1 Samuel 17

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (HAUSA) vs NVT

Sair da comparação
NVT Nova Versão Transformadora
1 To, fa, Filistiyawa suka tattara mayaƙansu suka haɗu a Soko cikin Yahuda domin yaƙi. Suka yi sansani a Efes-Dammim, tsakanin Soko da Azeka.
1 Os filisteus reuniram seu exército para a batalha e acamparam em Efes-Damim, entre Socó, em Judá, e Azeca.
2 Shawulu da Isra’ilawa suka taru suka yi sansani a Kwarin Ela suka ja dāgā don su yi yaƙi da Filistiyawa.
2 Em resposta, Saul reuniu as tropas israelitas perto do vale de Elá.
3 Filistiyawa suka zauna a tudu guda, Isra’ilawa kuma suka zauna a ɗaya tudun. Kwari yana a tsakaninsu.
3 Assim, os filisteus e os israelitas ficaram frente a frente, em colinas opostas, com o vale entre eles.
4 Wani jarumin da ake kira Goliyat wanda ya fito daga Gat, ya fita daga sansanin Filistiyawa. Tsawonsa ya fi ƙafa tara.
4 Então Golias, um guerreiro filisteu de Gate, saiu das fileiras do exército filisteu. Ele tinha 2,90 metros de altura,
5 Ya sa hular kwanon da aka yi da tagulla, da rigar ƙarfe mai sulke, nauyin rigar ya kai shekel dubu biyar.
5 usava um capacete de bronze e vestia uma couraça de escamas de bronze que pesava sessenta quilos.
6 A ƙafafunsa kuwa ya sa ƙarafar tagulla, rataye a bayansa kuma māshi ne na tagulla.
6 Também usava caneleiras de bronze e carregava no ombro um dardo de bronze.
7 Ƙotar kibiyarsa kuwa kamar sandar saƙar igiya take, ƙarfen kibiyar kuma nauyinsa ya kai shekel ɗari shida. Mai riƙe masa garkuwa yana tafe a gabansa.
7 A haste de sua lança era pesada e grossa, como o eixo de um tear, e a ponta de ferro da lança pesava cerca de sete quilos. Seu escudeiro caminhava à frente dele.
8 Goliyat ya tsaya ya tā da murya wa hafsoshin Isra’ila ya ce, “Me ya sa kuka fito kuna layi don yaƙi? Ni ba Bafilistin ba ne? Ku kuma ba bayin Shawulu ba ne? Ku zaɓi waninku yă zo nan.
8 Golias parou e gritou para as tropas israelitas: “Por que saíram todos para lutar? Eu sou filisteu, e vocês são servos de Saul. Escolham um homem para vir aqui e lutar comigo!
9 In zai iya yin faɗa har yă kashe ni, to, za mu zama bayinku. Amma in na fi ƙarfinsa na kashe shi, to, sai ku zama bayinmu, ku kuma yi mana bauta.”
9 Se ele me matar, seremos seus escravos. Mas, se eu o matar, vocês serão nossos escravos!
10 Sai Bafilistin ya ce, “A wannan rana, na kalubalanci sojojin Isra’ila, ku ba ni mutum ɗaya mu yi faɗa.”
10 Desafio hoje os exércitos de Israel. Mandem um homem para lutar comigo!”.
11 Da jin maganganun Bafilistin, sai Shawulu da dukan Isra’ila suka damu suka kuma ji tsoro.
11 Quando Saul e os israelitas ouviram isso, ficaram aterrorizados e muito abalados.
12 To, Dawuda dai ɗan wani mutumin Efratawa ne mai suna Yesse, shi mutumin Betlehem ne a cikin Yahudiya. Yesse yana da yara maza takwas, a zamanin Shawulu kuwa, Yesse ya riga ya tsufa.
12 Davi era filho de Jessé, efrateu de Belém, na terra de Judá. Na época do rei Saul, Jessé já era idoso e tinha oito filhos.
13 Manyan ’ya’yansa maza uku, sun bi Shawulu wajen yaƙi. Ɗansa na fari shi ne Eliyab, na biyu shi ne Abinadab, na uku kuwa shi ne Shamma.
