1 Tessalonicenses 5
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (HAUSA) vs VC
1 To, ’yan’uwa, game da lokuta da ranaku, ba ma bukata mu rubuta muku,
1 A respeito da época e do momento, não há necessidade, irmãos, de que vos escrevamos.
2 gama kun sani sarai cewa ranar Ubangiji za tă zo kamar ɓarawo da dare.
2 Pois vós mesmos sabeis muito bem que o dia do Senhor virá como um ladrão de noite.
3 Yayinda mutane suke cewa, “Akwai salama da zaman lafiya,” hallaka za tă auko musu farat ɗaya, kamar yadda naƙuda take kama mace mai ciki, ba za su kuwa tsira ba.
3 Quando os homens disserem: Paz e segurança!, então repentinamente lhes sobrevirá a destruição, como as dores à mulher grávida. E não escaparão.
4 Amma ku, ’yan’uwa, ba kwa cikin duhu da wannan rana za tă zo muku ba zato kamar ɓarawo.
4 Mas vós, irmãos, não estais em trevas, de modo que esse dia vos surpreenda como um ladrão.
5 Dukanku ’ya’yan haske ne da kuma ’ya’yan rana. Mu ba mutanen dare ko na duhu ba ne.
5 Porque todos vós sois filhos da luz e filhos do dia. Não somos da noite nem das trevas.
6 Saboda haka fa, kada mu zama kamar saura, waɗanda suke barci, sai dai mu zama masu tsaro da masu kamunkai.
6 Não durmamos, pois, como os demais. Mas vigiemos e sejamos sóbrios.
7 Gama masu barci, da dad dare suke barci, masu sha su bugu kuwa, da dad dare suke buguwa.
7 Porque os que dormem, dormem de noite; e os que se embriagam, embriagam-se de noite.
8 Amma da yake mu na rana ne, bari mu zama masu kamunkai, sanye da bangaskiya da ƙauna kamar sulke, begen cetonmu kuma kamar hular kwano.
8 Nós, ao contrário, que somos do dia, sejamos sóbrios. Tomemos por couraça a fé e a caridade, e por capacete a esperança da salvação.
9 Gama Allah bai naɗa mu don mu sha fushi ba, sai dai mu sami ceto ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi.
9 Porquanto não nos destinou Deus para a ira, mas para alcançar a salvação por nosso Senhor Jesus Cristo.
10 Ya mutu saboda mu domin, ko muna a faɗake ko muna barci, mu kasance tare da shi.
10 Ele morreu por nós, a fim de que nós, quer em estado de vigília, quer de sono, vivamos em união com ele.
11 Saboda haka ku ƙarfafa juna ku kuma gina juna, kamar dai yadda kuke yi.
11 Assim, pois, consolai-vos mutuamente e edificai-vos uns aos outros, como já o fazeis.
12 To, muna roƙonku, ’yan’uwa, ku girmama waɗanda suke aiki sosai a cikinku, waɗanda suke bisanku cikin Ubangiji da kuma waɗanda suke yin muku gargaɗi.
12 Suplicamo-vos, irmãos, que reconheçais aqueles que arduamente trabalham entre vós para dirigir-vos no Senhor e vos admoestar.
13 Ku riƙe su da mutunci sosai cikin ƙauna saboda aikinsu. Ku yi zaman lafiya da juna.
13 Tende para com eles singular amor, em vista do cargo que exercem. Conservai a paz entre vós.
14 Muna kuma gargaɗe ku, ’yan’uwa, ku gargaɗe waɗanda suke zaman banza, ku ƙarfafa masu raunanar zuciya, ku taimaki marasa ƙarfi, ku yi haƙuri da kowa.
14 Pedimo-vos, porém, irmãos, corrigi os desordeiros, encorajai os tímidos, amparai os fracos e tende paciência para com todos.
15 Ku tabbata cewa kada kowa yă rama mugunta da mugunta, sai dai kullum ku yi ƙoƙarin yin wa juna alheri da kuma dukan mutane.
15 Vede que ninguém pague a outro mal por mal. Antes, procurai sempre praticar o bem entre vós e para com todos.
16 Ku riƙa farin ciki kullum;
16 Vivei sempre contentes.
17 ku ci gaba da yin addu’a;
17 Orai sem cessar.
18 ku yi godiya cikin kowane hali, gama wannan shi ne nufin Allah dominku cikin Kiristi Yesu.
18 Em todas as circunstâncias, dai graças, porque esta é a vosso respeito a vontade de Deus em Jesus Cristo.
19 Kada ku danne aikin Ruhu.
19 Não extingais o Espírito.
20 Kada ku rena annabci,
20 Não desprezeis as profecias.
21 amma ku gwada kome, ku riƙe abin da yake mai kyau,
21 Examinai tudo: abraçai o que é bom.
22 ku ƙi kowace mugunta.
22 Guardai-vos de toda a espécie de mal.
23 Bari Allah da kansa, Allah na salama, yă tsarkake ku sarai. Bari dukan ruhunku, ranku, da kuma jikinku su zama marar aibi a dawowar Ubangijinmu Yesu Kiristi.
23 O Deus da paz vos conceda santidade perfeita. Que todo o vosso ser, espírito, alma e corpo, seja conservado irrepreensível para a vinda de nosso Senhor Jesus Cristo!
24 Wannan wanda ya kira ku mai aminci ne zai kuwa aikata.
24 Fiel é aquele que vos chama, e o cumprirá.
25 ’Yan’uwa, ku yi mana addu’a.
25 Irmãos, orai também por nós.
26 Ku gaggai da dukan ’yan’uwa da sumba mai tsarki.
26 Saudai a todos os irmãos com o ósculo santo.
27 Na gama ku da Ubangiji ku sa a karanta wannan wasiƙa ga dukan ’yan’uwa.
27 Peço-vos encarecidamente, no Senhor, que esta carta seja lida a todos os irmãos.
28 Alherin Ubangijinmu Yesu Kiristi yă kasance tare da ku.
28 A graça de nosso Senhor Jesus Cristo esteja convosco!
Atalhos do teclado
- Capítulo anterior←
- Próximo capítulo→
- Versículo anteriork
- Próximo versículoj
- Limpar seleçãoEsc
- Esta ajuda?
Estude este capítulo no WhatsApp
Peça à IA da Bíblia Fala para explicar 1 Tessalonicenses 5, comparar traduções ou montar um estudo — tudo direto pelo WhatsApp.