Mateus 12

Litafi Mai-tsarki (HAU_ULB) vs NAA

Sair da comparação
NAA Nova Almeida Atualizada 2017
1 A wannan lokaci, Yesu ya tafi a ranar Asabaci, ya bi cikin gonar hatsi. Almajiransa na jin yunwa, sai suka fara zagar hatsi suna ci.
1 Por aquele tempo, num sábado, Jesus passou pelas searas. Estando os seus discípulos com fome, começaram a colher espigas e a comer.
2 Amma da Farisawa suka gan su, sai su ka ce wa Yesu. “Duba, almajiranka su na yin abin da doka ta haramta a ranar Asabaci.”
2 Os fariseus, vendo isso, disseram a Jesus: — Olhe! Os seus discípulos estão fazendo o que não é lícito fazer num sábado.
3 Amma Yesu ya ce masu, “Baku karanta abin da Dauda ya yi ba, lokacin da ya ke jin yunwa, tare da mazan da ke tare da shi?
3 Mas Jesus lhes disse:
4 Yadda ya shiga gidan Allah, ya ci gurasar alfarwa da doka ta hana shi ko mazan da ke tare da shi su ci, sai dai Firistoci ne kawai doka ta basu damar ci?
4 Como entrou na Casa de Deus, e comeram os pães da proposição, os quais não era lícito comer, nem a ele nem aos que estavam com ele, mas exclusivamente aos sacerdotes?
5 Sa'annan ba ku karanta cikin shari'a cewa, a ranar Asabaci, Firistoci da ke cikin haikali na sabawa ranar Asabaci, amma kamar ba su yi laifi ba?
5 Ou vocês não leram na Lei que, aos sábados, os sacerdotes no templo profanam o sábado e ficam sem culpa?
6 Amma ina tabbatar maku da cewa, wani wanda ya fi haikali girma yana nan.
6 Pois eu lhes digo que aqui está quem é maior do que o templo.
7 In da kun san ma'anar wannan 'Na fi son jinkai fiye da hadaya,' da baku shari'anta wa marar laifi ba.
7 Mas, se vocês soubessem o que significa: “Quero misericórdia, e não sacrifício”, não teriam condenado inocentes.
8 Gama Dan mutum shine Ubangijin Asabaci.”
8 Porque o Filho do Homem é senhor do sábado.
9 Sa'annan Yesu ya bar wannan wuri, ya shiga majami'ar su.
9 Tendo Jesus saído dali, entrou na sinagoga deles.
10 Sai ga wani mutum wanda hannun sa ya shanye, sai Farisawa suka tambayi Yesu, cewa, “Doka ta halarta a yi warkarwa a ranar Asabaci?” Domin su zarge shi a kan zunubi.
10 Achava-se ali um homem que tinha uma das mãos ressequida. Então, a fim de o acusar, perguntaram a Jesus: — É lícito curar no sábado?
11 Yesu ya ce masu, “Wanene a cikin ku, wanda idan ya na da tunkiya guda, sa'annan tunkiyar nan ta fada a rami mai zurfi a ranar Asabaci ba zai kamo ta ya fitar da ita ba?
11 Ao que lhes respondeu:
12 Yaya za a kwatanta darajar mutum da tunkiya! Saboda haka ya halarta a yi alheri ranar Asabaci.”
12 Ora, quanto mais vale um homem do que uma ovelha! Logo, é lícito nos sábados fazer o bem.
13 Sai Yesu ya ce wa mutumin nan “Mika hannun ka.” Ya mike hannunsa, sai hannun nan ya dawo lafiyaye kamar dayan hannunsa.
13 Então Jesus disse ao homem: O homem estendeu a mão, e ela foi restaurada e ficou sã como a outra.
14 Amma Farisawa su ka fita waje su ka fara mugun shiri domin sa. Su na neman hanyar da za su kashe shi.
14 Mas os fariseus, saindo dali, conspiravam contra ele, procurando ver como o matariam.
15 Da Yesu ya fahimci wannan, sai ya janye kan sa daga nan. Mutane da dama su ka bi shi, ya warkar da su duka.
15 Mas Jesus, sabendo disto, afastou-se dali. Muitos o seguiram, e a todos ele curou,
16 Ya dokace su da kada su bayyana shi ga kowa,
16 advertindo-lhes, porém, que não o expusessem à publicidade.
17 domin ya zama gaskiyar abin da aka fada ta wurin annabi Ishaya, cewa,
17 Isso aconteceu para se cumprir o que foi dito por meio do profeta Isaías:
18 “Dubi, bawa na zababbe; kaunatacce na, wanda ya ke faranta mani raina sosai. Zan sa Ruhu na bisan sa, za ya furta hukunci zuwa al'ummai.
18 “Eis aqui o meu servo, que escolhi, o meu amado, em quem a minha alma se agrada. Farei repousar sobre ele o meu Espírito, e ele anunciará juízo aos gentios.
19 Ba za ya yi jayayya ko tada murya ba, babu wanda za ya ji muryar sa a karabku.
