1 Reis 20

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (HAUSA) vs VC

Sair da comparação
VC Versão Católica
1 Ben-Hadad sarkin Aram kuwa ya tattara mayaƙansa gaba ɗaya. Sarakuna talatin da biyu suka tafi tare da shi haɗe da dawakansu da kekunan yaƙinsu. Ya haura ya yi wa Samariya kwanto, ya kuma yaƙe ta.
1 Ben-Hadad, rei da Síria, mobilizou todo o seu exército. Tinha com ele trinta e dois reis, cavalos e carros. Subiu, pôs o cerco diante de Samaria e atacou-a.
2 Ya aika da ’yan aika zuwa cikin birnin wurin Ahab sarkin Isra’ila yana cewa, “Ga abin da Ben-Hadad ya ce,
2 Mandou mensageiros a Acab, rei de Israel, na cidade, com esta mensagem:
3 ‘Azurfarka da zinariyarka nawa ne. Mafi kyau cikin matanka da ’ya’yanka nawa ne.’ ”
3 Eis o que diz Ben-Hadad: Tua prata e teu ouro são meus. São minhas as tuas mulheres e os mais belos de teus filhos.
4 Sarkin Isra’ila ya amsa, ya ce, “Kamar dai yadda ka faɗa, ranka yă daɗe, sarki. Ni da dukan abin da nake da shi, naka ne.”
4 Como tu dizes, meu senhor e rei, respondeu Acab, eu sou teu com tudo o que me pertence.
5 Sai ’yan aikan suka sāke dawo suka ce, “Ga abin da Ben-Hadad ya ce, ‘Na aika ka ba da azurfarka da zinariyarka, matanka da kuma ’ya’yanka.
5 Mas os mensageiros voltaram e disseram: Isto diz Ben-Hadad: Mandou-te dizer: dá-me tua prata e teu ouro, tuas mulheres e teus filhos.
6 Amma war haka gobe zan aika shugabannina su bincika fadanka da kuma gidajen shugabanninka. Za su kwashe dukan abubuwan da kake ganin darajarsu su tafi.’ ”
6 Amanhã, pois, a esta mesma hora, mandarei os meus servos à tua casa; eles a revistarão, assim como as casas de teus servos; tomarão com as suas mãos tudo o que lhes aprouver.
7 Sarkin Isra’ila ya tattara dukan dattawan ƙasar, ya ce musu, “Ku duba fa, wannan mutum yana neman tsokana! Sa’ad da ya aika in ba shi matana da ’ya’yana, azurfana da zinariyana, ban hana masa ba.”
7 Então o rei de Israel convocou todos os anciãos da terra e disse-lhes: Considerai e vede que esse homem quer a nossa perda. Quando me mandou pedir minhas mulheres, meus filhos, minha prata e meu ouro, nada lhe recusei.
8 Dattawa da dukan mutane suka amsa, suka ce, “Kada ka saurare shi ko ka yarda da abin da yake bukata.”
8 Os anciãos e todo o povo disseram-lhe: Não lhe dês ouvidos, nem o atendas em nada.
9 Saboda haka ya ba wa ’yan aikan Ben-Hadad amsa, ya ce, “Ku faɗa wa ranka yă daɗe, sarki, ‘Bawanka zai yi dukan abin da ka bukaci da farko, amma wannan na ƙarshe ba zan iya yin ba.’ ” Suka tafi suka kai amsar wa Ben-Hadad.
9 Acab respondeu aos mensageiros de Ben-Hadad: Dizei ao rei, meu senhor: estou pronto a fazer o que pediste ao teu servo da primeira vez; mas o que agora exiges, não o posso consentir. Os mensageiros foram-se e deram tal resposta ao rei.
10 Sai Ben-Hadad ya aika da wani saƙo wa Ahab, ya ce, “Bari alloli su yi da ni yadda suke so, su kuma yi haka da tsanani, in isashen ƙura ta rage a Samariya da za a iya ba wa mutanena a tafin hannu.”
10 Ben-Hadad mandou dizer a Acab: Que os deuses me tratem com o mais extremo rigor, se o pó da Samaria bastar para encher o côncavo da mão dos guerreiros que me seguem!
11 Sarki Isra’ila ya amsa, ya ce, “Ku faɗa masa, ‘Wanda ya sa kayan yaƙinsa bai kamata yă yi fariya ba sai ya tuɓe su.’ ”
11 O rei de Israel, respondendo, disse: Dizei-lhe que aquele que põe o seu cinturão não deve gloriar-se como aquele que o tira.
