1 João 3
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (HAUSA) vs ARIB
1 Dubi irin ƙaunar da Uba ya ƙaunace mu da ita mana, har ana ce da mu ’ya’yan Allah! Haka kuwa muke! Dalilin da ya sa duniya ba tă san mu ba shi ne, don ba tă san shi ba.
1 Vede que grande amor nos tem concedido o Pai: que fôssemos chamados filhos de Deus; e nós o somos. Por isso o mundo não nos conhece; porque não conheceu a ele.
2 Abokaina ƙaunatattu, yanzu, mu ’ya’yan Allah ne, kuma abin da za mu zama nan gaba ba a riga an bayyana ba. Sai dai mun san cewa sa’ad da Kiristi ya bayyana, za mu zama kamar sa, domin za mu gan shi kamar yadda yake.
2 Amados, agora somos filhos de Deus, e ainda não é manifesto o que havemos de ser. Mas sabemos que, quando ele se manifestar, seremos semelhantes a ele; porque assim como é, o veremos.
3 Duk mai wannan bege a cikinsa yakan tsarkake kansa, kamar yadda shi Kiristi yake da tsabta.
3 E todo o que nele tem esta esperança, purifica-se a si mesmo, assim como ele é puro.
4 Duk mai yin zunubi yana karya doka ne; tabbatacce, zunubi, karya doka ne.
4 Todo aquele que vive habitualmente no pecado também vive na rebeldia, pois o pecado é rebeldia.
5 Sai dai kun san cewa Kiristi ya bayyana ne domin yă ɗauke zunubanmu. A cikinsa kuwa babu zunubi.
5 E bem sabeis que ele se manifestou para tirar os pecados; e nele não há pecado.
6 Ba mai rayuwa a cikinsa da yake cin gaba da yin zunubi. Kowa da yake aikata zunubi, bai taɓa ganinsa ba, bai ma san shi ba.
6 Todo o que permanece nele não vive pecando; todo o que vive pecando não o viu nem o conhece.
7 ’Ya’yana ƙaunatattu, kada ku yarda wani yă ruɗe ku. Duk mai yin abin da yake daidai mai adalci ne, yadda Kiristi yake mai adalci.
7 Filhinhos, ninguém vos engane; quem pratica a justiça é justo, assim como ele é justo;
8 Duk mai aikata abin da yake zunubi shi na Iblis ne, domin Iblis mai aikata zunubi ne tun farko. Dalilin da ya sa Ɗan Allah ya bayyana kuwa shi ne don yă rushe aikin Iblis.
8 quem comete pecado é do Diabo; porque o Diabo peca desde o princípio. Para isto o Filho de Deus se manifestou: para destruir as obras do Diabo.
9 Babu haifaffe na Allah da zai ci gaba da yin zunubi, domin iri na Allah yana a cikinsa; ba zai iya ci gaba da yin zunubi ba, domin haifaffe ne na Allah.
9 Aquele que é nascido de Deus não peca habitualmente; porque a semente de Deus permanece nele, e não pode continuar no pecado, porque é nascido de Deus.
10 Ta haka muka san waɗanda suke ’ya’yan Allah da kuma waɗanda suke ’ya’yan Iblis. Duk wanda ba ya yin abin da yake daidai, ba ɗan Allah ba ne; haka ma wanda ba ya ƙaunar ɗan’uwansa.
10 Nisto são manifestos os filhos de Deus, e os filhos do Diabo: quem não pratica a justiça não é de Deus, nem o que não ama a seu irmão.
11 Wannan shi ne saƙon da kuka ji tun farko. Ya kamata mu ƙaunaci juna.
11 Porque esta é a mensagem que ouvistes desde o princípio, que nos amemos uns aos outros,
12 Kada ku zama kamar Kayinu, wanda ya zama na mugun nan, ya kuma kashe ɗan’uwansa. Me ya sa ya kashe shi? Domin ayyukansa mugaye ne, na ɗan’uwansa kuma na adalci ne.