13 Os três filhos mais velhos de Jessé — Eliabe, Abinadabe e Simeia — haviam se alistado no exército de Saul para lutar contra os filisteus.
14 Dawuda shi ne ɗan autansu. Manyan ’yan mazan nan uku suka bi Shawulu.
14 Davi era o mais novo. Seus três irmãos mais velhos seguiam o exército de Saul,
15 Amma Dawuda yakan tafi sansanin Shawulu lokaci-lokaci yă kuma koma Betlehem don yă yi kiwon tumakin mahaifinsa.
15 enquanto Davi ia e voltava para ajudar seu pai a cuidar das ovelhas em Belém.
16 Kwana arba’in cif, Bafilistin nan ya yi ta fitowa kowane safe da kuma kowace yamma.
16 Durante quarenta dias, pela manhã e à tarde, o guerreiro filisteu se apresentava diante do exército israelita e o desafiava.
17 Yesse ya ce wa ɗansa Dawuda, “Ka ɗauki wannan gasasshen hatsi da waɗannan curin burodi goma, ka kai wa ’yan’uwanka a sansani da sauri.
17 Um dia, Jessé disse a Davi: “Leve depressa para seus irmãos que estão no acampamento este cesto com grãos tostados e estes dez pães.
18 Ka haɗa da waɗannan cuku guda goma, ka kai wa komandan rundunarsu. Ka ga lafiyar ’yan’uwanka, ka kawo mini labari daga wurinsu.
18 Leve também estes dez queijos para o capitão deles. Veja como estão seus irmãos e traga notícias deles”.
19 Suna tare da Shawulu da kuma dukan mutanen Isra’ila a Kwarin Ela, suna can suna yaƙi da Filistiyawa.”
19 Os irmãos de Davi estavam com Saul e o exército israelita no vale de Elá, lutando contra os filisteus.
20 Kashegari da sassafe, Dawuda ya tashi ya bar tumakinsa wa wani yă lura da su, sai ya ɗauki kayansa, ya kama hanya kamar yadda Yesse ya umarce shi. Ya isa sansanin daidai sa’ad da rundunar tana fitowa zuwa bakin dāgā, suna kirarin yaƙi.
20 Davi deixou as ovelhas com outro pastor e, na manhã seguinte, partiu bem cedo com os presentes, como Jessé havia ordenado. Chegou ao acampamento quando o exército israelita saía para o campo de batalha com gritos de guerra.
21 Isra’ila da Filistiyawa suka ja dāgā suna fuskantar junansu.
21 Logo, filisteus e israelitas estavam frente a frente, exército contra exército.
22 Dawuda ya bar kayansa a wajen wani mai lura da kaya, sai ya ruga zuwa bakin dāgā yă gai da ’yan’uwansa.
22 Davi deixou suas coisas com o responsável pelos suprimentos e correu até a frente de batalha para saudar seus irmãos.
23 Da yana magana da su sai Goliyat, jarumin nan Bafilistin daga Gat ya fito daga rundunar Filistiyawa, ya tā da murya kamar yadda ya saba. Dawuda kuwa ya ji shi.
23 Enquanto falava com eles, Golias, o guerreiro filisteu de Gate, saiu das fileiras do exército filisteu. Davi o ouviu gritar seu desafio habitual.
24 Da Isra’ilawa suka ga mutumin, sai dukansu suka gudu saboda tsananin tsoro.
24 Quando os israelitas viram Golias, começaram a fugir, apavorados.
25 Isra’ilawa suka yi ta cewa, “Kun ga yadda wannan mutum yana ta fitowa? Yana fitowa ne don yă kalubalanci Isra’ila. Sarki zai sāka wa mutumin da ya kashe wannan da dukiya mai yawa. Zai kuma ba shi ’yarsa yă aura, yă cire suna mahaifinsa daga biyan kuɗin haraji cikin Isra’ila.”
