Romanos 8

Litafi Mai-tsarki (HAU_ULB) vs VC

Sair da comparação
VC Versão Católica
1 Saboda haka babu kayarwa yanzu ga wadanda ke cikin Almasihu Yesu.
1 De agora em diante, pois, já não há nenhuma condenação para aqueles que estão em Jesus Cristo.
2 Domin ka'idar ruhun rai a cikin Almasihu Yesu ta maishe mu 'yanttatu daga ka'idar zunubi da mutuwa.
2 A lei do Espírito de Vida me libertou, em Jesus Cristo, da lei do pecado e da morte.
3 Saboda abin da shari'a bata iya aikatawa ba domin kasawa ta wurin jiki, Allah ya yi. Ya aiko da dansa a kamanin jiki mai zunubi domin ya zama hadaya domin zunubi, sai ya yi Allah wadai da zunubi a cikin jiki.
3 O que era impossível à lei, visto que a carne a tornava impotente, Deus o fez. Enviando, por causa do pecado, o seu próprio Filho numa carne semelhante à do pecado, condenou o pecado na carne,
4 Ya yi haka domin bukatar shari'a ta sami cika a cikinmu, mu da muke tafe ba ta gwargwadon jiki ba, amma ta gwargwadon ruhaniya.
4 a fim de que a justiça, prescrita pela lei, fosse realizada em nós, que vivemos não segundo a carne, mas segundo o espírito.
5 Wadanda ke rayuwa gwargwadon jiki sukan lura da al'amuran jiki, amma su da ke rayuwa a gwargwadon Ruhu sukan mai da hankali ga al'amuran Ruhu.
5 Os que vivem segundo a carne gostam do que é carnal; os que vivem segundo o espírito apreciam as coisas que são do espírito.
6 To kwallafa rai ga jiki mutuwa ce, amma kwallafa rai ga Ruhu rai ne da salama.
6 Ora, a aspiração da carne é a morte, enquanto a aspiração do espírito é a vida e a paz.
7 Haka yake domin kwallafa rai ga jiki gaba yake da Allah, gama baya biyyaya ga shari'ar Allah, balle ma ya iya.
7 Porque o desejo da carne é hostil a Deus, pois a carne não se submete à lei de Deus, e nem o pode.
8 Wadanda ke a jiki ba su iya faranta wa Allah zuciya.
8 Os que vivem segundo a carne não podem agradar a Deus.
9 Duk da haka, ba ku cikin jiki amma a cikin Ruhu, idan gaskiya ne, Ruhun Allah na rayuwa cikinku. Amma idan wani ba shi da Ruhun Almasihu, shi ba na sa bane.
9 Vós, porém, não viveis segundo a carne, mas segundo o Espírito, se realmente o espírito de Deus habita em vós. Se alguém não possui o Espírito de Cristo, este não é dele.
10 In Almasihu na cikinka, jikin ka fa matacce ne ga zunubi, amma ruhu na rayuwa bisa ga adalci.
10 Ora, se Cristo está em vós, o corpo, em verdade, está morto pelo pecado, mas o Espírito vive pela justificação.
11 Idan Ruhun wanda ya tada Yesu daga matattu na raye a cikinku, to shi wanda ya tada Almasihu da ga matattu za ya bada rai ga jikinku masu matuwa ta wurin Ruhunsa, da ke rayuwa a cikin ku.
11 Se o Espírito daquele que ressuscitou Jesus dos mortos habita em vós, ele, que ressuscitou Jesus Cristo dos mortos, também dará a vida aos vossos corpos mortais, pelo seu Espírito que habita em vós.
12 To, 'yan' uwa, muna da hakki amma ba bisa jiki ba, da za mu yi rayuwa bisa ga dabi'ar jiki.
12 Portanto, irmãos, não somos devedores da carne, para que vivamos segundo a carne.
13 Gama idan kun yi rayuwa gwargwadon jiki, za ku mutu kenan, amma idan ta wurin Ruhu ku ka kashe ayyukan jiki, za ku rayu.
13 De fato, se viverdes segundo a carne, haveis de morrer; mas, se pelo Espírito mortificardes as obras da carne, vivereis,
