2 Tessalonicenses 3

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (HAUSA) vs ARIB

Sair da comparação
ARIB Almeida Revisada Imprensa Bíblica
1 A ƙarshe, ’yan’uwa, ku yi mana addu’a domin saƙon Ubangiji yă yi saurin bazuwa a kuma girmama shi, kamar yadda yake a wurinku.
1 Finalmente, irmãos, orai por nós, para que a palavra do Senhor se propague e seja glorificada. como também o é entre vós,
2 Ku kuma yi addu’a yadda za a cece mu daga mugayen mutane masu mugunta, gama ba kowa ba ne yake da bangaskiya.
2 e para que sejamos livres de homens perversos e maus; porque a fé não é de todos.
3 Ubangiji mai aminci ne, zai ƙarfafa ku, yă kuma tsare ku daga mugun nan.
3 Mas fiel é o Senhor, o qual vos confirmará e guardará do maligno.
4 Muna da tabbaci cikin Ubangiji cewa kuna bin umarnai da muka yi muku, za ku kuma ci gaba da yin abubuwan da muka umarta.
4 E, quanto a vós, confiamos no Senhor que não só fazeis, mas fareis o que vos mandamos.
5 Bari Ubangiji yă bi da zukatanku ga ƙaunan nan ta Allah da kuma jimirin nan na Kiristi.
5 Ora, o Senhor encaminhe os vossos corações no amor de Deus e na constância de Cristo.
6 A cikin sunan Ubangiji Yesu Kiristi, muna muku umarni, ’yan’uwa, da ku kiyaye kanku daga kowane ɗan’uwa mai zaman banza da ba ya rayuwa bisa ga koyarwar da kuka karɓa daga wurinmu.
6 mandamo-vos, irmãos, em nome do Senhor Jesus Cristo, que vos aparteis de todo irmão que anda desordenadamente, e não segundo a tradição que de nós recebestes.
7 Gama ku kanku kun san yadda ya kamata ku bi gurbinmu. Ba mu yi zaman banza sa’ad da muke tare da ku ba,
7 Porque vós mesmos sabeis como deveis imitar-nos, pois que não nos portamos desordenadamente entre vós,
8 ba mu kuwa ci abincin kowa ba tare da ba mu biya ba. A maimakon haka, mun yi aiki dare da rana, muna fama muna wahala kuma don kada mu nawaita wa waninku.
8 nem comemos de graça o pão de ninguém, antes com labor e fadiga trabalhávamos noite e dia para não sermos pesados a nenhum de vós.
9 Mun yi wannan, ba don ba mu da ’yancin karɓar irin taimakon nan ba ne, sai dai domin mu zama gurbin da za ku bi.
9 Não porque não tivéssemos direito, mas para vos dar nós mesmos exemplo, para nos imitardes.
10 Ko ma a sa’ad da muke tare da ku, mun ba ku wannan umarni cewa, “In mutum ya ƙi yin aiki, kada a ba shi abinci.”
10 Porque, quando ainda estávamos convosco, isto vos mandamos: se alguém não quer trabalhar, também não coma.
11 Mun ji cewa waɗansunku suna zaman banza. Ba sa aikin kome; sai shisshigi kurum.
11 Porquanto ouvimos que alguns entre vós andam desordenadamente, não trabalhando, antes intrometendo-se na vida alheia;
12 Irin waɗannan mutane muna ba da umarni muna kuma gargaɗe su cikin Ubangiji Yesu Kiristi su natsu su kuma nemi abincin da suke ci.
12 a esses tais, porém, ordenamos e exortamos por nosso Senhor Jesus Cristo que, trabalhando sossegadamente, comam o seu próprio pão.
13 Game da ku kuma ’yan’uwa, kada ku gaji da yin abin da yake daidai.
13 Vós, porém, irmãos, não vos canseis de fazer o bem.
14 In wani bai yi biyayya da umarninmu a wannan wasiƙa ba, sai fa ku lura da shi. Kada ku haɗa kai da shi, don yă ji kunya.
14 Mas, se alguém não obedecer à nossa palavra por esta carta, notai-o e não tenhais relações com ele, para que se envergonhe;
15 Duk da haka kada ku mai da shi abokin gāba, sai dai ku gargaɗe shi a matsayin ɗan’uwa.
15 todavia não o considereis como inimigo, mas admoestai-o como irmão.
16 Yanzu, bari Ubangiji mai salama kansa yă ba ku salama a kowane lokaci da kuma a ta kowace hanya. Ubangiji yă kasance tare da ku duka.
16 Ora, o próprio Senhor da paz vos dê paz sempre e de toda maneira. O Senhor seja com todos vós.
17 Ni, Bulus, nake rubuta wannan gaisuwa da hannuna, wannan ce shaida a kowace wasiƙata, haka nake rubutu.
17 Esta saudação é de próprio punho, de Paulo, o que é o sinal em cada epístola; assim escrevo.
18 Alherin Ubangijinmu Yesu Kiristi yă kasance tare da ku duka.
18 A graça de nosso Senhor Jesus Cristo seja com todos vós.

Ler em outra tradução

Comparar com outra

Estude este capítulo no WhatsApp

Peça à IA da Bíblia Fala para explicar 2 Tessalonicenses 3, comparar traduções ou montar um estudo — tudo direto pelo WhatsApp.