12 Ben-Hadad ya ji wannan saƙo yayinda shi da sarakunan suke sha a cikin tentunansu, sai ya umarce mutanensa, ya ce, “Ku shirya don yaƙi.” Saboda haka suka shirya don su yaƙi birnin.
12 Recebendo esta resposta, Ben-Hadad, que estava bebendo nas suas tendas com os reis, disse à sua gente: Aos vossos postos! E eles ordenaram as tropas para o ataque à cidade.
13 Ana cikin haka sai wani annabi ya zo wurin Ahab sarkin Isra’ila ya sanar masa cewa, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Ka ga wannan ɗumbun mayaƙa? Zan ba da su cikin hannunka a yau, sa’an nan za ka san cewa ni ne Ubangiji.’ ”
13 Nesse momento, um profeta aproximou-se de Acab, rei de Israel, e disse-lhe: Eis o que diz o Senhor: Vês esta imensa multidão? Pois declaro-te que hoje te entrego nas mãos, para que saibas que eu sou o Senhor.
14 Ahab ya ce, “Amma wa zai yi haka?”
14 Acab perguntou: Por quem será ela entregue? O profeta respondeu: Assim fala o Senhor: Por meio dos servos dos chefes de províncias. Quem começará o combate? Tu mesmo.
15 Saboda haka Ahab ya kira sojoji matasa na shugabannin yankuna, mutum 232. Sa’an nan ya tattara sauran Isra’ilawa su 7,000 gaba ɗaya.
15 Acab passou em revista os servos dos chefes de províncias, e encontrou duzentos e trinta e dois. Depois contou todo o povo dos israelitas, e viu que eram sete mil.
16 Suka fita da tsakar rana yayinda Ben-Hadad tare da sarakuna 32 masu goyon bayansa suke cikin tentunansu suna sha, suna buguwa.
16 Saíram ao meio-dia, quando Ben-Hadad bebia e se embriagava nas tendas com os trinta e dois reis, seus auxiliares.
17 Sojojin nan matasa na shugabannin yankuna suka fara fita.
17 Os servos dos chefes de províncias tinham saído em primeiro lugar. Ben-Hadad mandou ver o que se passava. Disseram-lhe: São alguns homens que saem de Samaria.
18 Ya ce, “In sun fito don salama, ku kamo su da rai; in sun fito yaƙi ne, ku kamo su da rai.”
18 O rei disse: Venham eles para tratar de paz, ou venham para combater, capturai-os vivos.
19 Sojojin nan matasa na shugabannin yankuna suka taka suka fita daga birnin da mayaƙa a bayansu.
19 Os servos dos chefes de províncias saíram, pois, da cidade, seguidos do exército.
20 Kowannensu kuwa ya buge abokin gābansa. Ganin wannan, sai Arameyawa suka gudu, Isra’ilawa suna bi. Amma Ben-Hadad na Aram ya tsere a kan dokinsa tare da waɗansu mahayan dawakansa.
20 Cada um deles feriu o seu homem. Os sírios fugiram, perseguidos por Israel; Ben-Hadad, rei da Síria, fugiu a cavalo com alguns cavaleiros.
21 Sarki Isra’ila ya bi, ya kuma sha ƙarfin dawakan da keken yaƙin, ya kashe Arameyawa da yawa.
21 Então o rei de Israel saiu e feriu cavalos e carros, causando uma grande ruína aos sírios.
22 Daga baya, annabin ya zo wurin sarkin Isra’ila ya ce, “Ka ƙarfafa matsayinka ka kuma ga abin da za a yi, gama a bazara mai zuwa sarkin Aram zai sāke kawo yaƙi.”
22 O profeta foi ter com o rei de Israel e disse-lhe: Vai, cobra ânimo e examina o que te é preciso fazer, porque no próximo ano voltará o rei da Síria para atacar-te.
23 Ana cikin haka, shugabannin sarkin Aram suka ba shi shawara, “Allolinsu, allolin tuddai ne. Shi ya sa suka fi mu ƙarfi. Amma in mun yaƙe su a fili, tabbatacce za mu fi su ƙarfi.
23 Os servos do rei da Síria disseram ao seu soberano: O seu deus é um deus dos montes; por isso foram mais fortes do que nós. Se os atacarmos na planície, veremos se não somos os mais fortes.