14 Gama duk wadanda Ruhun Allah ke bishe su, su 'ya 'yan Allah ne.
14 pois todos os que são conduzidos pelo Espírito de Deus são filhos de Deus.
15 Gama ba ku karbi ruhun bauta da ke sa tsoro ba. Maimakon haka, kun karbi ruhun diyanci, ta wurinsa muke tadda murya muna kira, “Abba, Uba!”
15 Porquanto não recebestes um espírito de escravidão para viverdes ainda no temor, mas recebestes o espírito de adoção pelo qual clamamos: Aba! Pai!
16 kansa na bada shaida tare da namu ruhun cewa mu 'ya'yan Allah ne.
16 O Espírito mesmo dá testemunho ao nosso espírito de que somos filhos de Deus.
17 Idan mu 'ya'ya ne, ai mu magada ne kenan, magadan Allah. Kuma mu magada ne tare da Almasihu, hakika idan mun sha wahala tare da shi za a kuma daukaka mu tare da shi.
17 E, se filhos, também herdeiros, herdeiros de Deus e co-herdeiros de Cristo, contanto que soframos com ele, para que também com ele sejamos glorificados.
18 Gama na yi la'akari cewa wahalonin zamanin nan ba su isa a kwatanta su da daukakar da za'a bayyana mana ba.
18 Tenho para mim que os sofrimentos da presente vida não têm proporção alguma com a glória futura que nos deve ser manifestada.
19 Saboda yadda halitta ke marmarin bayyanuwar 'ya'yan Allah.
19 Por isso, a criação aguarda ansiosamente a manifestação dos filhos de Deus.
20 Gama an kaskantar da halitta ga banza, ba da nufin ta ba, amma na shi wanda ya kaskantar da ita. Ta na cikin tabbacin alkawarin.
20 Pois a criação foi sujeita à vaidade {não voluntariamente, mas por vontade daquele que a sujeitou},
21 Cewa halitta kanta za ta kubuta daga bautar rubewa, kuma za a kawo ta zuwa ga 'yantarwa na yabon daukakar 'ya'yan Allah.
21 todavia com a esperança de ser também ela libertada do cativeiro da corrupção, para participar da gloriosa liberdade dos filhos de Deus.
22 Gama mun sani dukan halitta na nishi da zafin nakuda tare har ya zuwa yanzu.
22 Pois sabemos que toda a criação geme e sofre como que dores de parto até o presente dia.
23 Ba haka kadai ba, amma ko mu kanmu, da ke nunar farko na Ruhu—mu kanmu muna nishi acikin mu, muna jiran diyancinmu, wato ceton jikinmu kenan.
23 Não só ela, mas também nós, que temos as primícias do Espírito, gememos em nós mesmos, aguardando a adoção, a redenção do nosso corpo.
24 Gama ta wanan hakikancewa aka cece mu. Amma dai abin da muke da tabbacin zai faru ba mu gan shi ba tukuna, domin wanene wa ke begen tabbatacce abin da yake gani?
24 Porque pela esperança é que fomos salvos. Ora, ver o objeto da esperança já não é esperança; porque o que alguém vê, como é que ainda o espera?
25 Amma idan muna da tabbacin abin da ba mu gani ba tukuna, to sai mu jjira shi da hakuri.
25 Nós que esperamos o que não vemos, é em paciência que o aguardamos.
26 Hakanan, Ruhu kuma ke taimako a kasawarmu. Gama ba mu da san yadda zamu yi addu'a ba, amma Ruhu kansa na roko a madadinmu da nishe-nishen da ba'a iya ambatawa.
26 Outrossim, o Espírito vem em auxílio à nossa fraqueza; porque não sabemos o que devemos pedir, nem orar como convém, mas o Espírito mesmo intercede por nós com gemidos inefáveis.
27 Shi da ke bidar zuciya yana sane da tunanin Ruhu, domin yana roko a madadin masu badagaskiya ta wurin nufin Allah.