12 não sendo como Caim, que era do Maligno, e matou a seu irmão. E por que o matou? Porque as suas obras eram más e as de seu irmão justas.
13 Kada ku yi mamaki ’yan’uwana, in duniya ta ƙi ku.
13 Meus irmãos, não vos admireis se o mundo vos odeia.
14 Mun san cewa mun riga mun ratsa daga mutuwa zuwa rai, domin muna ƙaunar ’yan’uwanmu. Duk wanda ba ya ƙauna matacce ne har yanzu.
14 Nós sabemos que já passamos da morte para a vida, porque amamos os irmãos. Quem não ama permanece na morte.
15 Duk mai ƙin ɗan’uwansa mai kisankai ne, kun kuma san cewa ba mai kisankan da yake da rai madawwami a cikinsa.
15 Todo o que odeia a seu irmão é homicida; e vós sabeis que nenhum homicida tem a vida eterna permanecendo nele.
16 Yadda muka san ƙauna ke nan, wato, Yesu Kiristi ya ba da ransa dominmu. Ya kamata mu ma mu ba da rayukanmu domin ’yan’uwanmu.
16 Nisto conhecemos o amor: que Cristo deu a sua vida por nós; e nós devemos dar a vida pelos irmãos.
17 In wani yana da arziki, ya kuma ga ɗan’uwansa cikin rashi, bai kuwa taimake shi ba, anya, ƙaunar Allah tana a cikinsa kuwa?
17 Quem, pois, tiver bens do mundo, e, vendo o seu irmão necessitando, lhe fechar o seu coração, como permanece nele o amor de Deus?
18 ’Ya’yana ƙaunatattu, kada mu yi ƙauna da fatar baki kawai, sai dai mu nuna ta ta wurin aikatawa da kuma gaskiya.
18 Filhinhos, não amemos de palavra, nem de língua, mas por obras e em verdade.
19 Ta haka muka san cewa mu na gaskiya ne, kuma za mu iya tsaya a gaban Allah ba tare da rawar jiki ba.
19 Nisto conheceremos que somos da verdade, e diante dele tranqüilizaremos o nosso coração;
20 Idan zuciyarmu ta nuna mana muna da laifi, mun san cewa Allah ya fi zuciyarmu, ya kuma san dukan kome.
20 porque se o coração nos condena, maior é Deus do que o nosso coração, e conhece todas as coisas.
21 Abokaina ƙaunatattu, in zukatanmu ba su ba mu laifi ba, muna da ƙarfin halin tsayawa a gaban Allah ke nan.
21 Amados, se o coração não nos condena, temos confiança para com Deus;
22 Muna kuma samun dukan abin da muka roƙa daga gare shi, domin muna biyayya da umarnansa, muna kuma yin abin da ya gamshe shi.
22 e qualquer coisa que lhe pedirmos, dele a receberemos, porque guardamos os seus mandamentos, e fazemos o que é agradável à sua vista.
23 Umarninsa kuwa shi ne, mu gaskata da sunan Ɗansa, Yesu Kiristi, mu kuma ƙaunaci juna kamar yadda ya umarce mu.
23 Ora, o seu mandamento é este, que creiamos no nome de seu Filho Jesus Cristo, e nos amemos uns aos outros, como ele nos ordenou.
24 Waɗanda suke biyayya da umarnansa kuwa suna rayuwa a cikinsa, shi kuma a cikinsu. Ta haka muka san cewa yana raye a cikinmu. Mun san haka ta wurin Ruhun da ya ba mu.
24 Quem guarda os seus mandamentos, em Deus permanece e Deus nele. E nisto conhecemos que ele permanece em nós: pelo Espírito que nos tem dado.
Atalhos do teclado
- Capítulo anterior←
- Próximo capítulo→
- Versículo anteriork
- Próximo versículoj
- Limpar seleçãoEsc
- Esta ajuda?
Estude este capítulo no WhatsApp
Peça à IA da Bíblia Fala para explicar 1 João 3, comparar traduções ou montar um estudo — tudo direto pelo WhatsApp.