19 Não entrará em discussões, nem gritará, nem fará ouvir nas praças a sua voz.
20 Ba zai karya kara da ya tankwashe ba; ba zai kashe fitilar da ta kusa mutuwa ba; sai ya kawo hukunci ga nasara.
20 Não esmagará a cana quebrada, nem apagará o pavio que fumega, até que faça vencedor o juízo.
21 Sa'annan al'ummai za su dogara a ga sunansa.
21 E no seu nome os gentios colocarão a sua esperança.”
22 Sa'annan wani mutum, makaho ne, kurma kuma, aljannu kuma na cikinsa, an kawo shi wurin Yesu. Ya warkar da shi, ya sami ganin gari ya kuma yi magana.
22 Então trouxeram a Jesus um endemoniado, cego e mudo. Jesus o curou, e o homem passou a falar e a ver.
23 Jama'a su ka yi mamaki kwarai, su na cewa, “Ko wannan ne Dan Dawuda?”
23 E toda a multidão se admirava e dizia: — Não seria este, por acaso, o Filho de Davi?
24 Amma da Farisawa su ka ji wannan al'ajibi, sai su ka ce, “Mutumin nan yana fitar da aljannu ta wurin Bahalzabuba sarkin aljannu ne.”
24 Mas os fariseus, ouvindo isto, diziam: — Este não expulsa demônios senão pelo poder de Belzebu, o maioral dos demônios.
25 Amma Yesu ya san tunanin su, sai ya ce. “Duk mulkin da ya rabu gaba da kan sa, ba zaya tsaya ba, duk wani birni da ya rabu ba zai tsaya ba, ko gida da ya tsage, za ya rushe.
25 Mas Jesus, sabendo o que eles pensavam, disse-lhes:
26 Idan Shaidan ya fitar da Shaidan, ya rabu gaba da kansa. Yaya mulkin sa za ya tsaya?
26 Se Satanás expulsa Satanás, está dividido contra si mesmo; como, então, o seu reino subsistirá?
27 Idan Ina fitar da aljannu da ikon Ba'alzabuba, ta wurin wa masu bin ku su ke fitar da su? Saboda haka, su za su shari'anta ku.
27 E, se eu expulso os demônios por Belzebu, por quem os filhos de vocês os expulsam? Por isso, eles mesmos serão os juízes de vocês.
28 Amma idan ina fitar da aljannu da Ruhun Allah ne, hakika mulkin Allah ya zo gare ku.
28 Se, porém, eu expulso os demônios pelo Espírito de Deus, certamente é chegado o Reino de Deus sobre vocês.
29 Kuma ta yaya mutum za ya shiga gidan mai karfi ya kwashe masa kaya ba tare da ya fara daure shi ba? Sa'annan ne za ya iya satar masa kaya daga gidansa.
29 Ou como pode alguém entrar na casa do valente e roubar-lhe os bens sem primeiro amarrá-lo? E só então saqueará a casa dele.
30 Wanda baya tare da ni yana gaba da ni ke nan, wanda kuma baya tarawa tare da ni, yana watsarwa ne.
30 — Quem não é por mim é contra mim; e quem comigo não ajunta espalha.
31 Saboda haka ina ce maku, kowanne zunubi da sabo, za a gafarta wa mutum, amma sabon Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta shi ba.
31 Por isso, digo a vocês que todo pecado e blasfêmia serão perdoados aos homens; mas a blasfêmia contra o Espírito não será perdoada.
32 Duk wanda yayi batanci ga Dan Mutum, za a gafarta masa. Amma duk wanda yayi batanci game da Ruhu Mai Tsarki ba za a gafarta masa ba, a nan duniya da har abada.
32 Se alguém disser alguma palavra contra o Filho do Homem, isso lhe será perdoado; mas, se alguém falar contra o Espírito Santo, isso não lhe será perdoado, nem neste mundo nem no porvir.
33 Ko dai a mai da itace mai kyau 'ya'yansa kuma su yi kyau, ko a mai da itace marar kyau 'ya'yansa kuma marasa kyau, gama ana sanin itace ta wurin 'ya'yansa.
33 — Tornem a árvore boa e o seu fruto será bom, ou tornem a árvore má e o seu fruto será mau; porque pelo fruto se conhece a árvore.
34 Ku 'ya'yan macizai, tun da ku miyagu ne, yaya za ku iya fadin abubuwa nagari? Gama daga cikar zuciya baki ke magana.
34 Raça de víboras! Como vocês podem falar coisas boas, sendo maus? Porque a boca fala do que está cheio o coração.
35 Mutumin kirki daga ajiyar zuciyarsa ya kan fitar da abubuwa masu kyau, mugun mutum kuma daga mummunar ajiyar zuciyarsa ya kan fitar da abubuwan mugunta.
35 A pessoa boa tira do tesouro bom coisas boas; mas a pessoa má do mau tesouro tira coisas más.
