Apocalipse 10

Litafi Mai-tsarki (HAU_ULB) vs ARC

Sair da comparação
ARC Almeida Revista e Corrigida 2009
1 Sa'anan na ga wani babban mala'ika yana zuwa daga sama. Yana lullube cikin girgije, a bisa kansa akwai bakangizo. Fuskarsa kamar rana, kafafunsa kamar ginshikan wuta.
1 E vi outro anjo forte, que descia do céu, vestido de uma nuvem; e por cima da sua cabeça estava o arco celeste, e o rosto era como o sol, e os pés, como colunas de fogo;
2 Yana rike da karamin littafi a hannunsa, da aka bude, sai ya sa kafarsa ta dama a bisa teku, kafarsa ta hagu kuma a kan kasa.
2 e tinha na mão um livrinho aberto e pôs o pé direito sobre o mar e o esquerdo sobre a terra;
3 Sai yayi ihu da babbar murya kamar zaki mai ruri. Lokacin da ya yi ihu, tsawan nan bakwai suka yi magana da karar su.
3 e clamou com grande voz, como quando brama o leão; e, havendo clamado, os sete trovões fizeram soar as suas vozes.
4 Da tsawan nan bakwai suka yi magana, ina dab da rubutu, amma na ji wata murya daga sama cewa, “Ka rike asirin abin da tsawan nan bakwai suka fada. Kada ka rubuta shi.”
4 E, sendo ouvidas dos sete trovões as suas vozes, eu ia escrevê-las, mas ouvi uma voz do céu, que dizia: Sela o que os sete trovões falaram e não o escrevas.
5 Sai mala'ikan da na gani tsaye bisa teku da kasa, ya daga hannun damarsa sama.
5 E o anjo que vi estar sobre o mar e sobre a terra levantou a mão ao céu
6 Sai ya rantse da wannan da ke raye har abada abadin - wanda ya halicci sama da duk abinda ke cikinsa, da duniya da duk abin da ke a kanta, da teku da dukan abin da ke cikinsa, sai mala'ikan ya ce, “Babu sauran jinkiri.
6 e jurou por aquele que vive para todo o sempre, o qual criou o céu e o que nele há, e a terra e o que nela há, e o mar e o que nele há, que não haveria mais demora;
7 Amma a ranar da mala'ika na bakwai yana dab da busa kahonsa, a lokacin ne asirin Allah zai cika, daidai da yadda ya sanar wa bayinsa annabawa.”
7 mas nos dias da voz do sétimo anjo, quando tocar a sua trombeta, se cumprirá o segredo de Deus, como anunciou aos profetas, seus servos.
8 Muryar da na ji daga sama ta sake magana da ni: “Tafi, ka dauki budadden littafin da ke hannun mala'ikan da ke tsaye bisa teku da kan kasa.”
8 E a voz que eu do céu tinha ouvido tornou a falar comigo e disse: Vai e toma o livrinho aberto da mão do anjo que está em pé sobre o mar e sobre a terra.
9 Sai na tafi wurin mala'ikan na ce da shi ka bani karamin littafin. Yace dani, “Dauki littafin ka ci. Zai sa cikinka ya yi daci, amma a bakinka zai yi zaki kamar zuma.”
9 E fui ao anjo, dizendo-lhe: Dá-me o livrinho. E ele disse-me: Toma-o e come-o, e ele fará amargo o teu ventre, mas na tua boca será doce como mel.
10 Na dauki karamin littafin daga hannun mala'ikan na ci. Ya yi zaki sosai a bakina kamar zuma, amma da na ci, sai cikina ya zama da daci.
10 E tomei o livrinho da mão do anjo e comi-o; e na minha boca era doce como mel; e, havendo-o comido, o meu ventre ficou amargo.
11 Wani yace mani, “Dole ka sake yin annabci kuma game da mutane masu yawa, da al'ummai, da harsuna da sarakuna.”
11 E ele disse-me: Importa que profetizes outra vez a muitos povos, e nações, e línguas, e reis.

Ler em outra tradução

Comparar com outra

Estude este capítulo no WhatsApp

Peça à IA da Bíblia Fala para explicar Apocalipse 10, comparar traduções ou montar um estudo — tudo direto pelo WhatsApp.