25 “Vocês viram aquele homem?”, perguntavam uns aos outros. “Ele sai todos os dias para desafiar Israel. O rei ofereceu uma grande recompensa para quem o matar. Dará uma de suas filhas como esposa e isentará toda a família dele de pagar impostos!”
26 Dawuda ya tambayi mutanen da suke tsaye kusa da shi ya ce, “Me za a yi wa wanda ya kashe Bafilistin nan, ya kuma cire wannan kunya daga Isra’ila? Wane ne wannan bafilistin marar kaciya da yake kalubalantar rundunar yaƙi na Allah mai rai?”
26 Então Davi perguntou aos soldados que estavam por perto: “O que receberá o homem que matar esse filisteu e acabar com suas provocações contra Israel? Afinal de contas, quem é esse filisteu incircunciso para desafiar os exércitos do Deus vivo?”.
27 Sai suka sāke gaya masa abin da suka faɗa cewa, “Ga abin da zai faru da wanda ya kashe shi.”
27 Os soldados repetiram o que tinham dito e confirmaram: “Sim, essa será a recompensa para quem o matar”.
28 Da wansa Eliyab, ya ji yana magana da mutanen, sai ransa ya ɓace ƙwarai saboda fushi, sai ya ce wa Dawuda, “Me ka zo yi a nan? Wa kuma ka bar wa ’yan tumakin a jeji? Na san ka da taurinkai, da kuma mugun hali. Ka zo nan ne don ka yi kallon yaƙi kawai.”
28 Quando Eliabe, irmão mais velho de Davi, o ouviu falando com os soldados, ficou furioso e perguntou: “O que você está fazendo aqui? Não devia estar tomando conta daquelas poucas ovelhas? Conheço sua arrogância e suas más intenções. Você quer apenas ver a batalha!”.
29 Dawuda ya ce, “To, yanzu me na yi? Ba zan ma yi magana ba?”
29 “O que eu fiz agora?”, disse Davi. “Só fiz uma pergunta!”
30 Sai ya juya wajen wani kuma ya sāke kawo zancen, mutanen kuwa suka amsa masa kamar dā.
30 Então foi até outros soldados, fez a mesma pergunta e recebeu a mesma resposta.
31 Aka ji abin da Dawuda ya ce, aka kuwa gaya wa Shawulu, Shawulu kuma ya aika a kawo shi.
31 Alguém contou ao rei Saul o que Davi tinha dito, e o rei mandou chamá-lo.
32 Da Shawulu ya tambayi Dawuda, sai Dawuda ya ce masa, “Kada kowa yă damu saboda wannan Bafilistin. Bawanka zai je yă yi faɗa da shi.”
32 Davi disse a Saul: “Ninguém se preocupe por causa desse filisteu. Seu servo vai lutar contra ele”.
33 Shawulu ya ce, “Ba za ka iya yin faɗa da wannan Bafilistin ba, ya daɗe yana yaƙi, ya yi yaƙi tun yana saurayi. Ga shi kuwa kai ɗan yaro ne kawai.”
33 Saul respondeu: “Você não conseguirá lutar contra esse filisteu e vencer! É apenas um rapaz, e ele é guerreiro desde a juventude”.
34 Amma Dawuda ya ce wa Shawulu, “Bawanka yana kiwon tumakin mahaifinsa. Sa’ad da zaki ko beyar ta zo ta kama tunkiya, ta tafi da ita.
34 Davi, porém insistiu: “Tomo conta das ovelhas de meu pai e, quando um leão ou um urso aparece para levar um cordeiro do rebanho,
35 Nakan bi ta a baya in buga ta in kuma ƙwato tunkiyar daga bakinta. In kuma ta taso mini, nakan cafke ta a gashinta in buga ta in kashe.
35 vou atrás dele com meu cajado e tiro o cordeiro de sua boca. Se o animal me ataca, eu o seguro pela mandíbula e dou golpes nele com o cajado até ele morrer.
36 Bawanka ya kashe zaki da beyar, wannan Bafilistin marar kaciya zai zama kamar ɗaya daga cikinsu, domin ya rena rundunar Allah mai rai.