36 Sa'annan ina ce maku a ranar shari'a, mutane za su bada lissafin abubuwan banza da su ka fadi.
36 — Digo a vocês que, no Dia do Juízo, as pessoas darão conta de toda palavra inútil que proferirem;
37 Gama ta wurin maganganun ku, za a 'yantar da ku, ta wurin maganganun ku kuma za a kashe ku.”
37 porque, pelas suas palavras, você será justificado e, pelas suas palavras, você será condenado.
38 Sa'annan wadansu Malaman Attaura, da Farisawa suka amsa suka ce wa Yesu, “Mallam, muna so mu ga wata alama daga gare ka.”
38 Então alguns escribas e fariseus disseram a Jesus: — Mestre, queremos ver algum sinal feito pelo senhor.
39 Amma Yesu ya amsa ya ce masu, “Mugun zamani da mazinaciyar tsara, su na bukutar alama. Amma babu alamar da za a ba su, sai dai alamar annabi Yunusa.
39 Mas ele respondeu:
40 Gama yadda Yunusa ya yi kwana uku da dare uku a cikin babban kifi, haka ma Dan Mutum zaya yi kwana uku da dare uku a cikin zuciyar kasa.
40 Porque assim como Jonas esteve três dias e três noites no ventre do grande peixe, assim o Filho do Homem estará três dias e três noites no coração da terra.
41 Mutanen Nineba za su tsaya a ranar shari'a da wannan zamani sannan su kashe su. Domin sun tuba da suka ji wa'azin Yunusa, amma duba wanda ya fi Yunusa yana nan.
41 Ninivitas se levantarão, no Juízo, com esta geração e a condenarão, porque se arrependeram com a pregação de Jonas. E aqui está quem é maior do que Jonas.
42 Sarauniyar Kudu za ta tashi da mutanen wannan zamani ta kuma kashe su. Ta zo daga karshen duniya domin ta ji hikimar Sulaimanu, kuma duba, wanda ya fi Sulaimanu yana nan.
42 A rainha do Sul se levantará, no Juízo, com esta geração e a condenará, porque veio dos confins da terra para ouvir a sabedoria de Salomão. E aqui está quem é maior do que Salomão.
43 Idan kazamin ruhu ya rabu da mutum, ya kan wuce ya nemi wuraren da ruwa yake domin ya huta, amma bai samu ba.
43 — Quando o espírito imundo sai de uma pessoa, anda por lugares áridos procurando repouso, porém não encontra.
44 Sai ya ce, 'zan koma gidana inda na fito'. Bayan ya dawo, sai ya tarar da gidan nan an share shi ya zama da tsabta.
44 Por isso, diz: “Voltarei para a minha casa, de onde saí.” E, voltando, ele a encontra vazia, varrida e arrumada.
45 Sai ya koma ya kawo wadansu ruhohi guda bakwai, wadanda su ka fi shi mugunta, sa'annan dukan su su zo su zauna a nan. Sa'annan yanayin mutumin nan na karshe ya fi na farko muni. Haka zaya kasance ga wannan mugun zamani.
45 Então vai e leva consigo outros sete espíritos, piores do que ele, e, entrando, habitam ali. E o último estado daquela pessoa se torna pior do que o primeiro. Assim também acontecerá a esta geração perversa.
46 Sa'adda Yesu ya ke yi wa Jama'a jawabi, sai mahaifiyarsa da 'yan'uwansa su ka zo su ka tsaya a waje, suna neman su yi magana da shi.
46 Enquanto Jesus ainda falava ao povo, eis que a mãe e os irmãos dele estavam do lado de fora, procurando falar com ele.
47 Sai wani ya ce masa, “Duba, mahaifiyarka da 'yan'uwanka suna tsaye a waje, suna so su yi magana da kai”.
47 E alguém lhe disse: — A sua mãe e os seus irmãos estão lá fora e querem falar com o senhor.
48 Amma Yesu ya amsa ya ce wa shi wanda ya gaya masa, “Wacece mahaifiyata? Kuma su wanene 'yan'uwana?”
48 Porém Jesus respondeu ao que lhe trouxe o aviso:
49 Sai ya mika hannu ya nuna almajiransa ya ce, “Duba, ga mahaifiyata da 'yan'uwana!
49 E, estendendo a mão para os discípulos, disse:
50 Gama duk wanda yake aikata nufin Ubana wanda ya ke cikin sama, shine dan'uwana, da 'yar'uwata da mahaifiyata.”
50 Portanto, aquele que fizer a vontade de meu Pai celeste, esse é meu irmão, minha irmã e minha mãe.

Ler em outra tradução

Comparar com outra

Estude este capítulo no WhatsApp

Peça à IA da Bíblia Fala para explicar Mateus 12, comparar traduções ou montar um estudo — tudo direto pelo WhatsApp.