24 Ka yi wannan. Ka cire dukan sarakuna daga matsayinsu ka sa waɗansu shugabanni a maimakonsu.
24 Eis o que tens de fazer: Destitui todos os reis e substitui-os por governadores.
25 Dole kuma ka tā da waɗansu mayaƙa kamar waɗanda ka rasa, doki don doki, keken yaƙi kuma don keken yaƙi, saboda mu iya yaƙe Isra’ila a fili. Ta haka tabbatacce za mu fi ƙarfinsu.” Sai ya yarda da su, ya kuma yi haka.
25 Levanta um exército semelhante ao que perdeste, uma cavalaria equivalente e outro tanto de carros. Combateremos na planície e com toda a certeza seremos mais fortes do que eles. O rei ouviu e seguiu o seu conselho.
26 Bazara na biye Ben-Hadad ya tattara Arameyawa, ya haura zuwa Afek don yă yaƙi Isra’ila.
26 No ano seguinte, Ben-Hadad, depois de ter passado em revista os sírios, avançou até Afec para combater Israel.
27 Sa’ad da aka tattara Isra’ilawa, aka kuma ba su guzuri, sai suka taka suka fita don su sadu da Arameyawa. Isra’ilawa suka kafa sansani ɗaura da su kamar ƙananan garkuna biyu na awaki, yayinda Arameyawa suka rufe dukan jejin.
27 Os israelitas recenseados e providos de víveres foram contra os sírios e acamparam diante deles. Eram como dois pequenos rebanhos de cabras, enquanto os sírios cobriam toda a terra.
28 Sai mutumin Allah ya zo ya ce wa sarkin Isra’ila, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Domin Arameyawa suna tsammani Ubangiji allahn tuddai ne, ba allahn kwari ba, zan ba da wannan ɗumbun mayaƙa a hannuwanka, za ka kuwa sani ni ne Ubangiji.’ ”
28 Então o homem de Deus aproximou-se do rei de Israel e disse-lhe: Isto diz o Senhor: Porque os sírios disseram: O Senhor é um deus dos montes e não das planícies - vou entregar-te nas mãos essa imensa multidão, a fim de que saibas que eu sou o Senhor.
29 Kwana bakwai suka yi sansani ɗaura da juna, a rana ta bakwai sai yaƙi ya haɗu. Isra’ilawa suka kashe sojojin kafa na Arameyawa dubu ɗari a rana ɗaya.
29 Durante sete dias ficaram acampados um em face do outro. No sétimo dia deu-se a batalha; os israelitas mataram num só dia cem mil sírios.
30 Sauransu suka tsere zuwa birnin Afek, inda katangar ya fāɗa a kan mutum dubu ashirin da bakwai. Sai Ben-Hadad ya gudu zuwa birni ya ɓuya a ciki cikin ɗaki.
30 O resto fugiu para a cidade de Afec, mas as muralhas caíram sobre os vinte e sete mil sobreviventes. Ben-Hadad, que se refugiara na cidade, escondia-se de quarto em quarto.
31 Fadawansa suka je suka ce masa, “Mun ji an ce sarakunan Isra’ila masu jinƙai ne, bari mu sa tufafin makoki, mu ɗaura igiyoyi a wuyanmu, sa’an nan mu tafi wurin sarkin Isra’ila, wataƙila zai bar ka da rai.”
31 Seus servos disseram-lhe: Ouve: nós temos ouvido dizer que os reis de Israel são clementes. Ponhamos sacos sobre nossos rins e cordas ao nosso pescoço, e vamos ter com o rei de Israel; talvez ele te poupe a vida.
32 Saye da tufafin makoki kewaye a gindinsu, da kuma igiyoyi kewaye da kawunansu, suka tafi wurin sarkin Isra’ila, suka ce, “Bawanka Ben-Hadad ya ce, ‘Ina roƙonka bari in rayu.’ ”
32 Cingiram-se, pois, com sacos pelos rins, puseram cordas em volta do pescoço, e apresentaram-se ao rei de Israel, dizendo: Teu servo Ben-Hadad roga-te: Concede-me a vida! Ele está ainda vivo?, perguntou Acab; mas ele é meu irmão!
33 Da ma abin da fadawan suke so su ji ke nan, sai suka yi sauri, suka karɓi maganar a bakinsa, suka ce, “I, ɗan’uwanka, Ben-hadad!”