36 Fiz isso com o leão e o urso, e farei o mesmo com esse filisteu incircunciso, pois ele desafiou os exércitos do Deus vivo!”.
37 Ubangiji wanda ya cece ni daga kumbar zaki da kuma kumbar beyar, zai cece ni daga hannun wannan Bafilistin.”
37 E disse ainda: “O S enhor que me livrou das garras do leão e do urso também me livrará desse filisteu!”. Por fim, Saul consentiu. “Está bem, então vá”, disse. “E que o S
38 Sai Shawulu ya kawo kayan yaƙinsa ya sa wa Dawuda. Ya sa masa hular kwanon da aka yi da tagulla a kansa, ya kuma sa masa rigar ƙarfensa.
38 Então Saul deu a Davi sua própria armadura, incluindo uma couraça e um capacete de bronze.
39 Dawuda ya ɗaura māshin Shawulu a sulken, ya yi ƙoƙari yă zaga, sai ya ji ba zai iya ba saboda bai saba ba.
39 Davi prendeu a espada sobre a armadura e tentou dar alguns passos, pois nunca tinha usado essas coisas. “Não consigo andar com tudo isso, pois não estou acostumado”, disse a Saul, e tirou a armadura.
40 Sai ya ɗauki sandansa, ya zaɓi duwatsu guda biyar masu sulɓi daga cikin rafi, ya sa su a ’yar jakarsa ta makiyaya; ya kuma ɗauki majajjawarsa, ya tafi, yă fuskanci Bafilistin.
40 Pegou cinco pedras lisas de um riacho e as colocou em sua bolsa de pastor. Armado apenas com seu cajado e sua funda, foi enfrentar o filisteu.
41 Ana ciki haka, sai Bafilistin nan shi ma ya fita yana gusowa zuwa wurin Dawuda. Mai riƙe masa garkuwar yaƙi kuwa yana tafe a gabansa.
41 Golias, com seu escudeiro à frente, caminhava em direção a Davi,
42 Bafilistin ya dubi Dawuda daga sama har ƙasa, ya gan dai ɗan yaro ne kawai, kyakkyawa kuma mai ƙoshin lafiya, sai ya rena shi.
42 rindo com desprezo do belo jovem ruivo.
43 Ya ce masa, “Kana tsammani ni kare ne da za ka zo mini da sanda?” Sai ya la’anci Dawuda da sunayen allolin Filistiyawa.
43 Gritou para Davi: “Por acaso sou um cão para que você venha a mim com um pedaço de pau?”. E amaldiçoou Davi em nome de seus deuses.
44 Ya ce, “Zo nan, ni kuwa zan ba da naman jikinka ga tsuntsayen sama da namun jeji su ci.”
44 “Venha cá, e darei sua carne às aves e aos animais selvagens!”, berrou Golias.
45 Dawuda ya ce wa Bafilistin, “Kana zuwa ka yaƙe ni da māshi da takobi da kere, amma ni ina zuwa in yaƙe ka a cikin sunan Ubangiji Maɗaukaki, Allah na rundunar Isra’ila, wanda ka rena.
45 Davi respondeu ao filisteu: “Você vem a mim com uma espada, uma lança e um dardo, mas eu vou enfrentá-lo em nome do S enhor dos Exércitos, o Deus dos exércitos de Israel, que você desafiou.
46 Yau nan, Ubangiji zai bashe ka a hannuna, zan kuwa kashe ka, in datse kanka. Yau, zan ba da gawawwakin rundunar Filistiyawa ga tsuntsayen sama da namun jeji, da haka duniya za tă sani lalle akwai Allah a cikin Isra’ila.
46 Hoje o S enhor entregará você em minhas mãos, e eu o matarei e cortarei sua cabeça. Então darei os cadáveres de seus homens às aves e aos animais selvagens, e o mundo todo saberá que há Deus em Israel!
47 Duk waɗanda suka taru a nan za su san cewa ba da māshi ko takobi ne Ubangiji yake ceto ba, gama yaƙin nan na Ubangiji ne, shi kuwa zai bashe ku duka a hannuwanmu.”