27 E aquele que perscruta os corações sabe o que deseja o Espírito, o qual intercede pelos santos, segundo Deus.
28 Mun san cewa ga wadanda ke kaunar Allah, yakan aikata dukan al'amura domin su zuwa ga alheri, ga duk wadanda aka kira bisa ga nufinsa. Dukan abubuwa sukan zama alheri.
28 Aliás, sabemos que todas as coisas concorrem para o bem daqueles que amam a Deus, daqueles que são os eleitos, segundo os seus desígnios.
29 Saboda wadanda ya sani tuntuni su ne ya kardara su zama da kamanin dansa, domin ya zama dan fari a cikin 'yan'uwa masu yawa.
29 Os que ele distinguiu de antemão, também os predestinou para serem conformes à imagem de seu Filho, a fim de que este seja o primogênito entre uma multidão de irmãos.
30 Su da ya kaddara, ya kiraye su. Wadanda ya kira, su ya kubutar. Su da ya kubutar, sune kuma ya daukaka.
30 E aos que predestinou, também os chamou; e aos que chamou, também os justificou; e aos que justificou, também os glorificou.
31 Me zamu ce game da wadannan al'amura? Idan Allah na tare da mu, wake gaba da mu?
31 Que diremos depois disso? Se Deus é por nós, quem será contra nós?
32 Shi da baya hana dansa ba, amma ya bada shi a madadinmu dukka, me zai hana shi bamu dukkan abubuwa a yalwace tare da shi?
32 Aquele que não poupou seu próprio Filho, mas que por todos nós o entregou, como não nos dará também com ele todas as coisas?
33 Wa zaya kawo wata tuhuma ga zababbu na Allah? Allah ne ke “yantarwa.
33 Quem poderia acusar os escolhidos de Deus? É Deus quem os justifica.
34 Wanene ke hukumtawa? Almasihu ne da ya mutu sabili da mu har ma fiye da haka, shi wanda kuma aka tasar. Yana mulki tare da Allah a wuri mai daukaka, shi ne kuma ya ke roko sabili da mu.
34 Quem os condenará? Cristo Jesus, que morreu, ou melhor, que ressuscitou, que está à mão direita de Deus, é quem intercede por nós!
35 Wa za ya raba mu da kaunar Allah? Kunci, ko bacin rai, ko tsanani, ko yunwa, ko tsiraci, ko hadari, ko takobi?
35 Quem nos separará do amor de Cristo? A tribulação? A angústia? A perseguição? A fome? A nudez? O perigo? A espada?
36 Kamar yadda aka rubuta, “Saboda kai ake kisanmu dukkan yini. An mai da mu kamar tumaki yanka.”
36 Realmente, está escrito: Por amor de ti somos entregues à morte o dia inteiro; somos tratados como gado destinado ao matadouro {Sl 43,23}.
37 A dukan al'amuran nan mun fi karfi a ce da mu masu nasara ta wurin shi da ke kaunar mu.
37 Mas, em todas essas coisas, somos mais que vencedores pela virtude daquele que nos amou.
38 Gama na tabata cewa ko mutuwa, ko rai, ko mala'iku, ko mulkoki, ko al'amuran yanzu, ko al'amura masu zuwa, ko iko,
38 Pois estou persuadido de que nem a morte, nem a vida, nem os anjos, nem os principados, nem o presente, nem o futuro, nem as potestades,
39 ko tsawo, ko zurfi, kai ko wace irin halitta, ba su isa su raba mu da kaunar Allah, da ke a cikin Almasihu Yesu Ubangijin mu ba.
39 nem as alturas, nem os abismos, nem outra qualquer criatura nos poderá apartar do amor que Deus nos testemunha em Cristo Jesus, nosso Senhor.

Ler em outra tradução

Comparar com outra

Estude este capítulo no WhatsApp

Peça à IA da Bíblia Fala para explicar Romanos 8, comparar traduções ou montar um estudo — tudo direto pelo WhatsApp.