisse a Jerusalém.
13 Sai Bulus ya amsa ya ce, “Don me kuke kuka kuna kuma ɓata mini zuciya? A shirye nake ba ma a daure ni kawai ba, amma har ma in mutu a Urushalima saboda sunan Ubangiji Yesu.”
13 Paulo, porém, respondeu: Por que chorais e me magoais o coração? Pois eu estou pronto não só a ser preso, mas também a morrer em Jerusalém pelo nome do Senhor Jesus.
14 Da dai ya ƙi rarrasuwa, muka yi shiru, muka ce, “Bari Ubangiji yă yi nufinsa.”
14 Como não pudéssemos persuadi-lo, desistimos, dizendo: Faça-se a vontade do Senhor!
15 Bayan haka, sai muka shirya muka kuma haura zuwa Urushalima.
15 Depois desses dias, terminados os preparativos, subimos a Jerusalém.
16 Waɗansu almajirai daga Kaisariya suka raka mu suka kawo mu gidan Minason, inda za mu sauka. Shi mutumin Saifurus ne kuma ɗaya daga cikin almajirai na farko.
16 Foram também conosco alguns dos discípulos de Cesaréia, que nos levaram à casa de Menason de Chipre, um antigo discípulo em cuja casa nos devíamos hospedar.
17 Sa’ad da muka zo Urushalima, ’yan’uwa suka karɓe mu da murna.
17 À nossa chegada em Jerusalém, os irmãos nos receberam com alegria.
18 Kashegari Bulus da sauranmu muka tafi domin mu ga Yaƙub, dukan dattawan kuwa suna nan.
18 No dia seguinte, Paulo dirigiu-se conosco à casa de Tiago, onde todos os anciãos se reuniram.
19 Bulus ya gaishe su ya kuma ba su rahoto dalla-dalla a kan abin da Allah ya yi a cikin Al’ummai ta wurin aikinsa.
19 Tendo-os saudado, contou-lhes uma por uma todas as coisas que Deus fizera entre os pagãos por seu ministério.
20 Da suka ji haka, sai suka yabi Allah. Sa’an nan suka ce wa Bulus, “Ka gani ɗan’uwa, yawan dubban Yahudawan da suka gaskata, kuma dukansu masu himma ne a wajen bin doka.
20 Ouvindo isso, glorificaram a Deus e disseram a Paulo: Bem vês, irmão, quantos milhares de judeus abraçaram a fé sem abandonar seu zelo pela lei.
21 An sanar da su cewa kana koya wa dukan Yahudawan da suke zama a cikin Al’ummai cewa su juye daga Musa, kana kuma faɗa musu kada su yi wa ’ya’yansu kaciya ko su yi rayuwa bisa ga al’adunmu.
21 Eles têm ouvido dizer de ti que ensinas os judeus, que vivem entre os gentios, a deixarem Moisés, dizendo que não devem circuncidar os seus filhos nem observar os costumes {mosaicos}.
22 To, me za mu yi ke nan? Lalle za su ji cewa ka iso,
22 Que se há de fazer? Sem dúvida, saberão de tua chegada.
23 saboda haka, ka yi abin da muka faɗa maka. Akwai mutum huɗu tare da mu da suka yi alkawari.
23 Faze, pois, o que te vamos dizer. Temos aqui quatro homens que têm um voto.
24 Ka ɗauki waɗannan mutane, ka tafi da su ku tsarkaka gaba ɗaya, ka kuma biya musu kome don su samu su yi aski. Ta haka kowa zai sani babu gaskiya a waɗannan rahotanni game da kai, za a kuma ga cewa kai kanka kana kiyaye dokar.
24 Toma-os contigo, faze com eles os ritos da purificação e paga por eles {a oferta obrigatória} para que rapem a cabeça. Então todos saberão que é falso quanto de ti ouviram, mas que também tu guardas a lei.
25 Game da Al’ummai masu bi kuwa, mun yi musu wasiƙa a kan shawararmu cewa su guji abincin da aka miƙa wa gumaka, da jini, da naman dabbar da aka maƙure da kuma fasikanci.”
25 Mas a respeito dos que creram dentre os gentios, já escrevemos, ordenando que se abstenham do que for sacrificado aos ídolos, do sangue, da carne sufocada e da fornicação.
26 Kashegari, sai Bulus ya ɗauki mutanen ya kuma tsarkake kansa tare da su. Sa’an nan ya tafi haikali domin yă sanar da ranar cikar tsarkakewarsu da kuma ranar da za a ba da sadaka domin kowannensu.
26 Então Paulo acompanhou aqueles homens no dia seguinte e, purificando-se com eles, entrou no templo e fez aí uma declaração do termo do voto, findo o qual se devia oferecer um sacrifício a favor de cada um deles.
27 Da kwana bakwai ɗin suka yi kusan cika, waɗansu Yahudawa daga lardin Asiya suka ga Bulus a haikali. Sai suka zuga taron duka, suka kama shi,
