1 Samuel 8

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (HAUSA) vs NVT

Sair da comparação
NVT Nova Versão Transformadora
1 Da Sama’ila ya tsufa, sai ya naɗa ’ya’yansa maza su zama alƙalan Isra’ila.
1 Quando Samuel ficou idoso, nomeou seus filhos para serem juízes sobre Israel.
2 Sunan ɗansa na fari Yowel, na biyu kuwa Abiya. Suka yi alƙalanci a Beyersheba.
2 Joel, seu filho mais velho, e Abias, o segundo mais velho, julgavam em Berseba,
3 Amma ’ya’yansa ba su bi hanyar mahaifinsu ba. Suka mai da hankalinsu ga neman kuɗi da cin hanci, suna kuma danne gaskiya.
3 mas não eram como seu pai. Eram gananciosos, aceitavam subornos e pervertiam a justiça.
4 Sai dukan shugabannin Isra’ila suka taru suka zo wurin Sama’ila a Rama.
4 Por fim, as autoridades de Israel se reuniram em Ramá para discutir essa questão com Samuel.
5 Suka ce masa, “Ka tsufa, ’ya’yanka kuma ba sa bin hanyarka, saboda haka sai ka naɗa sarkin da zai bi da mu kamar yadda sauran ƙasashe suke da su.”
5 Eles disseram: “Olhe, o senhor está idoso e seus filhos não seguem seu exemplo. Escolha um rei para nos julgar, como ocorre com todas as outras nações”.
6 Amma Sama’ila bai ji daɗi sa’ad da suka ce, “Ka ba mu sarki da zai bi da mu.” Sai ya yi addu’a ga Ubangiji.
6 Samuel não gostou de que lhe tivessem pedido um rei e buscou a orientação do S enhor .
7 Ubangiji kuwa ya ce masa, “Ka saurari dukan maganganun da mutanen suke gaya maka. Ai, ba kai ba ne suka ƙi, ni ne suka ƙi in zama sarkinsu.
7 O S enhor lhe respondeu: “Faça tudo que eles pedem, pois é a mim que rejeitam, e não a você. Eles me rejeitaram como seu rei.
8 Haka suka yi daga tun daga ranar da na fitar da su daga Masar har zuwa yau, suka ƙi ni, suka bauta wa waɗansu alloli, haka ma suke yi maka.
8 Desde que os tirei do Egito até hoje, eles têm me abandonado e seguido outros deuses. Agora, tratam você da mesma forma.
9 Yanzu ka saurare su amma ka yi musu kashedi sosai, ka sa su san abin da sarkin da zai bi da su zai yi.”
9 Faça o que eles pedem, mas advirta-os solenemente a respeito de como o rei os governará”.
10 Sama’ila kuwa ya ce wa mutanen da suke roƙo yă naɗa musu sarki dukan abin da Ubangiji ya faɗa.
10 Então Samuel transmitiu a advertência do S enhor ao povo que lhe pedia um rei.
11 Ya ce musu, “Ga abin da sarkin da zai yi mulkinku zai yi. Zai kwashe ’ya’yanku yă sa su yi aiki da kekunan yaƙi da dawakansa, waɗansu za su riƙa gudu a gaban keken yaƙinsa.
11 Disse ele: “Este é o modo como o rei governará sobre vocês. Ele convocará seus filhos para servi-lo em seus carros de guerra e como seus cavaleiros e os fará correr à frente dos carros dele.
12 Zai sa waɗansu su zama shugabannin mutum dubu-dubu da kuma na hamsin-hamsin. Waɗansu za su yi masa noma da girbi. Waɗansu za su ƙera masa makaman yaƙi da kayayyaki don keken yaƙinsa.
12 Colocará alguns como generais e capitães de seu exército, obrigará outros a arar seus campos e a fazer as colheitas e forçará outros mais a fabricar armas e equipamentos para os carros de guerra.
13 Zai sa ’ya’yanku mata yin aikin turare da dafe-dafe da kuma toye-toye.
13 Tomará suas filhas e as obrigará a cozinhar, assar pães e fazer perfumes para ele.
14 Zai karɓi gonakinku mafi kyau da gonakin inabinku da gonakin zaitunku yă ba wa ma’aikatansa.
14 Tomará de vocês o melhor de seus campos, vinhedos e olivais e os dará aos servos dele.
15 Zai kuma karɓi zakan hatsinku da na inabinku yă ba shugabannin fadarsa da sauran masu hidimarsa.
15 Tomará um décimo de sua colheita de cereais e uvas para distribuir entre seus oficiais e servos.
16 Zai ƙwace bayinku maza da mata, da shanunku, da jakunanku mafi kyau domin su yi masa aiki.
16 Tomará seus escravos e escravas e o melhor do gado e dos jumentos para uso próprio.
17 Zai karɓi zakan dabbobinku, ku kanku za ku zama bayinsa.
17 Exigirá um décimo de seus rebanhos, e vocês se tornarão escravos dele.
18 Sa’ad da ranar ta zo, za ku yi kuka ku nemi a fishe ku daga sarkin da kuka zaɓa, Ubangiji kuwa ba zai ji ku ba.”
18 Quando esse dia chegar, lamentarão por causa desse rei que agora pedem, mas o S enhor não lhes dará ouvidos”.
19 Amma mutanen suka ƙi jin Sama’ila, sai suka ce, “A’a, mu dai, muna son sarki yă bi da mu.”
19 Mas o povo se recusou a ouvir a advertência de Samuel. “Mesmo assim, queremos um rei”, disseram.
20 Ta haka za mu zama kamar sauran ƙasashe, mu kasance da sarkin da zai bi da mu, yă tafi tare da mu zuwa yaƙe-yaƙe.
20 “Queremos ser como todas as nações ao nosso redor. Nosso rei nos julgará e nos conduzirá nas batalhas.”
21 Da Sama’ila ya ji duk maganganun da mutanen suka faɗa, sai ya mayar wa Ubangiji.
21 Samuel repetiu para o S enhor aquilo que o povo tinha dito,
22 Ubangiji kuwa ya ce, “Ka saurare su, ka naɗa masu sarki.”
22 e o S enhor lhe respondeu: “Faça o que eles pedem e dê-lhes um rei”. Então Samuel ordenou aos israelitas que voltassem cada um para sua cidade.

Ler em outra tradução

Comparar com outra

Estude este capítulo no WhatsApp

Peça à IA da Bíblia Fala para explicar 1 Samuel 8, comparar traduções ou montar um estudo — tudo direto pelo WhatsApp.