33 Tomando bom augúrio dessas palavras, os sírios tomaram logo a palavra de sua boca e disseram-lhe: Ben-Hadad é teu irmão! Trazei-mo, disse o rei. Veio Ben-Hadad à presença de Acab, e este mandou-o subir ao seu carro.
34 Ben-Hadad ya ce, “Zan mayar da biranen mahaifinka da na ƙwace daga mahaifinka. Za ka iya sa wurin kasuwarka a cikin Damaskus, kamar yadda mahaifinka ya yi a Samariya.”
34 Vou restituir-te, disse Ben-Hadad, as cidades que meu pai tomou do teu. Terás um quarteirão em Damasco, como meu pai o tinha em Samaria. Eu, disse Acab, feita esta aliança, te deixarei partir. Acab fez um tratado com Ben-Hadad e deixou-o ir livre.
35 Ta wurin maganar Ubangiji, ɗaya daga cikin ’ya’ya maza na annabawa ya ce wa abokinsa, “Ka buge ni da makaminka,” amma mutumin ya ƙi.
35 Então um dos filhos dos profetas disse ao seu companheiro, por ordem do Senhor: Fere-me. Mas o outro recusou.
36 Sai annabin ya ce, “Domin ba ka yi biyayya da Ubangiji ba, da zarar ka bar ni zaki zai kashe ka.” Daga baya mutumin ya tafi, zaki ya same shi, ya kuma kashe shi.
36 Porque não ouviste a voz do Senhor, disse-lhe o primeiro, logo que me tiveres deixado, serás morto por um leão. Mal se havia afastado, um leão o encontrou e o matou.
37 Annabin ya sami wani mutum ya ce, “Ka buge ni, ina roƙonka.” Sai mutumin ya buge shi, ya ji masa ciwo.
37 O profeta, encontrando depois outro homem, disse-lhe: Fere-me. Este homem lançou-se contra ele e o feriu.
38 Sa’an nan annabin ya tafi ya tsaya a bakin hanya yana jiran sarki. Ya ɓad da kamanni da ƙyalle a kansa. Ƙyallen ya sauka zuwa bisa idanunsa.
38 Então postou-se o profeta no caminho por onde devia passar o rei, pondo nos olhos uma faixa que o tornava irreconhecível.
39 Yayinda sarki yake wucewa, sai annabin ya yi kira da ƙarfi gare shi ya ce “Ni bawanka na tafi yaƙi, sai ga wani ya kawo mini wani mutum, ya ce, ‘Ka riƙe wannan mutum, kada ka bar shi yă kuɓuta ko da ƙaƙa, idan ka bari ya kuɓuta, a bakin ranka, ko kuwa ka biya talanti ɗaya na azurfa.’
39 Tendo o rei passado, ele pôs-se a gritar-lhe: Teu servo estava em pleno combate, quando alguém lhe trouxe um homem, dizendo: Guarda este homem! Se ele desaparecer, a tua vida responderá pela sua, ou então pagarás um talento de prata.
40 Yayinda bawanka yana fama, yana kai da kawowa, sai mutumin ya ɓace.”
40 Mas andando o teu servo ocupado daqui e dali, o prisioneiro desapareceu. O rei de Israel disse-lhe: Esta é a tua sentença; tu mesmo a pronunciaste.
41 Sai annabin ya cire ƙyallen da sauri daga kansa, da ya rufe idanunsa, sarkin Isra’ila kuwa ya gane shi a matsayi ɗaya daga cikin annabawa.
41 Então o outro tirou subitamente a faixa que lhe cobria os olhos, e o rei viu que ele era um dos profetas.
42 Sai ya ce wa sarki, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Ka saki mutumin da na ƙudura yă mutu. Saboda haka ranka zai zama a maimakon ransa, mutanenka a maimakon mutanensa.’ ”
42 Ele disse ao rei: Eis o que diz o Senhor: Pois que deixaste escapar de tuas mãos o homem que eu tinha votado ao interdito, tua vida responderá pela sua, e teu povo pelo seu povo.
43 Cike da fushi, sarkin Isra’ila ya tafi fadarsa a Samariya.
43 O rei de Israel voltou para a sua casa sombrio e irritado, e chegou a Samaria.

Ler em outra tradução

Comparar com outra

Estude este capítulo no WhatsApp

Peça à IA da Bíblia Fala para explicar 1 Reis 20, comparar traduções ou montar um estudo — tudo direto pelo WhatsApp.