27 Ao fim dos sete dias, os judeus, vindos da Ásia, viram Paulo no templo e amotinaram todo o povo. Lançando-lhe as mãos,
28 suna ihu suna cewa “Mutanen Isra’ila ku taimake mu! Ga mutumin da yake koya wa dukan mutane ko’ina cewa su ƙi mutanenmu da dokarmu da kuma wannan wuri. Ban da haka ma, ya kawo Hellenawa a cikin filin haikali ya ƙazantar da wurin nan mai tsarki.”
28 gritavam: Ó judeus, valei-nos! Este é o homem que por toda parte prega a todos contra o povo, a lei e o templo. Além disso, introduziu até gregos no templo e profanou o lugar santo.
29 (Dā ma can sun ga Turofimus mutumin Afisa a birni tare da Bulus suka yi tsammani Bulus ya kawo shi filin haikali.)
29 É que tinham visto Trófimo, de Éfeso, com ele na cidade, e pensavam que Paulo o tivesse introduzido no templo.
30 Duk birnin ya ruɗe, mutane suka zaburo da gudu daga kowane gefe. Suka kama Bulus, suka ja shi daga haikali, nan da nan aka rurrufe ƙofofi.
30 Alvoroçou-se toda a cidade com grande ajuntamento de povo. Agarraram Paulo e arrastaram-no para fora do templo, cujas portas se fecharam imediatamente.
31 Yayinda suke ƙoƙari su kashe shi, sai labari ya kai ga shugaban ƙungiyar sojan Roma cewa birnin Urushalima duk ta hargitse.
31 Como quisessem matá-lo, o tribuno da coorte foi avisado de que toda Jerusalém estava amotinada.
32 Nan da nan ya ɗibi waɗansu hafsoshi da sojoji suka gangara a guje wurin taron. Da masu hargitsin suka ga shugaban ƙungiyar sojan da sojojinsa, sai suka daina dūkan Bulus.
32 Ele tomou logo soldados e oficiais e correu aos manifestantes. Estes, ao avistarem o tribuno e os saldados, cessaram de espancar Paulo.
33 Shugaban ƙungiyar sojan ya zo ya kama shi ya ba da umarni a daure shi da sarƙoƙi biyu. Sa’an nan ya yi tambaya ko shi wane ne, da kuma abin da ya yi.
33 Aproximando-se então o tribuno, prendeu-o e mandou acorrentá-lo com duas cadeias. Perguntou então quem era e o que havia feito.
34 Waɗansu daga cikin taron suka ɗau kururuwa suna ce abu kaza, waɗansu kuma suna ce abu kaza, da yake shugaban ƙungiyar sojan ya kāsa samun ainihin tushen maganar saboda yawan hayaniyar, sai ya yi umarni a kai Bulus barikin soja.
34 Na multidão todos gritavam de tal modo que, não podendo apurar a verdade por causa do tumulto, mandou que fosse recolhido à cidadela.
35 Sa’ad da Bulus ya kai bakin matakala, sai da sojoji suka ɗaga shi sama saboda tsananin haukan taron.
35 Quando Paulo chegou às escadas, foi carregado pelos soldados, por causa do furor da multidão.
36 Taron da suka bi suka dinga kururuwa, suna cewa, “A yi da shi!”
36 O povo o seguia em massa dizendo aos gritos: À morte
37 Da sojoji suka kai gab da shigar da Bulus cikin bariki, sai ya ce wa shugaban ƙungiyar sojan, “Ko ka yarda in yi magana da kai?”
37 Quando estava para ser introduzido na fortaleza, Paulo perguntou ao tribuno: É-me permitido dizer duas palavras? Este respondeu: Sabes o grego!
38 Ba kai ba ne mutumin Masar nan da ya haddasa tawaye har ya yi jagorar ’yan ta’ada dubu huɗu zuwa hamada a shekarun baya?”
38 Não és tu, portanto, aquele egípcio que há tempos levantou um tumulto e conduziu ao deserto quatro mil extremistas?
39 Bulus ya amsa ya ce, “Ni mutumin Yahuda ne, daga Tarshish a Silisiya shahararren birnin nan. In ka yarda bari in yi wa mutane magana.”
39 Paulo replicou: Eu sou judeu, natural de Tarso, na Cilícia, cidadão dessa ilustre cidade. Mas rogo-te que me permitas falar ao povo.
40 Da ya sami izini daga shugaban ƙungiyar sojan, sai Bulus ya tsaya a matakala, ya ɗaga wa taron hannu. Da dukan suka yi shiru, sai ya ce musu da Arameyanci,
40 O tribuno lho permitiu. Paulo, em pé nos degraus, acenou ao povo com a mão e se fez um grande silêncio. Falou em língua hebraica do seguinte modo:

Ler em outra tradução

Comparar com outra

Estude este capítulo no WhatsApp

Peça à IA da Bíblia Fala para explicar Atos 21, comparar traduções ou montar um estudo — tudo direto pelo WhatsApp.