47 E todos que estão aqui reunidos saberão que o S enhor salva seu povo, mas não com espada nem com lança. A batalha é do S enhor , e ele entregará vocês em nossas mãos!”.
48 Yayinda Bafilistin yana matsowa kusa domin yă fāɗa wa Dawuda, sai Dawuda ya ruga a guje zuwa bakin dāgā don yă same shi.
48 Quando o filisteu se aproximou para atacar, Davi foi correndo enfrentá-lo.
49 Ya sa hannu a jakarsa ya ɗauki dutse, ya sa cikin majajjawa ya wurga, dutsen kuwa ya bugi Bafilistin a goshi, dutsen ya shiga cikin goshinsa, sai Bafilistin ya fāɗi rubda ciki.
49 Enfiou a mão na bolsa, pegou uma pedra e atirou-a com sua funda. A pedra acertou o filisteu na testa e ficou encravada ali. E Golias caiu com o rosto em terra.
50 Da majajjawa da dutse kawai Dawuda ya ci nasara a kan Bafilistin. Ya buge shi, ya kashe shi ba tare da takobi a hannunsa ba.
50 Assim, Davi venceu o filisteu e o matou com apenas uma funda e uma pedra, pois não tinha espada.
51 Dawuda ya ruga ya tsaya a bisan Bafilistin, ya zare takobin Bafilistin daga kubensa, ya datse masa kai da shi.
51 Em seguida, correu até o filisteu, puxou da bainha a espada dele e a usou para matá-lo e cortar-lhe a cabeça. Quando os filisteus viram que seu melhor guerreiro estava morto, deram meia-volta e fugiram.
52 Mutanen Isra’ila da na Yahuda suka rugo gaba da babbar murya, suka fafari Filistiyawa har zuwa mashigin Gat da kuma ƙofofin Ekron. Gawawwakin Filistiyawa suka bazu a hanyar Sha’arayim zuwa Gat da kuma Ekron.
52 Os soldados de Israel e de Judá soltaram um forte grito de vitória e perseguiram os filisteus até Gate e até os portões de Ecrom. E os corpos dos filisteus mortos e feridos ficaram espalhados pelo caminho de Saarim até Gate e Ecrom.
53 Da Isra’ilawa suka komo daga bin Filistiyawa sai suka washe sansanin Filistiyawa.
53 Então o exército israelita voltou e saqueou o acampamento abandonado dos filisteus.
54 Dawuda ya ɗauki kan Bafilistin zuwa Urushalima. Sai Dawuda ya ajiye kayan yaƙin Bafilistin a tentinsa.
54 (Davi levou a cabeça do filisteu para Jerusalém, mas guardou as armas dele em sua própria tenda.)
55 Yayinda Shawulu yake kallon Dawuda sa’ad da za shi yă yaƙi Bafilistin, sai ya tambayi Abner, komandan rundunarsa ya ce, “Abner, ɗan wane ne wannan saurayi?”
55 Quando Saul viu Davi sair para lutar contra os filisteus, perguntou a Abner, o comandante de seu exército: “Abner, quem é o pai desse rapaz?”. “Não faço ideia, ó rei!”, disse Abner.
56 Sarki ya ce, “Ka tambaya mini ko yaron wane ne wannan saurayi.”
56 “Então descubra quem é o pai dele!”, ordenou.
57 Dawuda yana dawowa daga karkashe Filistiyawa ke nan, sai Abner ya kai shi gaban Shawulu, riƙe da kan Bafilistin.
57 Assim que Davi voltou, depois de matar Golias, Abner o levou a Saul. Ele ainda carregava a cabeça do filisteu em suas mãos.
58 Sai Shawulu ya ce, “Kai ɗan wane ne, saurayi?”
58 Saul perguntou: “Quem é seu pai, meu rapaz?”. E Davi respondeu: “Sou filho de Jessé, que vive em Belém”.

Ler em outra tradução

Comparar com outra

Estude este capítulo no WhatsApp

Peça à IA da Bíblia Fala para explicar 1 Samuel 17, comparar traduções ou montar um estudo — tudo direto pelo WhatsApp.